Editor

9513 Posts
Kafuwar Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Kafuwar Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban Bankin Najeriya, wanda ake kira Central Bank of Nigeria (CBN), shi ne bankin da ke da ruwa-da-tsaki wajen gudanar da harkokin kuɗaɗen gwamnatin Jamhuriyyar Tarayyar Nijeriya a hukumance. Banki ne da doka ta kafa shi a shekarar 1958 sannan kuma ya kama aiki a ranar 1 ga watan Juli na shekarar 1959. Kafuwa: An kafa Babban Bankin Nijeriya a shekarar 1958 sannan kuma ya fara aiki a ranar 1 ga watan Juli na shekarar 1959. Doka: Tushen dokar da ta kafa wannan banki ita ce dokar Majalisar Tarayya ta shekarar 1958 wadda aka yi wa…
Read More
Kotun Ƙoli ta dakatar da hana amfani da tsohuwar Naira na wucin-gadi

Kotun Ƙoli ta dakatar da hana amfani da tsohuwar Naira na wucin-gadi

Daga BASHIR ISAH A ranar Laraba Kotun Ƙoli ta dakatar da yunƙurin Gwamnatin Tarayya na daina amfani da tsohuwar Naira daga ranar 10 ga Fabrairu, 2023. Tawagar alƙalai bakwai ƙarƙasbin jagorancin Mai Shari'a John Okoro ne suka yanke wannan hukuncin biyo bayan ƙarar da gwamnonin Kaduna da Kogi da Zamfara suka shigar. Kowacce daga jihohin da lamarin ya shafa ta shigar da ƙara inda ta nemi kotu ta dakatar da Gwamnatin Tarayya ta hannun Babban Bankin Ƙasa (CBN) ko kuma sauran bankuna daga matakin da aka ɗauka na daina karɓar tsohuwar Naira (200, 500 da 1000) daga ran 10 ga…
Read More
BIDIYO: Za mu ci gaba da amfani da tsohuwar Naira a Kaduna nan da shekara 4 – El-Rufai

BIDIYO: Za mu ci gaba da amfani da tsohuwar Naira a Kaduna nan da shekara 4 – El-Rufai

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce ba za a daina karɓar tsohuwar Naira, N200, N500 da N1000 ba a jihar har zuwa shekaru huɗu masu zuwa. Ya faɗi haka ne a cikin wani faifan bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta na zamani a ranar Laraba. "Ina muku alƙawari, duk ɗan jihar Kaduna da ke da tsohon kudi ya ci gaba da amfani da shi, za mu amsa daga nan har shekara huɗu," in ji shi. Kalli bidiyon don ƙarin bayani:
Read More
Nasarawa 2023: Zan bai wa masarautun gargajiya fifiko – Yakubu Maidoya

Nasarawa 2023: Zan bai wa masarautun gargajiya fifiko – Yakubu Maidoya

Daga JOHN D. WADA, A LAFIYA Ɗan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a Jam’iyyar NNPP, Alhaji Abdullahi Yakubu Maidoya, ya ce idan al’ummar jihar suka zaɓe shi a matsayin gwamnan jihar a zaɓen gwamnan jihar da ke tafe zai tabbatar ya inganta tare da ɗaukaka harkokin masarautun gargajiyar jihar baki ɗaya ta yadda za su yi daidai da zamani ba kamar yadda lamarin yake a yanzu ba. Yakubu Maidoya ya bayyana haka ne a ci gaba da kamfen ɗinsa da yake yi a lokacin da ya ziyarci masarautar Keana, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Keana da ke jihar. Da yake bayyana wa Sarkin…
Read More
Buhari ya kira taron Majalisar Ƙasa kan rashin fetur da ƙarancin sabon kuɗi

Buhari ya kira taron Majalisar Ƙasa kan rashin fetur da ƙarancin sabon kuɗi

Daga BASHIR ISAH Bayanai sun nuna Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kira taron gaggawa inda zai gana da masu ruwa da tsaki wanda zai gudana ranar Juma'a domin tattauna mafita dangane da matsalar rashin fetur da ƙarancin sabbin kuɗi gabanin babban zaɓe mai zuwa. Rahoto ya ce, yayin taron wanda za a gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa, ana sa ran Gwamnan CBN ya ba da bayanin halin da ake cike game da sabbin takardun Naira da sauransu. Kazalika, shi ma Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Mahmood Yakubu da Sufeto Janar na 'yan sanda, IGP Usman Alƙali Baba, za su…
Read More
2023: Maidoya ya gana da shugabannin NNPP na ƙananan hukumomi a Nasarawa

