Editor

9513 Posts
APC ta dakatar da ‘yar takarar gwamnanta a Adamawa

APC ta dakatar da ‘yar takarar gwamnanta a Adamawa

Daga BASHIR ISAH Shugabancin Jam'iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Yola ta Kudu a Jihar Adamawa ta dakatar da mai yi wa jam'iyyar takarar gwamna a jihar, Sanata Aishatu Ahmed Dahiru Modibbo (Binani), daga jam'iyyar. Wasiƙar dakatarwar wadda ta samu sa hannun jami'an jam'iyyar 21, ta nuna an ɗauki matakin dakatar da Binani na tsawon wata shida daga jam'iyyar ne saboda zargin rashin biyayya ga kotu da ake yi mata. Kazalika, shugabannin jam'iyyar sun zargi Binani da haddasa ɓangaranci da rarraban kan mambobin jam'iyyar. Wannan na zuwa ne yayin da ya rage 'yan kwanaki kafin zaɓen gwamnoni a faɗin ƙasa. Ga…
Read More
CBN ya ƙaryata bai wa bankuna damar karɓar tsoffin N500 da N1000

CBN ya ƙaryata bai wa bankuna damar karɓar tsoffin N500 da N1000

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Nijeriya ya ce hankalinsa ya kai kan wasu saƙonnin ƙarya da ake yaɗawa inda aka ce bankin ya bai wa sauran bankuna damar karɓar tsoffin takardun N500 da N1000. Cikin sanrwar manema labarai da ya fitar da yammacin Juma'a, CBN ya ce wannan batu ba gaskiya ba ne. Domin kwaranye wa mutane kokwanto, CBN ya ce N200 kaɗai aka yarda a ci gaba da amfani da ita kamar yadda Shugaban Ƙasa ya sanar a jawabinsa da ya gabatar ranar Alhamis, 16 ga Fabrairu. Kuma ƙarin wa'adin da aka yi wa N200 zai yi aiki ne…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: CBN ya umarci bankuna su karɓi N500 da N1000

Da ɗumi-ɗumi: CBN ya umarci bankuna su karɓi N500 da N1000

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umarci bankuna su fara karɓar tsoffin takardun N500 da N1,000 daga hannun jama'a nan take. Sai dai, CBN ya sharɗanta cewa Naira 500,000 ita ce mafi girman abin da bankunan za su karɓa amma ban da abin da ya haura haka. Majiyarmu ta ce CBN ya ɗauki wannan mataki ne domin sauƙaƙe wa jama'a wahalar zuwa rassan CBN a faɗin ƙasa don mayar da tsofaffin kuɗin. Wani jami'in CBN ya ce, "Ku tafi bankunanku, amma ku tabbatar kun cike fom kafin ku tafi. Ku je da kebaɓɓun lamɓoɓin da kuka samu. "Bankuna…
Read More
Buhari ya tafi Habasha ana tsaka da balahirar canjin kuɗi

Buhari ya tafi Habasha ana tsaka da balahirar canjin kuɗi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tafi birnin Adis Ababa na ƙasar Habasha domin halartar taron zaman lafiya na Mungiyar Tarayyar Afrika (AU) karo na 36. A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar, ta ce, Buhari ya bar Nijeriya ne a Alhamis, 16 ga Fabrairu, 2023. Fadar Shugaban Ƙasar ta kuma ce, a yayin ziyarar, Shugaba Buhari zai halarci taron tattaunawa kan matsaloli da ke addabar ƙasashen yammacin Afirka, tare da shugabannin ƙasashen. Zai kuma halarcin zaman shugabannin ƙasashen ECOWAS, kuma zai gabatar da jawabai, kafin daga bisani ya dawo Abuja ranar Litinin. Buhari kai…
Read More
Farashin kaya ya tashi saboda ƙarancin Naira na cigaba da tsananta

Farashin kaya ya tashi saboda ƙarancin Naira na cigaba da tsananta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya sake tashi zuwa matsayi mafi girma da kashi 21.82 a watan Janairu daga kashi 21.34 cikin ɗari a watan Disambar bara. Wannan na zuwa ne a rahoton baya-bayan nan da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar ranar Laraba, 15 ga Fabrairu, 2023. Sabon ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ya zo ne a daidai lokacin da ’yan Nijeriya ke fuskantar rashin matsalolin tattalin arziki sakamakon ƙarancin kuɗin da aka yi wa kwaskwarima na Naira. Wannan ƙaruwar na Janairu yana nuna ƙaruwar kashi 0.47 idan aka kwatanta da 21.34 da…
Read More
Taron tunawa da marubuci Mahmoon Baba-Ahmed ya yi armashi

Taron tunawa da marubuci Mahmoon Baba-Ahmed ya yi armashi

Daga AISHA ASAS Kamar yadda Manhaja ta shelanta a makon da ya gabata cewa, shahararriyar ƙungiyar nan ta marubata da ke Jihar Kaduna, wato Ƙungiyar Marubuta Alƙalam ta shirya tsaf don gudanar da taro na musamman don tunawa da fitacce kuma shahararren ɗan jarida kuma marubuci, marigayi Mahmoon Baba-Ahmed, wanda ya kasance jagaba kuma ginshiqi na cigaban da ƙungiyar ta samu. Ƙungiyar mai ɗauke da manyan marubutan da Jihar Kaduna ke alfarahi da su, ta sanar da ƙaddamar da litatafin marigayin na ƙarshe, wanda ya rubuta, amma bai samu damar bugawa kafin Allah Ya ɗauki ransa ba, duk dai a…
Read More
Masu sayar da Naira za su fuskanci ɗauri a gidan yari – CBN

Masu sayar da Naira za su fuskanci ɗauri a gidan yari – CBN

Daga AMINA YUSUF ALI A yayin da ake tsaka da halin matsi a sakamakon canjin kuɗin Nijeriya, Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya sha alwashin cafkewa da gurfanar da duk wani mai POS ko makamancinsa da aka samu da sayar da takardun Naira a matsayin kuɗin hada-hada (cajis). CBN ya ja kunne cewa, wannan lafi ne da yake da alaƙa da rashawa kuma laifi ne da zai iya sa a kulle mutum a gidan kaso. A cewar babban bankin, an yarda da biyan kuɗin ladan hada-hada wanda ake cewa cajis. Kuma a cewar sa, ba a haramta wannan ba. Amma wannan…
Read More
Benzema ya kafa tarihin yawan cin ƙwallaye a La Liga

Benzema ya kafa tarihin yawan cin ƙwallaye a La Liga

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Karim Benzema ya kafa tarhin zama na biyu a yawan cin ƙwallaye a gasar La Liga a Real Madrid. Ranar Laraba, Real ta doke Elche 4-0 a wasan mako na 21 a gasar La Liga a Santiago Bernabeu. Marco Asensio ne ya fara cin awallo, sai Karim Benzema ya zura biyu a raga duk a bugun fenariti, sanan Luka Modric ya ƙara na huɗu Benzema ya ci ƙwallo 230 kenan, shine na biyu a yawan ci wa Real Madrid ƙwallaye a La Liga, ya haura Raul mai riƙe da gurbin. Cristiano Ronaldo kyaftin tawagar Portugal shi…
Read More
Sharholiyar ranar masoya fasiƙanci ne – Sheikh Moh’d Aliyu

Sharholiyar ranar masoya fasiƙanci ne – Sheikh Moh’d Aliyu

Daga MOH BELLO a Zariya Limamin masallacin Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi dake Ƙofar Gayan Low-cost cikin Ƙaramar Hukumar Zariyan Jihar Kaduna, Sheikh Muhammad Aliyu ya gargaɗi Musulmi da su guji danganta kansu da sharholiyar ranar masoya wanda ake yi 14 ga Fabrairun kowace shekara. Ya yi wannan gargaɗin ne a cikin hudubarsa ta ranar Juma'ar makon da ya gabata, inda malamin ya ce wannan sharholiyar (valentine) ya saɓa wa koyarwar addinin Musulunci, "don haka ahir ɗin dukkan Musulmi." Sheikh Muhammad Aliyu ya ce dukkan yin wannan ta ranar masoya waɗanda suka jiɓanci sheɗan ne. "Bikin sharholiyar (valentine day) fasiƙanci ne,…
Read More
Zaɓen 2023: FRSC za ta bada goyon baya don samun nasara: Kwamanda Auwalu Mohammed

Zaɓen 2023: FRSC za ta bada goyon baya don samun nasara: Kwamanda Auwalu Mohammed

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Kwamandan Hukumar Kula da Manyan Hanyoyi da Kiyaye Haɗura ta Ƙasa, (FRSC), reshen Ƙaramar Hukumar Keffi a Jihar Nasarawa, Auwalu Magaji Mohammed, ya ce a shirye hukumar take shiyyar ta bada nata gagarumar gudunmawa don tabbatar da nasarar zavukan gama-gari na shekarar 2023 dake tafe a jihar da ƙasa baki ɗaya. Kwamanda Auwalu Magaji Mohammed ya bayyana haka ne alokacin da yake tattaunawa da wakilin Blueprint Manhaja a ofishinsa dake garin Keffi hedikwatar ƙaramar hukumar Keffi a jihar ranar Laraba 15 ga Fabrairun shekarar 2023 da ake ciki. Ya ce ba shakka kamar sauran…
Read More