Editor

9513 Posts
Hukumar Alhazan Jihar Kano ta soma bitar mako-mako ga maniyyata

Hukumar Alhazan Jihar Kano ta soma bitar mako-mako ga maniyyata

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Hukumar jin daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta ƙaddamar da fara gudanar da bitar mako-mako ga maniyyatan aikin Hajjin bana. Da yake jawabi a yayin taron, Kwamishinan ayyuka na musamman, Hon. Kabir Muhammad Tarauni da ya wakilci Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Ganduje, ya ce irin kulawa da Gwamnan Kano ke bai wa cigaban addini ya sa ake tsara bitar da wuri. Ya ce bitar ta ilmantar da da maniyyata ne dukkan nauyi da ya ɗoru a kan su na ibada da za su aiwatar don kyautata aikin Hajji da za su je. Kabiru Muhammad Tarauni…
Read More
Gobe Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta FAMSAS za ta yi bikin rantsar da sabbin ɗalibanta

Gobe Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta FAMSAS za ta yi bikin rantsar da sabbin ɗalibanta

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Shugaban Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta FAMSAS mai zaman kanta dake garin Keffi, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Keffi a jihar Nasarawa, Alhaji Mohammad Idris Lukumbogo ya ce a ƙoƙarinta na cigaba da samar wa al’ummar jihar da qasa baki ɗaya ingantataccen ilimin kiwon lafiya na zamani, Kwalejin ta FAMSAS ta kimtsa caf don gudanar da wani gagarumin taron ta mai muhimmanci mai kuma ɗimbin tarihi wato na rantsar da sabbin ɗalibanta da suka samu damar fara karatu a kwalejin na zangon karatun shekarar 2023 da ake ciki a gobe Asabar 11 ga watan Fabrairun shekarar 2023…
Read More
Girmama matasa da ba su dama zai kawo ci gaban Nijeriya – Farfesa Adamu Tanko

Girmama matasa da ba su dama zai kawo ci gaban Nijeriya – Farfesa Adamu Tanko

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Mataimakin Shugaban Jami'ar BUK, Farfesa Adamu Idris Tanko, ya ce akwai buƙatar dattawan Nijeriya, da shugabanin Nijeriya, kowa ya yi karatun tanutsu ta hanyar cewa wannan ba zamaninka ba ne ka bar wa yara matasa ka zama uba malami mai karantarwa da shawarwari ga matasa kamar yadda shugabar ƙasar Naizland, ta sauka da kanta, ya ce wani ya riƙe qasar ta yi iya nata ƙoƙarin, saboda kishin al'umma da ƙasar ta a lokacin da yake ganawa da manema labarai a harabar jami'ar dake birnin Kano a wannan lokaci. Haka kuma ya ce, "baiwar matasan Nijeriya,…
Read More
Lafiya lau za a yi zaɓukan 2023 ba tare da rikici ba – Monguno

Lafiya lau za a yi zaɓukan 2023 ba tare da rikici ba – Monguno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mai Bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, NSA, Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za a gudanar da zaɓen 2023 ba tare da rikici ba. Monguno ya bada wannan tabbacin ne yayin ganawarsa da Hukumar Zave Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC da kuma shugabannin hukumomin tsaro a ƙasar. Ya shawarci 'yan Nijeriya da su yi watsi da duk wani nau’i na ɓata-gari, labaran ƙarya da fargaba kan yadda za a gudanar da babban zaɓen 2023, yana mai cewa za a gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.…
Read More
Tinubu bai cancanci shugabancin Nijeriya ba, inji Abubakar Billy, jikan Tafawa Ɓalewa

Tinubu bai cancanci shugabancin Nijeriya ba, inji Abubakar Billy, jikan Tafawa Ɓalewa

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi A kwanakin baya ne dai, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, a cikin wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Chanels, ya yi tsokaci da cewar, akwai wasu jami’ai dake cikin Fadar Shugaban Ƙasa waɗanda ba su so Tinubu ya kasance ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar APC ba. Ya ce waɗannan mutane suna yin bultu don ganin Shugaba Muhammadu Buhari ya yi abinda ya dace. El-Rufa’i ya ce, “akwai wasu gungu a fadar shugaban ƙasa da suke yin da’awar mu faɗi zaɓe."  Wakilin Blueprint Manhaja na daga cikin wasu manema labarai da…
Read More
Zaɓe: Gwamnatin Tarayya ta rufe jami’o’i na makonni 3

