Editor

9513 Posts
Gwamnatin Yobe ta ƙaryata kai wa jiga-jigan APC hari a wajen taro

Gwamnatin Yobe ta ƙaryata kai wa jiga-jigan APC hari a wajen taro

Daga WAKILINMU Gwamnatin Jihar Yobe, ta ƙaryata labarin da aka yaɗa a wasu kafafen yaɗa labarai cewa an yi wa gangamin yaƙin neman zaɓen Jam'iyyar APC ruwan duwatsu a Ƙaramar Hukumar Gashua da ke jihar. Darakta Janar na yaɗa labarai ga Gwamnan Yobe, Mamman Mohammed, ya ƙaryata faruwar haka, tare da cewa babu ƙamshin gaskiya a cikin lamarin. “Gangamin ya samu dubban mahalarta wanda ba taɓa ganin irinsa ba a tarihin siyasar garin Gashua. "Taron ya yi kyakkyawar tarba ga Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, Gwamna Buni da mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe. “Gwamna Buni ya ratsa taron zuwa kan…
Read More
Zaɓen 2023: Aski ya zo gaban goshi!

Zaɓen 2023: Aski ya zo gaban goshi!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Azancin zancen Hausawa na cewa aski in ya zo gaban goshi ya fi zafi duk da ba lalle kowa ya kan ji zafi don askin da a ke yi ma sa ya zo goshi ba. Gaskiya ma hakan ya danganta ga wanzamin da ya ke askin. Idan an samu goni ya jika sabulu da ɗan ruwa mai sanya ya shafa ya murza aska sai askin ya yi sanyi kuma har ma a riƙa hira tsakanin wanzamin da wanda a ke yi wa askin. Shin wannan zaɓen ya na zafi ko ba shi da shi a zahiri…
Read More
Ganduje ya rufe kanti a Kano saboda ƙin karɓar tsoffin kuɗu

Ganduje ya rufe kanti a Kano saboda ƙin karɓar tsoffin kuɗu

Daga HAMISU IBRAHIM a Kano Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya ba da umarnin rufe katafaren kantin zamanin nan, wato Wellcare Supermarket, saboda ƙin karɓar tsoffin takardun Naira 200, 500 da kuma 1000. Muƙaddashin Hukumar Kare Muradin Kwastoma na Jihar Kano, Dokta Baffa Babba Dan’Agundi ne ya bayyana haka ga manema labarai jim kaɗan bayan rufe kantin. A cewar Dan’Agundi, aiwatar da umarnin na Gwamna ya zama wajibi sakamakon shagon ya ƙi karɓar tsoffin kuɗi wanda hakan ya saɓa wa umarnin Gwamna Ganduje da ya ce a ci gaba da amfani da tsoffin Naira a jihar. Ya ƙara…
Read More
Cutar sanƙarau ta ɓulla a Jigawa – NCDC

Cutar sanƙarau ta ɓulla a Jigawa – NCDC

Daga BASHIR ISAH Shugaban Hukumar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa, Dokta Ifedayo Adetifa, ya ce hukumar ta yi tattaron gaggawa sakamakon ɓullar cutar sanƙarau a Jihar Jigawa. Dr Adetifa ya ce taron ya tattauna ƙalubale da kuma mafita dangane da ɓullar cutar a Jigawa. Shugaban NCDC ya bayyana haka ne a shafinsa na Tiwita a ranar Lahadi. A cewar masana, sanƙarau cuta ce wadda kan haifar da ƙagewar wuya idan ta kama mutum, wasu lokutan ma takan shafi ƙwaƙwalwa. Masanan sun ƙara da cewa, alamomin da ke nuni da kamuwa da wannan cuta sun haɗa da; zazzaɓi, ciwon kai,…
Read More
Buhari ya kafa majalisar bankwana da mulki

Buhari ya kafa majalisar bankwana da mulki

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya kafa majalisar da za ta lura da yadda zai miƙa mulki ga sabuwar zaɓaɓɓiyar gwamnatin farar hula a watan Mayu na 2023 bayan kammala zaɓen da za a gudanar a watan nan na Fabrairu, 2023, cikin nasara. Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, ne ya bayar da sanarwar a jiya, Alhamis, 9 ga Fabrairu, 2023, mai ɗauke da sa hannun Daraktan Yaɗa Labarai, Mista Willie Bassey. Sanarwar ta ce, shi kansa Sakataren Gwamnatin ne zai jagoranci majalisar tare da Shugaban Ma’aikata na Gwamnatin Tarayya da Solisita Janar kuma…
Read More
Gangamin APC ya gamu da cikas a Yobe

Gangamin APC ya gamu da cikas a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, a Damaturu Ɗaruruwan 'yan dabar siyasa sun haifar da cikas a gangamin yaƙin neman zaɓen Jam'iyyar APC na shiyya ta uku (Zome C). Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a garin Gashuwa, shalkwatar Ƙaramar Hukumar Bade da ke jihar Yobe, mahaifar Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya. An tsara aiwatar da gangamin ne bayan buɗe sabuwar kasuwar zamani wadda Gwamnan Jihar, Mai Mala Buni, ya gina a garin Nguru inda daga bisani aka hallara a Filin Agric da ke unguwar Katuzu a Gashuwa. Bugu da ƙari, tun a garin Nguru aka fara ganin alamun yi wa tawagar…
Read More
Barazanar matsalar tsaro ga zaɓen 2023

Barazanar matsalar tsaro ga zaɓen 2023

Assalam alaikum. Kamar yadda Ƙungiyar da ke hanƙoron tabbatar da ’yancin bil'adama ta Human Rights Watch ta ce rashin hukunta waɗanda aka kama da laifi a zaɓukan ƙasar na baya da kuma gazawar gwamnati na magance matsalar tsaro na barazana ga aiwatar da babban zaɓen ƙasar na 2023. A ranar 25 ga watan Fabrairu ne al'ummar Nijeriya za su zaɓi sabon shugaban ƙasa domin maye gurbin shugaba mai ci Muhammadu Buhari, wanda ke kammala wa'adin shugabancinsa, tare da na 'yan majalisar dokokin tarayya, bayan mako biyu kuma za su fita domin kaɗa ƙuri'arsu a zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun…
Read More
Ƙarancin fetur da gabatowar zaɓe

Ƙarancin fetur da gabatowar zaɓe

Duk da alqawarin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi na tabbatar da gudanar da sahihin zaɓe a wannan shekara, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta yi gargaɗin cewa matsalar ƙarancin man fetur da ake fama da shi na iya kawo cikas ga zirga-zirgar kayayyaki da ma’aikata a ranakun zaɓe, idan ba a gaggauta magance shi ba. Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana fargabar da ke tattare da zaɓen 2023 a wani taron tuntuvar juna da Ƙungiyar Ma’aikatan Sufurin Jiragen Ruwa ta Ƙasa (NURTW) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ruwa ta Nijeriya (MWUN) kan zaɓen da…
Read More
A bari a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun Naira – Majalisa

A bari a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun Naira – Majalisa

Daga BASHIR ISAH Majalisar Tarayya ta ce akwai buƙatar Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya bari a ci gaba da amfani da tsofaffi da sabobbin takardun Naira tare. Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ne ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan ganawarsu da Shugaba Muhammadu a ranar Juma'a. Ya ce yin hakan zai taimaka wajen sauƙaƙe wa 'yan ƙasa wahalar ƙarancin kuɗi da ake fuskanta a halin yanzu. “Mu a Majalisar Dattawa, da farko mun ɗauka babu wata matsala tattare da tsarin, kuma muna jin ce babu buƙatar ƙayyade wani wa'adi, a bari a ci…
Read More
Dalilin fuskantar ƙarancin sabbin takardun Naira – Emefiele

Dalilin fuskantar ƙarancin sabbin takardun Naira – Emefiele

Daga WAKILINMU Babban Bakin Nijeriya ta bakin shugabansa, Godwin Emefiele, ya bayyana dalilin da ya haifar musu da tsaiko wajen samar da sabbin takardun Naira da aka sauya wa fasali a wadace. A Emefiele, a halin yanzu Babban Bankin ba shi da halin buga sabbin takardun kudin da za su wadata kasar saboda takardun da ake buga kudin da su sun yanke. Ya yi wannan furuci ne a ranar Juma’a yayin da yake yi wa Majalisar Ƙasa jawabi kan batun sauya fasalin takardun Naira. Majiyar Jaridar Premium Times da ta halarci zaman Majalisar ta ruwaito cewa, Emefiele ya koka kan…
Read More