Editor

9513 Posts
Rubuta fim ɗin da zai amfanar da al’umma ne babban burina – Yusra Yusuf

Rubuta fim ɗin da zai amfanar da al’umma ne babban burina – Yusra Yusuf

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano Yusra Yusuf Yunusa wadda aka fi sani da Yusra AGM matashiyar da ta yi fice a wajen rubuta labarin fim a masana'atar Kannywood. A tattaunawarta da wakilin Manhaja a Kano, Ibrahim Hamisu, za ku ji tarihinta da kuma irin faɗi-tashin da ta yi har ta kai ana karbar rubutunta a Kannywood. A sha karatu lafiya: MANHAJA: Muna son ki gabatar mana da kanki ga masu karatunmu? YUSRAH YUSUF: Sunana Yusrah Yusuf Yunusa, wacce aka fi sani da Yusra AGM Bashir kamar yadda ake kira na. Ko za ki ba mu taƙaitaccen tarihinka? Nayi karatu a Mai…
Read More
APC ta kori Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Omo-Agege

APC ta kori Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Omo-Agege

Daga BASHIR ISAH Jam'iyyar APC a Jihar Delta ta kori Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege, daga zama mamban jam'iyyar kan zargin yi wa jam'iyya zagon ƙasa da sauran laifuka da ba a bayyana su ba. APC reshen Delta ta sanar da koran Omo-Agage daga jam'iyyar ce cikin wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 31 ga Maris, 2023 wadda aka raba wa manema labarai a ranar Litinin. Idan ba a manta ba, Omo-Agege ya yi takarar gwamnan jihar Delta ƙarƙashin APC inda ya sha kaye a hannun ɗan takarar jam'iyyar PDP, Sheriff Oborevwori a zaɓen da ya gudana kwanan baya.…
Read More
Matar Sanata Kalu, Ifeoma Kalu ta rasu

Matar Sanata Kalu, Ifeoma Kalu ta rasu

Daga WAKILINMU Tsohon Gwamnan Jihar Abia, Sanata Orji Kalu, ya ba da sanarwar mutuwar matarsa, Mrs Ifeoma Kalu. Marigayiyar ta bar duniya tana da shekara 61. Sanata Kalu ya sanar da mutuwar matar tasa ne a shafinsa na soshiyal midiya. “Zuciya cike da alhini da jimami muke sanar da mutuwar Mrs Ifeoma Ada Kalu tana da shekara 61. “Mutumiyar kirki ce a halin rayuwarta, kuma mai himma wajen bautar Allah da hidimta wa al'umma. “Za a gudanar da ibadar tunawa da ita a Amurka," in sanarwar. Kalu ya buƙaci al'umma da su tuna da marigayiyar cikin addu'o'insu a wannan lokaci…
Read More
Amfanin kankana ga gyaran fata

Amfanin kankana ga gyaran fata

Daga AISHA ASAS Kankana na ɗaya daga cikin 'ya'yan itace da ke da matuƙar tasiri a gyaran fata da kuma kawar da cututtukan fata masu dama. Tana ɗauke da sinadaran da ke gusar da maiƙon da ke fita a hanyoyin fitar gumi, wanda idan ya yawaita zai iya haifar da fesowar qananan ƙuraje. Kankana na taka muhimmiyar rawa wajen gyara fatar da ta ke yawan yankwanewa, idan aka markaɗe ta (ba tare da an zuba mata ruwa ko kaɗan ba, kuma za a haɗe ne har 'ya'anta) aka zuba mata zuma kaɗan, ana shafawa a inda matsalar ta ke sau…
Read More
Kafafen yaɗa labaran Nijeriya sun ƙaddamar da cibiyar ƙorafe-ƙorafe

Kafafen yaɗa labaran Nijeriya sun ƙaddamar da cibiyar ƙorafe-ƙorafe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Litinin ne kafafen yaɗa labaran Nijeriya su ka ƙaddamar da kwamitin mutane tara na hukumar sauraron ƙorafe-ƙorafen Kafafen Yaɗa Labaran Ƙasa (NMCC), wadda aka fi sani da ‘National Ombudsman’. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Kabiru Yusuf, shugaban ƙungiyar ’yan jaridu ta ƙasa NPAN, kuma shugaban ƙungiyar ’yan jaridu ta Nijeriya NPO ya fitar. Yusuf ya ce, a cikin sanarwar da aka fitar ranar Juma’a a Legas, an zaɓo mambobin hukumar ne daga kafafen yaɗa labarai, malamai da ƙungiyoyin farar hula. Ya ce, matakin ya zama wajibi a yunƙurin da ake…
Read More
Ganduje ya naɗa Farfesa Jega a matsayin Shugaban Gudanarwar Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi

