Alamomin rushewar zamantakewa

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da sake haɗuwa a filin zamantakewa na wannan makon. Ya zazumin nan? Fatan Allah ya sa mu yi ibada karɓaɓɓiya. Sannunku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini, Blueprint Manhaja.

A wannan mako muna tafe da alamommin da suke nuna cewa aurenku yana da masassarar mutuwa, wato kwanansa yana gab da ƙarewa. Kamar yadda Hausawa kan ce aure rai ne da shi, duk ranar da wa’adin ajalinsa ya zo, labudda ba ya ƙara kwana, wannan batu haka yake. Idan ajalin aure ya zo, za ka ga alamomi suna ta nunawa. An san dole da ma a zaman aure zama ne na zo mu zauna, zo mu saɓa ne.

Amma akwai wasu matsaloli da suke alamta cewa, aure ya girgiza, igiyarsa tana rawa. Za a ga auren ya salamce ya rasa karsashin da yake da shi na tun na farko. Duk da dai saɓani a aure ana iya zama a gyara, amma akwai wasu abubuwa da idan suka fara ɓullowa, da wahala ba su a ƙarar da auren ba.

Don haka, idan an ga waɗannan alamomi, dole ma’aurata su miƙe su yi wani abu don ganin an kawar da matsalolin ko kuma aurensu ya haɗu da ajalinsa. Wato dai ta yadda aka fuskanci matsalar, shi ne zai kai ga sasantawa ko rabuwa. A sha karatu lafiya.

Ga alamomi da suke nuna alamomin aurenku yana cikin garari:

  1. Kullum kuna adawa da juna. Babbar nasarar da ake so a samu a gidan aure wacce mutane kan yi wa ma’aurata san-barka ita ce, haɗin kai. Su zama masu ra’ayi da magana da murya ɗaya, sai ka ga zama ya zamo gwanin sha’awa. Amma a ce kullum kuna adawa da juna. Kullum idan wani ya yi Gabas, sai wani ya yi Yamma? An san dole da ma zo mu zauna zo mu saɓa. Ba a kan kowanne abu ba ne ma’aurata za su yi tarayya ba. Amma idan adawa da sukar juna suka shallake yawan yadda ba a yaba wa juna da fahimtar juna kamar haka, gaskiya akwai matsala babba wacce take buƙatar a tara hankali a gano ta, kuma a magance ta. Don tana iya yi wa auren ƙamshin mutuwa. Saboda ita adawa idan ta yi zafi takan shigo da ƙiyayya. Ka ga ko a gidan aure ƙiyayya abar gudu ce. Don a kan ƙauna da so ake gina gidan auren.
  2. Rashin mu’amalar aure na tsahon lokaci. Shi ma babbar matsala ce ga aure wacce za ta iya kai wa ga rabuwa da gaggawa. Saduwa tana daga cikin manyan dalilan da suka sa ake yin aure. Idan har ma’aurata suka daina burge juna da son kusantar juna a aure, akwai gagarumar matsala wacce take buƙatar a duba ta. Duk da dai ba abinci ba ne, sinadari ne, amma idan har ma’aurata lafiyayyu za su kai satittika ko watanni da dama ba tare da sun kusanci juna ba, akwai babbar matsala. Na maimaita, akwai babbar matsala!
  3. Sai na uku, yawan yin dogon musu a kan abu guda. Na san masu karatu za su yarda da ni cewa, a farko-farkon kowanne aure ba a fiye samun dogon musu tsakananin ma’aurata ba. Dalili kuma ba ya wuce tsananin yarda da ra’ayin juna ba sannan kuma da gudun ɓata wa juna rai da kuma tsananin shauƙin son juna. Amma yayin da aka ga musu ya yawaita a gidan aure, to la shakka waɗancan abubuwan da aka lasafta a sama sun yi ƙaura daga gidan. Wato gudun ɓacin ran juna, fahimta da kuma tsananin son juna. Don haka sai a gaggauta kawo ɗauki a yi wa auren garambawul domin yana cikin masassarar mutuwa. Idan ba haka ba, ajali zai cim masa.

Abin tashin hankali ma game da musun, ko da gyara ko laifi ɗaya ya yi wa ɗaya, sai musu ya tashi. Daga ƙarshe dai, sai a dinga tsoron yi wa juna gyara ko magana a kan abu saboda gudun rashin fahimta da kuma zazzafar muhawara.

