11
Feb
Daga WAKILINMU Sanata Emmanuel Bwacha ya lashe zaɓen fidda gwani na Jam'iyyar (APC) da aka maimaita a matsayin ɗan takarar gwamna na Jihar Taraba . Wannan na zuwa ne yayin da zaɓen gwamnoni ya ƙarato, wanda za a gudanar 11 ga Maris. A zaɓen da aka sake, Bwacha ya samu ƙuri'u 778 yayin da abokin hamayyarsa, Yusuf Yusuf ya damu biyar. Baki ɗaya, dalaget 796 aka tantance yayin zaɓen.