Ganduje ya naɗa Farfesa Jega a matsayin Shugaban Gudanarwar Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa tsohon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zamanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, a matsayin Shugaban Majalisar Gudanarwar Sa’adatu Rimi dake Kano. Hakan na cikin wata sanarwa ce da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Kwamared Muhammad Garba ya fitar. Sanarwa ta ce Gwamna Ganduje ya kuma amince da naɗin Oba Dakta Sanata Moshood Olalekan Ishola Balogun na Aliiwo a matsayin Babban uba kuma shugaban Kwamitin Gudanarwar Jami’ar ta Sa’adatu Rimi. A cewar Muhammed Garba, sauran mambobin kwamitin gudanarwar Jami’ar sun haɗa da: Dakta Muhammad Adamu Kwankwaso,…
Read More
’Yan bindiga sun yi awon gaba da ɗalibai mata a Zamfara

’Yan bindiga sun yi awon gaba da ɗalibai mata a Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu gungun ’yan ta'adda sun sace ɗalibai mata biyu na Jami’ar Tarayya da ke Gusau (FUGUS) a Jihar Zamfara. An ruwaito cewa, lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi 2 Afirilu, 2023 lokacin da ’yan ta’addan suka farmaki ɗakin kwanan ɗaliban da ke Sabon-Gida. Rahotanni sun ce, ’yan matan da aka sacen sun haɗa da wata mai suna Maryam da kuma Zainab. ’Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin, inda Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Mohammed Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya bayyana yadda ya faru. A cewarsa, ’yan ta’addan sun mamaye ɗakin…
Read More
Ƙalubalantar canja fasalin Naira ya sa na sha kaye a zaɓe – Matawalle

Ƙalubalantar canja fasalin Naira ya sa na sha kaye a zaɓe – Matawalle

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya alaƙanta dalilin faɗuwarsa zaɓe da ƙarar da suka shigar da Gwamnatin Tarayya akan sauya fasalin kuɗi da Babban Bankin Nijeriya ya yi. Gwamnan ya zargi cewar, wasu ƙushoshi a cikin Gwamnatin Tarayya da yin yaƙi da shi tuƙuru domin ganin bai sake komawa gwamnan jihar ta Zamfara ba. Idan za a iya tunawa, Matawalle ya yi takara ne a jam'iyyar APC mai mulki, inda Dauda Lawal na jam'iyyar PDP ya buga shi da ƙasa. Bugu da ƙari, gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje sun kai…
Read More
INEC ta sanar da ranar sake zaɓen majalisar jiha a wasu ƙananan hukumomi a Katsina

INEC ta sanar da ranar sake zaɓen majalisar jiha a wasu ƙananan hukumomi a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) reshen Jihar Katsina, ta ayyana ranar 14 ga watan Afrilu, 2023 a matsayin ranar da za a sake gudanar da zaɓen wasu ƙananan hukumomin jihar guda uku da suka haɗa da Kankia da Ƙanƙara da kuma Kurfi. Hukumar ta bayyana cewar zaɓen da aka gudanar a ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa a ranar 18 ga watan Maris, 2023 bai kammalu ba, saboda haka ne aka sake saka ranar da za a kammala su. INEC ta ce, dokokinta ne suka yi tanadin sake gudanar da zaɓe a rumfuna ko…
Read More
Jaruma Mercy Aigbe ta musulunta

Jaruma Mercy Aigbe ta musulunta

Daga WAKILINMU Fitacciyar jaruma a masana'antar fina-finai ta Nollywood, Mercy Aigbe, ta bayyana sunanta na Musulunci biyo bayan musuluntar da ta yi. Ta bayyana sunan ne a wajen taron lacca na Ramadan da addu'a ta musamman da suka shirya ita da mijinta, Kazeem Adeoti. Hakan na ƙunshe ne cikin wani faifan bidiyon tattaunawar da aka yi da ita wanda aka yaɗa a kafar sada zumunta na zamani. An jiyo ta tana cewa, “Insha Allah, sabon sunana shi ne Hajiya Meenah Mercy Adeoti. Meenah mai ɗauke da harafin H."
Read More