Editor

9513 Posts
Mauludin Majma’u Niass na nuna ƙauna da haɗin kai ne – Shehi Tijjani Auwalu

Mauludin Majma’u Niass na nuna ƙauna da haɗin kai ne – Shehi Tijjani Auwalu

Mauludin bana, wanda ƙungiyar Majma’u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyas ta shirya, shi ne mauludi karo na 37 wanda ya yi daidai da shekarun Sheikh Ibrahim Niass shekara 123. Gagarumin mauludi ne da ake shirya shi duk shekara don tunawa da Sheikh Ibrahim Niass da gabatar da wasu ayyuka na musamman da tunasarwa ga mabiya ɗariƙar Tijjaniya. A wannan shekarar, za a gabatar da mauludin ne ranar 18 ga Fabrairu, 2023, a Jihar Kebbi idan Allah ya yarda. Don jin taƙaitaccen tarihin wannan mauludin da ƙudirce-ƙudircen da aka tanada da muhimmancin mauludin a wurin al’umma musamman mabiya Ɗariƙar Tijjaniya da Faira,…
Read More
Gangamin zaɓen 2023: APC ta bayyana gamsuwarta da goyon bayan al’ummar Jihar Yobe

Gangamin zaɓen 2023: APC ta bayyana gamsuwarta da goyon bayan al’ummar Jihar Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Shugaban Jam'iyyar APC na Jihar Yobe, Alhaji Muhammed Gadaka ya nemi haɗin kan dukkan magoya bayan Jam'iyyar APC a Yobe ta Kudu domin samun nasarar babban zaɓe mai zuwa na 2023. Shugaban Jam’iyyar ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi a yaƙin neman zaɓen da Jam’iyyar APC ta gudanar a shiyya ta biyu (Zone B), a filin wasa na Dabo Aliyu da ke ƙaramar hukumar Potiskum a Jihar Yobe. Gadaka ya bayyana cewa, sai ta hanyar cikakken haɗin kai da goyon bayan al’ummar yankin ne Jam’iyyar APC za ta samu nasarar lashe…
Read More
Yadda za ku kai rahoton masu sayar da sabbin takardun Naira

Yadda za ku kai rahoton masu sayar da sabbin takardun Naira

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya fitar da wasu hanyoyi domin bai wa 'ya ƙasa damar kai rahoton masu sana'ar POS da ke cajin fitar hankali idan an zo cire kuɗi. Darakta a CBN, Mr Joseph Omayuku, shi ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da suka shirya ranar Talata a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa. Omayuku ya gargaɗi masu wannan hali da su daina, kana ya shawarci jama'a da su yi amfani da waɗannan hanyoyi na ƙasa wajen kai rahoton duk wani mai POS da aka samu yana karɓar caji wuci misali: 07002255226; Telephone Ext: 711025…
Read More
A yi aiki da hankali wajen zaɓen shugabanni nagari

A yi aiki da hankali wajen zaɓen shugabanni nagari

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Duk da ƙalubalen tsaro da ake cigaba da fuskanta a wasu sassan ƙasar nan da suka haɗa da matsalar hare-hare kan ƙauyawa da satar jama'a, daga yankin Arewa maso Yamma, ga cigaba da kai hare-hare kan ofisoshin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa a wasu jihohin Kudu maso Gabashin ƙasar nan, sai kuma matsala ta baya-bayan nan ta hare-hare da wasu fusatattun 'yan Nijeriya ke kai wa kan bankuna, sakamakon halin matsi da talakawa suka shiga na rashin kuɗi a hannu don gudanar da kasuwanci da wasu harkokin rayuwa, a dalilin sauyin kuɗi da tsare-tsaren gwamnati, babu alamun…
Read More
HOTUNA: Khalifah Sanusi II ya shiga Kano a karon farko bayan barin sarauta

HOTUNA: Khalifah Sanusi II ya shiga Kano a karon farko bayan barin sarauta

A rana Laraba, Sarkin Kano na 14, Kalifah Muhammadu Sanusi II ya kai wa mahaifiyarsa, Hajiya Hafsat Aminu, ziyara a gidanta da ke kusa da masallacin Juma'a na Dangi a Birnin Kano. Khalifah Sanusi yana kan hanyarsa ta zuwa Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa, ne daga Legas, amma hazo ya hana shi ƙarasa wa filin jirgin sama dake Dutse, inda ya yi saukar gaggawa a Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano dake Jihar Kano. Ziyarar tasa taƙaitacciya ce inda, bayan ya yi sallar Azahar ya hau jirgi ya koma Legas. Majiyar Blueprint Manhaja ta ce, zai je Dutse ne, don…
Read More
Har yanzu CBN bai sakar wa INEC kuɗaɗe ba – Kwamishina

