Editor

9513 Posts
Tambuwal ya ƙaurace wa gangamin Atiku na Bauchi, ya ziyarci Buhari da Bagudu a Abuja

Tambuwal ya ƙaurace wa gangamin Atiku na Bauchi, ya ziyarci Buhari da Bagudu a Abuja

Daga WAKILINMU Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya ƙi halartar gangamin yaƙin neman zaɓen shugabancin ƙasa na jam’iyyarsu ta PDP a Bauchi domin halartar ganawar sirri da wasu gwamnonin APC, sannan daga bisani ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari. Jaridar News Point Nigeria ta kalato cewa, Tambuwal wanda shi ne Darakta-Janar na kwamitin neman yaƙin zaɓen Shugaban Ƙasa na PDP, ya yi ganawar sirri da Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC kuma Gwamnan Jhar Kebbi, Atiku Bagudu tare da tsohon Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi a gidansa da ke Maitama, Abuja. Majiyarmu ta ce Shugaba Buhari ne ya buƙaci ganawar bayan samun…
Read More
Ina ɗauke da cutar da mutane ƙalilan ne suka taɓa yin ta a duniya – celine Dion

Ina ɗauke da cutar da mutane ƙalilan ne suka taɓa yin ta a duniya – celine Dion

"Cutar ta taɓa damar da nake da ita ta sarrafa muryata zuwa waƙa" Daga AISHA ASAS Rayuwa tamkar karatun boko ce, za ka fara tun daga lokacin da ka ke naziri, zuwa firamare, har ka kai sakandare, daga ƙarshe ka dira jami'a, inda duk wani karatun ƙarshe ta ke cibiyarsa. Duk wannan tafiyar idan ka yi ta, ba za ka iya dawowa baya ba, ma'ana ba zai yiwu kana jami'a ka dawo firamare ba, yin hakan zai sa a yi ma kallon mai tavin hankali. Wannan shi ne ƙaramin misali akan rayuwa, duk ƙurciyarka wata rana za ka girma, kuma…
Read More
Buhari ya sake naɗa Kashifu Inuwa shugaban NITDA

Buhari ya sake naɗa Kashifu Inuwa shugaban NITDA

Daga ABUBAKAR M. TAHEER Shugaban kasa Muhammad Buhari ya sake naɗa Kashifu Inuwa Abdullahi a matsayin Darakta-Janar na Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA), sakamakon nasarorin da Hukumar ta samu bayan zaman Kashifu shugabanta. Shugaba Buhari ya bayyana haka ne yayin ƙaddamar da shirin manufar ƙasa kashi na biyu a fadarsa ranar Alhamis. Buhari ya ƙara da cewa, bayan dogon nazari da bibiyar ayyukan Hukumar NITDA ƙarƙashin Maikatar sadarwa da fasahar zamani, ƙarƙashin Kashifu Inuwa ya fahimci cewa hukumar ta cimma tarin nasarori wajen samar wa ƙasa cigaba. "A kan haka ne na yaba da ƙwazon Hukumar ta NITDA,…
Read More
Sama da mutum 1,800 sun mutu a girgizar ƙasar Turkiyya da Siriya

Sama da mutum 1,800 sun mutu a girgizar ƙasar Turkiyya da Siriya

Daga BASHIR ISAH Aƙalla mutum 1,800 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon girgizar ƙasar da ta auku a Turkiyya da Siriya. Iftila'in wanda ya auku da safiyar Litinin, ya lalata wasu manya biranen Turkiyya, yankunan da galibin 'yan gudun hijira daga Siriya ke da zama. An ga masu aikin ceto na ta ƙoƙarin bincike don gano mutanen da ƙasa ta rufta da su. Rahotanni sun ce wannan ita ce girgizar ƙasa mafi munin da aka fuskanta a baya-bayan a yankunan da lamarin ya shafa. Tuni ƙasashe duniya irin su Chana, Indiya, Qatar, Amurka da sauransu suka bayyana ƙudirinsu na tallafa…
Read More
Kotu ta dakatar da CBN aiwatar da dokar taƙaita cire kuɗi

Kotu ta dakatar da CBN aiwatar da dokar taƙaita cire kuɗi

…Ta yi barazanar tsare shugabannin bankuna Daga BASHIR ISAH Babban Kotu mai zamanta a Anuja, ƙarƙashin Mai Shari'a Eneojo Eneche, ta dakatar da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Babban Bankin Nijeriya (CBN) da kuma wasu bankuna 27 daga aiwatar da wa'adin daina amfani da tsoffi Naira na 10 ga Fabrairu ko bayar da wani umarni saɓanin wa'adin. Kazalika, kotun ta ba da umarnin shugabannin kotunan da lamarin ya shafa su ba da dalilin da ya sa ba za a tsare su tare da hukunta su ba saboda ɓarnar da suka yi wa fannin kuɗin ƙasa ta hanyar ɓoye sabbin Naira, wato…
Read More
2023: Akwai yunƙurin kashe Atiku idan ya ziyarci Kudu maso Gabas – IPOB