2023: Maidoya ya gana da shugabannin NNPP na ƙananan hukumomi a Nasarawa

*Ya buƙace su su riƙe amana Daga JOHN D. WADA, a LAFIYA Don tabbatar da nasarar jam’iyyar NNPP a duka matakai a jihar Nasarawa da ƙasa baki ɗaya, ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Nasarawa a inuwar jam’iyyar NNPP, Abdullahi Yakubu Maidoya, ya yi wani zama na musamman da duka shugabannin jam’iyyar na duka ƙananan hukumomi 13 da na gundumomin jihar. Zaman wanda aka yi a babban sakatariyar jam’iyyar dake garin Lafiya, babban birnin jihar, ya samu goyon bayan duka shugabannin ya kuma samu halarcin wasu jiga-jigan ‘yan jam’iyyar daga ciki da wajen jihar. Da yake jawabi, Yakubu Maidoya ya gode…
Read More
Dalilin IPMNAN kan dakatar da sayar da fetur a gidajen mai

Dalilin IPMNAN kan dakatar da sayar da fetur a gidajen mai

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Dillalan Fetur ta Nijeriya (IPMAN) ta dakatar da sayar da fetur a gidajen mai a faɗin ƙasa. Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin wasiƙar da ƙungiyar ta aike wa mambobinta mai ɗauke da sa hannun shugabanta, Mohammed Kuluwu da kuma kwanan wata 6 ga Fabrairun 2023. A cewar ƙungiyar, in ban da asara babu abin da manmobinta za su samu muddin suka ci gaba da sayar da fetur a cikin wannan yanayi. Wasiƙar ta ce, "Biyo bayan halin matsin da ake fuskanta wanda ya shafi hada-hadarmu da janyo mana asara, ana umartanku da ku dakatar da…
Read More
Kwamitin karɓar tallafin Abba Gida-gida a kano ya tara sama da miliyan N500

Kwamitin karɓar tallafin Abba Gida-gida a kano ya tara sama da miliyan N500

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar NNPP reshen Jihar Kano ya sami jimillar kuɗi Naira miliyan dari biyar da goma sha daya da naira dubu dari biyu da hamsin da bakwai domin gudanar da yakin neman zaɓe da sauran harkokin zabe da za a gudanar a ranakun 25 ga watan Fabrairu da 11 ga watan Maris 2023. Wannan na cikin wata sanarwa da babban mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen NNPP a Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana wa manema labarai ta ce, bayan taron liyafar cin abinci da jam’iyyar ta gudanar…
Read More
Abinda yake hana ƙauna tasiri a auren dole duk daɗewarsa

Abinda yake hana ƙauna tasiri a auren dole duk daɗewarsa

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a jaridarmu mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan mako za mu tattauna a kan dalilan da suke sanya a yi auren dole kuma duk da an ɗauki lokaci mai tsawo a cikinsa, ƙauna ba ta shigowa ta yi tasiri. Domin sai ka ga namiji ya yi shekaru masu yawa da macen da aka yi musu auren dole, ko auren haɗi, amma sai ka ga bayan shekaru ya dage sai ya ƙara aure. Ya auri zaɓinsa wace yake so. Idan ma kenan yana jin kunya ko nauyin iyayenta…
Read More
Girgizar ƙasar Siriya-Turkiyya: Yawan matattu ya kai 5000, gidaje 5775 sun rushe

Girgizar ƙasar Siriya-Turkiyya: Yawan matattu ya kai 5000, gidaje 5775 sun rushe

Daga BASHIR ISAH Kawo yanzu, kimanin mutum 5,000 aka tabbatar sun mutu, wasu dubbai sun jikkata a girgizar ƙasar da ta auku a Turkiyya da Siriya a ranar Litinin. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Mataimakin Shugaban Ƙasar Turkiyya, Fuat Oktay, da safiyar ranar Talata. Ya ce mutum 3,419 sun mutu yayin da 20,534 sun jikkata a Turkiyya. A ɓangaren Siriya kuwa, yawan waɗanda suka mutu ya ƙaru zuwa 1,602, wanda baki ɗaya jimillar ta kama 5,021. Hukumar kula da iftila'i ta ƙasar Turkiyya, ta ce rahotanni sun nuna gidaje 11,342 girgizar ta shafa, amma gidaje 5,775 ne aka…
Read More