Har yanzu CBN bai sakar wa INEC kuɗaɗe ba – Kwamishina

Daga BASHIR ISAH Yayin da ya rage kwanaki kaɗan kafin zaɓen 2023, har yanzu Babban Bankin Nijeriya (CBN) bai sakar wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), kuɗaɗen da take buƙata domin tura kayayyakin zaɓe zuwa sassan ƙasa ba. A makon jiya Shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya gana da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, inda suka tattauna yiwuwar bai INEC sabbin kuɗin da za ta yi amfani da shi wajen tura kayan zaɓe zuwa sassa. Inda a nan Emefiele ya bai wa INEC tabbacin ba zai bari a yi wa CBN kallon ana amfani da shi wajen yi wa…
Read More
Buhari ya tsawaita wa’adin tsohuwar N200

Buhari ya tsawaita wa’adin tsohuwar N200

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince a ci gaba da amfani da tsohuwar N200 nan da wata biyu. Ya bayyana haka ne yayin jawabin da ya yi wa 'yan ƙasa kai tsaye da safiyar Alhamis. Buhari ya ce ya tsawaita wa'adin amfani da N200 ne domin rage wa 'yan ƙasa raɗaɗin ƙarancin kuɗin da ake fuskanta a faɗin ƙasa. A cewarsa, za a ci gaba da amfani da N200 ne daga ran 10 Fabrairu zuwa 10 ga Afrilun 2023. Sai ƙarin wa'adin in ji Buhar, bai shafi tsoffin N500 da N100 ba. Shugaban ya ce ƙofar CBN…
Read More
Tsoffin kuɗi: Gwamnatin Kaduna ta sake shigar da ƙara kan Gwamnatin Tarayya

Tsoffin kuɗi: Gwamnatin Kaduna ta sake shigar da ƙara kan Gwamnatin Tarayya

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Kaduna, ta hannun lauyanta Abdulhakeem Mustapha SAN, ta shigar da ƙara kan Gwamnatin Tarayya saboda rashin kiyaye umarnin kotu. Wannan na zuwa ne kwanaki bayan da Gwamnatin Kaduna tare da takwarorinta Kogi da Zamfara suka maka Gwamnatin a Kotun Ƙoli dangane da matakin canjin kuɗin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ɗauka wanda hakan ya haifar da ƙarancin kuɗi a faɗin ƙasa. Yayin zaman kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Justice Inyang Okoro, Mustapha musta ya ja hankalin kotun kan zargin da ya yi cewa Gwamnatin Tarayya ba ta martaba umarnin da kotun ta bayar a…
Read More
Takardun kuɗi: CBN ya ce ba zai yi biyayya ga Kotun Ƙoli ba

Takardun kuɗi: CBN ya ce ba zai yi biyayya ga Kotun Ƙoli ba

*Ya ce duk mai tsohon kuɗi ya kai CBN Daga AISHA ASAS Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ce tsofaffin takardun kuɗi na N200, N500 da kuma N1000 sun daina amfani a hukumance tun daga ran 10 ga Fabrairu, 2023. Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban CBN a Bauchi, Haladu Idris Andaza, yayin zantawarsa da manema labarai ranar Litinin a garin Bauchi. Ya ce, “A tsakanin awowi 24 da suka gabata, mun samu tambayoyi da yawa daga wajen mutane game da batun tsoffin kuɗi." A cewarsa, "domin kawar wa jama'a shakku, muna sanar da cewa a shirye CBN yake…
Read More
Jerin mazaɓu 240 da INEC ta ce ba za a gudanar da zaɓe a cikinsu ba

Jerin mazaɓu 240 da INEC ta ce ba za a gudanar da zaɓe a cikinsu ba

Daga WAKILINMU Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta fitar da jerin sunayen mazaɓun da ta ce zaɓe ba zai gudana a cikinsu ba saboda rashin rijistar masu kaɗa ƙuri'a. Tun da fari, Shugaban INEC na Ƙasa, Mahmood Yakubu, ya bayyana a ranar Litinin cewa mazaɓun da lamarin ya shafa ba su da mutum ko guda da aka yi wa rijistar zaɓe a ƙarƙashinsu. A cewarsa, baki ɗaya mazaɓu 176,606 ake da su a faɗin ƙasa. Ya ƙara da cewa, waɗanda aka sauya wa mazaɓa za su samu saƙon tes ta waya mai ɗauke da bayanin mazaɓar da aka tura mutum…
Read More