Zaɓe: Gwamnatin Tarayya ta rufe jami’o’i na makonni 3

Daga WAKILINMU Gwamnatin Tarayya ta bai jami’o’in Nijeriya umarni kan su rufe daga ranar 22 ga Fabrairu zuwa 14 ga Maris saboda zaɓuɓɓukan da za a gudanar ran 25 ga Fabrairu da 11 ga Maris, 2023. Gwamnati ta ba da umarnin ne domin bai wa ɗalibai, malamai da saunran ma'aikata a jami'o'i damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓukan. Umarnin na ƙunshe ne cikin sanarwa mai ɗauke da kwanan wata 3 ga Fabrairu wadda Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta aike wa jami’o’i a faɗin ƙasa. Cikin sanarwar mai ɗauke da sa hannun Mataimakin Sakataren NUC, Dakta Chris Maiyaki,…
Read More
Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Naja’atu Bala Mohammed

Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Naja’atu Bala Mohammed

Daga FATUHU MUSTAFA Zuwa ga Gwaggo Naja'atu Bala Mohammed: Bayan dubun gaisuwa da fatan alheri, na saurari wata hira da kika yi, wacce ita ce ta farko, tun bayan da kika fice daga cikin tawagar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. A cikin wannan hira, kin bayyana cewa, kin fice ne, sakamakon fahimtar da kika yi na cewa, Asiwaju ba ya da wani tanadi da ya yi wa Arewa. A kan wannan nake da ja! Domin dai ni ganau ne ba jiyau ba. Domin a magana ta gaskiya, in har aka ce Asiwaju baya da wani tanadi da ya yi wa Arewa,…
Read More
Ba sai kana da jari ne za ka iya yin sana’a ba – Binta Tukur Nadada

Ba sai kana da jari ne za ka iya yin sana’a ba – Binta Tukur Nadada

"Sha'awa ta ga ƙirƙira ce ta sa ni yin sana'ar ƙera gadaje" Daga ABUBAKAR M. TAHIR Hajiya Binta Tukur Nadada 'yar asalin garin Bakori ce da ke Jihar katsina. Yar boko ce kuma mai sha'awar ƙirƙire-ƙirƙire, inda yanzu haka ta ke sana'ar ƙera kayan ɗaki irin su gado, kujeru da makamantan su. Hajiya Binta ta fito ne daga tsatson marigayi Makaman Katsina na Uku. Kuma a halin yanzu tana digirinta na uku kan yadda za a tallafa wa mutane su kafa kasuwancinsu don tsayawa da koafafunsu, wadda ta tabbatar ya fi raja'a ne ga matan Arewa. Yanzu haka Hajiya Binta…
Read More
Dubun masu tiransifa ta ƙarya ta cika a Kano

Dubun masu tiransifa ta ƙarya ta cika a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, a KANO Rundunar ‘yan sandan jiyhar Kano ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da damfarar wani mai shago a Sharaɗa da ke Ƙaramar Hukumar Binni ta jihar. Rahotanni sun nuna an kama waɗanda ake zargin, Mujihid Kabir da Abdu Imam da laifin damfara, sata da kuma kutse. Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da kama su a ranar Talatar da ta gabata, Ya ce, “Mun samu kiran gaggawa a ranar 2 ga watan Fabrairu daga Sharaɗa cewa wasu mutum biyu sun sayi shinkafa a wani shago inda suka…
Read More
Anya manufofin gwamnati na cigaban talakawa ne?

Anya manufofin gwamnati na cigaban talakawa ne?

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 'Yan Nijeriya na cigaba da fuskantar sauye sauye a ɓangaren siyasa, tattalin arziki da zamantakewa da aka jima ba a gani ba a ƙasar nan. Kusan hankalin kowa a farke yake, cikin tunanin me yake faruwa? Me zai faru? Wanne tasiri hakan zai yi a rayuwar mu? Ko ban yi bayani ba, na san wasu sun fara gano bakin zaren maganar da nake son nazarinta a wannan makon. Tun shigowar gwamnati mai ci ta shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ƙarƙashin Jam'iyyar APC a shekarar 2015, 'yan Nijeriya sun ga tsare tsare iri iri da gwamnati ta…
Read More