2023: Akwai yunƙurin kashe Atiku idan ya ziyarci Kudu maso Gabas – IPOB

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Haramtacciyar Ƙungiyar Masu Fafutukar Kafa Ƙasar Biyafara (IPOB) ta yi zargin cewa wasu ’yan siyasa na shirin kashe ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar. A wata sanarwa da Emma Powerful, mai magana da yawun ƙungiyar ’yan awaren ya fitar a ranar Lahadi, 5 ga watan Fabrairu, 2023, ya ce, an shirya makircin ne a yankin Kudu maso Gabas da nufin ɓata sunan ƙungiyar IPOB da kuma magoya bayan jam’iyyar LP da ke da tushe da shugabancin ɗan takararsu Peter Obi. “Ana shirin kashe Atiku Abubakar a yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya kuma da…
Read More
Yobe ta Arewa: Kotu ta tabbatar da takarar Sanata Lawan

Yobe ta Arewa: Kotu ta tabbatar da takarar Sanata Lawan

Daga BASHIR ISAH Kotun Ƙoli ta tabbatar da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, a matsayin ɗan takarar sanata na Jam'iyyar (APC) a shiyyar Yobe ta Arewa a zaɓen 2023. Kotun ta tabbatar da nasarar Lawan ne a zaman shari'a da ta yi ranar Litinin. Idan ba a manta ba, Lawan ya shigar da ƙara Kotun Ƙolin ne domin ƙalubalantar hukuncin Kotun Tarayya mai zamanta a Damaturu, bayan da kotun a Satumban 2022 ta tabbatar da Bashir Machina a matsayin halastaccen ɗan takrar sanata na yankin. Sau biyu Ahmad Lawan na shan kaye a kotu bayan da ya nemi ƙalubalantar…
Read More
NRC ta dakatar da jami’anta 3 kan sakaci da aiki

NRC ta dakatar da jami’anta 3 kan sakaci da aiki

Daga BASHIR ISAH Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa ta Ƙasa (NRC), ta dakatar da wasu jami’anta dangane da gocewar qafar jirgin da ya auku a yankin Kubwa na Abuja kwanan nan. Gocewar kta haifar da tsaiko ga aikin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna na ɗan lokaci kafin komawa da aiki bayan kwana, kuma bayan kammala aiki a matsalar da ta haifar da gocewar. Majiyarmu ta ce tuni hukumar ta dakatar da wasu jami’an da lamarin ya shafa sakamakon abin da ya faru wanda a cewar hukumar, sakacin jami’an ne ya haifar da akasin. Wata majiya ta ce jami’an da ke bakin aiki a…
Read More
Sabbin Naira: Gwamnonin APC 3 sun maka Gwamnatin Tarayya a kotu kan ƙarancin kuɗi

Sabbin Naira: Gwamnonin APC 3 sun maka Gwamnatin Tarayya a kotu kan ƙarancin kuɗi

Daga BASHIR ISAH Gwamnanonin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara sun maka Gwamnatin Tarayya a Kotun Ƙoli kan batun canjin kuɗi. Sun kai ƙara kotun ne inda suke neman kotu ta hana Gwamnatin aiwatar da cikakkun matakan da ta ɗauka dangane da sabbin kuɗaɗen. Ƙarar da suka shigar ta hannun lauyansu, AbdulHakeem Uthman Mustapha (SAN), gwannonin sun buƙaci Kotun Ƙoli da ta ba ikon dakatar dakatar da Gwamnatin Tarayya ko CBN da sauran bankuna dakatar da su daga hana kawo ƙarshen tsoffin takardun Naira na 200 da 500 da 1000. Waɗanda suka shigar da ƙara sun haɗa da Manyan Lauyoyi…
Read More
Sarkin Musulmi ya buƙaci sojojin sama su binciki kisan Nasarawa

Sarkin Musulmi ya buƙaci sojojin sama su binciki kisan Nasarawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Majalisar Jama’atu Nasril Islam, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya yi Allah-wadai da kisan makiyaya 47 da sojojin saman Nijeriya suka yi a Jihar Nasarawa bisa kuskure, tare da yin kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bincike waɗanda suka aikata laifin domin gurfanar da su gaban kuliya. Ƙungiyar ta JNI ta bakin babban sakatarenta, Dakta Khalid Abubakar-Aliyu, a wata sanarwa da ta fitar a Kaduna ranar Alhamis, ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta biya diyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa saboda asarar rayukan ’yan uwansu da suka yi…
Read More