  1. Na huɗu, rashin son zama a inuwa guda. Shi ma rashin son zama tare da abokin ko abokiyar rayuwa wata babbar alama ce da take nuna aurenku yana cikin garari. A yayin da ma’aurata suka fi ƙaunar kasancewa tare da wasu mutane daban, maimakon junansu, lallai akwai matsala babba da take buƙatar a kawar da ita don gudun kada ta yi sanadiyyar ajalin auren.

Wata matar idan ta ga mijinta a gida, sai ta ji duk Duniya ta yi mata zafi. Ta dinga Allah-Allah ya fice. Shi ma mijin ya gwammace zama da abokai ko ‘yanuwa a maimakon matarsa ta sunnah. Ma’auratan da suka samu kansu a wannan matsalar, su gaggauta saita ta. Domin so da ɗokin kasancewa tare da juna ga ma’aurata alama ce ta zaman lafiya da so da yarda a cikin aure. Ƙauracewarsu kuma alama ce da taje nuna aure yana cikin matsala.

  1. Na biyar, fara ɓoye wa juna sirrika. Ɓoye wasu sirrika daga abokin zama wajibi ne wannan. Domin kowanne ɗan adam da ma yana da sirrikansa na kansa da yake buƙatar ɓoye su ga sauran mutane. Amma ɓoye wasu sirrika don gudun kada abokin zamanki ko abokiyar zamanka ta sani, alama ce ta rashin yarda da juna. Kuma alama ce ta nuna aure yana cikin garari da neman ɗauki.
  2. Na shida, fara hangen wasu matan ko mazan a waje. Wacce alama ce kuma ta fi wannan nuna cewa aure yana cikin garari wataƙila ma yana gab da cim ma ajalinsa? Kawai namiji ya wayi gari matarsa ta daina birge shi. Ko mace ta wayi gari ta daina sha’awar mijinta mazan waje ne suke birge ta. Wata ma har ta fara kula wasu a waje. Ko kuma shi mijin har ya fara biye-biyen wasu matan a waje. Wannan babbar matsala ce wacce shi wanda yake ciki shi zai yi ƙoƙarin kawar da ita domin samar da maslaha a gidan aurensu. Misali idan mace ce ta ji irin wannan kada ta biye wa zuciyarta har ta fa]a son wani. Da gani ta san wannan akwai ɓurɓushin sharrin shaiɗan. Ta ji tsoron Allah ta fi ƙarfin zuciyarta. Ta nemi taimakon Allah don ya shiga lamarinta. Idan kuma hakan ta faru ne sakamakon rashin kulawa daga mijin, ta duba kura-kurenta ta gyara, sannan ta yi ƙoƙarin jawo hankalin mijinta.
  3. Sai na bakwai, mijinki shi ne mutum na farko da kike kira idan abin farin ciki ko matsala ta same ki? Matarka ita ce wacce kake fara kira idan abin farinciki ko matsala ta same ka? Idan amsoshinku suka kasance a’a ne, to aurenku yana cikin garari. Dalilin da ya sa na ce haka kuwa, duk lokacin da abun daɗi ko na farin ciki ya samu mutum, mutumin da ya fi yarda da shi ko wanda ka fi kusanci da shi shi kake ɗoki da gaggawar sanar wa.

In dai abokin zamanka ko zamanki ba shi ne mutum ma fi kusanci gare ki ba, to akwai matsala a zaman naku. Dole sai kun zauna kun binciki zaman naku kun magance matsalar da take akwai. Don aure ana gina shi a kan so da yarda. Idan babu su kuwa, akwai matsala a tattare da zaman. Don ba zai yi ƙarko ba har sai an gyara.

To amma ta yaya za ku ceto aurenku?

Waɗannan matsaloli ana iya warware su ta hanyar tattaunawa ta fahimta da juna. Ku samu lokaci ko ku bar garin ku je ku tattauna. Ko idan ba halin haka idan yara sun yi barci da dare ka ta da ita ku yi magana. Idan ma hakan ba zai yi ba, to a sanar da magabata idan abin ya ci tura a nemi shawarar girma daga gare su. Allah ya datar da mu.

Masu kira su yi mana addu’a, da tsokaci da shawara dukkanku muna godiya saboda kina ƙarfafa mana gwiwa. Sai Allah ya kai mu mako mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *