Editor

9513 Posts
Tarihin Sarkin Dutse, marigayi Mai Martaba Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi

Tarihin Sarkin Dutse, marigayi Mai Martaba Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Marigari Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi, CFR. Mutum ne mai ilimin addini da na zamani, ɗankasuwa, kuma mai son kyautatawa jama'arsa. Yana da jajircewa wajen ganin an aikata gaskiya a dukkan hali. Mutum ne mai son tafiye-tafiye. Rubutun da mai karatu zai karanta dangane da rayuwar Mai Martaba Sarki Nuhu Muhammadu Sanusi, an tsakuro shi ne daga littafin da shi Mai Martaba Sarki ya rubuta da hannunsa mai suna ‘The Days in My Life’. An haife ni da safiyar ranar Juma'a 5 ga watan Janairu na shekarar 1945 wanda ya yi daidai da…
Read More
Masarautar Zazzau ta yi sabbin naɗe-naɗe

Masarautar Zazzau ta yi sabbin naɗe-naɗe

Daga WAKILINMU Masarautar Zazzau ta naɗa ƙarin sabbin hakimai takwas tare da miƙa musu takardun fara aiki. Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ne ya ƙaddamar da sabbin hakiman a wani ƙwarya-ƙwaryan biki a fadarsa da ke birnin Zariya. An naɗa su ne bayan amincewar Gwmanan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ta hannun Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu ta jihar. Sanarwar da jami'in yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na masarautar, Abdullahi Aliyu Kwarbai, ya fitar ta nuna waɗanda naɗin ya shafa sun haɗa da: Alhaji Sufiyanu Umar Usman, Ƙarfen Dawakin Zazzau a matsayin Hakimin Pambegua, Mohammed Dahiru Dikko,…
Read More
Dandalin shawara: Wanda na sani a matsayin uba ke ƙoƙarin yi min fyaɗe

Dandalin shawara: Wanda na sani a matsayin uba ke ƙoƙarin yi min fyaɗe

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Salam. Ina yini. Don Allah wanga shi ne karo na uku Ina turo mi ki da tambayata, sai dai ban ji ke ce komai ba. Allah ba da wasa ni kai ba. Don Allah ki taimaka. Tun Ina da shekara tara, akwai wani ɗan'uwan babana da bai tava haihuwa ba, sai matatai ta nemi a bata ni ta riƙe. Ita lauya ce, kuma tana aiki. Tun da suka ɗauke ni, ba su tava nuna ba su suka haihe ni ba, ba ma kamar matar, saboda ni kaina wani lokaci har shagala ni kai kamar ita a…
Read More
Ni’imarki darajarki (4)

Ni’imarki darajarki (4)

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin kwalliya na jaridar al'umma Manhaja, sannunku da jimirin bibiyar wannan darasi da ya ɗauke mu tsayin sati huɗu. Kamar yadda muka yi alƙawarin kawo ma ku wasu daga ci gaban kayan da za su samar da ni'ima dawamamma ga mace, kuma kayan da ta ke da tabbacin tsafta da lafiyar su, kasancewar ita da kanta ne zata dinga haɗawa. Sai dai kafin nan, zan so in yi amfani da wannan dama in janyo hankalin mata kan illar shan maganin mata da ke bayar da ni'ima ta ɗai rana. Mata…
Read More
Dalilin soke taron Atiku a Ribas – PDP

Dalilin soke taron Atiku a Ribas – PDP

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP a Jihar Ribas, ya ce an soke gangamin kamfe na Atiku Abubakar da aka shirya gudanarwa a Fatakwal don kauce wa asarar rayuka. Shugaban Kwamitin a Jihar Ribas, Sanata Lee Maeba ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya shirya ranar Litinin a Fatakwal, babban birnin jihar. Maeba ya ce an kai wa mambobin PDP da magoya bayan Atiku hare-hare a tsakanin watanni ukun da suka gabata a jihar. Kazalika, ya yi zargin Gwamnatin Ribas ta rufe harkokin kasuwancin wasu jiga-jigan mambobin jam’iyyar masu mara…
Read More
Sanƙarau ta kashe mutum 20 a Jigawa

Sanƙarau ta kashe mutum 20 a Jigawa

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce cutar Sanƙarau ta kashe mutum 20 a faɗin jihar, lamarin da ya ɗaga hankalin jama'a da hukumomi a jihar. A cewar Babban Sakataren Ma'aikatar Lafiya ta jihar, Dr. Salisu Mu’azu, mutum 80 aka tabbatar da sun kamu da cutar daga cikin 360 da ake zargi, sannan ana fargabar ta kashe mutum 20 tun bayan ɓullarta a jihar. Sanarwar da Sakataren ya fitar ta ce, “Cikin alhini muke sanar da ɓullar cutar sanƙarau a Jihar Jigawa. “Mun tabbatar mutum 80 sun kamu da cutar, sannan ta yi ajalin mutum 20," in ji Mu'azu.…
Read More
Zaɓen 2023: Gwamnati ta rufe kwalejojin fasaha

Zaɓen 2023: Gwamnati ta rufe kwalejojin fasaha

Daga WAKILINMU Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin rufe duka kwalejojin fasaha da ke faɗin ƙasa har sai bayan babban zaɓe mai zuwa. Wannan na zuwa ne mako ɗaya bayan da Gwamnati ta ba da umarnin rufe ɗaukacin jami'o'in da ke faɗin ƙasar. Umarnin rufe makarantun na ƙunshe ne cikin takardar sanarwar da Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya ta aike wa hukumomi da shugabannin makarantun da lamarin ya shafa ta hannun Hukumar NBTE Wasiƙar, wadda Mr I. O Folorunsho ya rattaɓa wa hannu a madadin Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, mai ɗauke da kwanan wata 10 ga Fabrairu, an raba ta…
Read More
Da ɗumu-ɗumi: Buhari ya sake ganawa da Emefiele

Da ɗumu-ɗumi: Buhari ya sake ganawa da Emefiele

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da shugaban Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin. Wannan dai shi ne karo na uku da Shugaba Buhari ke ganawa da Emefiele tun lokacin da aka fara matsalar rashin kuɗaɗe a hannu 'yan Nijeriya, Bayan kammala ganawar, Emefiele bai ya ƙi amsa tambayoyin 'an jarida, inda ya fice daga Fadar ba da ɓata lokaci ba.
Read More
2023: Babu zaɓe a rumfunan zaɓe 240 – Yakubu

2023: Babu zaɓe a rumfunan zaɓe 240 – Yakubu

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ce zaɓe ba zai gudana ba a wasu rumfunan zaɓe 240 a faɗin ƙasa a zaɓe mai zuwa. Shugaban INEC na Ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a wajen ganawarsu da jam'yyun siyasa a ranar Litinin. A cewar Yakubu, hakan ya faru ne saboda babu wanda ya zaɓi ya kaɗa kuri'a a rumfunan zaɓen da lamarin ya shafa. Wannan na zuwa ne yayin da ya rage kwanaki 12 kafin baban zaɓen 2023. A cewar Yakubu babu wanda ya nuna sha'awar kaɗa ƙuri'a a rumfanar yayin rijistar zaɓen da aka…
Read More
DSS ta gayyaci Fani-Kayode kan zargin juyin mulki

DSS ta gayyaci Fani-Kayode kan zargin juyin mulki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar tsaro ta DSS ta gayyaci jigo a Jam'iyyar APC, Femi Fani-Kayode, kan zargin da ya yi cewa an shirya yunƙurin juyin mulki, kamar yadda jaridar News Point Nigeria ta rawaito. Fani-Kayode ya ba da sanarwar gayyatar da DSS ta yi masa ne cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar Litinin. A cewarsa babu abin da yake tsoro, don haka zai amsa gayyatar ba tare da wani haufi ba. Ya ƙara da cewa, babu abin da zai hana shi ci gaba da bayyana ra'ayinsa muddin yana raye. Ya ce, “Kwanaki uku da suka…
Read More