Editor

9513 Posts
Tattalin arziki da batun sake fasalin Naira

Tattalin arziki da batun sake fasalin Naira

Rashin aiwatar da manufofin sake fasalin Naira ya yi tasiri sosai ga tattalin arziki da jama'a. A saboda haka qarancin takardun kuɗin na naira ya ƙara taɓarɓara rayuwar ’yan Nijeriya. Har ila yau, matsalar man fetur ma na ƙara dagula al'amura a ƙasar. Bayan wannan kuma, ’yan Nijeriya na kokawa da matsalar wutar lantarki da hauhawar farashin kayayyaki. Hakan dai na zuwa ne duk da jinkirin da Kotun Ƙoli ta yi biyo bayan umarnin wucin gadi da ta bayar na hana babban bankin ƙasar CBN ci gaba da aiwatar da wa’adin da ya ɗiba a ranar 10 ga watan Fabrairu…
Read More
Bayan wata 11, an sako ma’aikacin lafiyar da aka yi garkuwa da shi a Borno

Bayan wata 11, an sako ma’aikacin lafiyar da aka yi garkuwa da shi a Borno

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Maiduguri 'Yan bindiga sun sako ma'aikacin kiwon lafiya, Bulama Gaidam, wanda suka yi garkuwa da shi kimanin watanni 11 da suka gabata a Jihar Borno. Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan T'ta'addan sun saki Bulama ne a garin Gubio kana daga bisani aka wuce da shi zuwa Maiduguri domin miƙa shi ga iyalansa. Sai dai rahotannin ba su bayar da cikakken bayani ba kan ko an biya kuɗin fansa kafin a sako shi, ko ba a biya ba. An yi garkuwa da Bulama ne tun a cikin watan Maris na 2022, a lokacin da mayaƙan ISWAP suka kai…
Read More
Jirgin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima ya sauka Borno

Jirgin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima ya sauka Borno

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Maiduguri Ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu tare da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima da wasu gwamnoni biyar sun yi wa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno tsinke domin gudanar da yaƙin neman zaɓe. Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, da takwarorinsa na jihohin Yobe da Gombe, haɗi da jiga-jigan gwamnatin Jihar Borno, su ne tarbi tawagar ɗan takarar da ƙusoshin Jam'iyyar APC yayin gangin da ya gudana ran Asabar. Jim kaɗan da saukarsa a Maiduguri, Tinubu da jiga-jigan jam'iyyar APC suka shiga tattaunawa ta musamman da masu ruwa da tsaki a babban ɗakin taro…
Read More
Ƙarancin Naira da man fetur barazana ce ga takarar Tinubu – Gbajabiamila

Ƙarancin Naira da man fetur barazana ce ga takarar Tinubu – Gbajabiamila

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya danganta matsalar da ake fuskanta a halin yanzu na ƙarancin man fetur da ƙarancin Naira ka iya daƙile nasarar ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu na cin zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu. Gbajabiamila ya bayyana haka ne a Legas ranar Talata a lokacin ƙaddamar da shirin raba motocin sufuri mai taken: ‘Gbaja Ride’ ga mazaɓarsa ta Surulere. Motocin bas guda 35 masu saukin farashi za su riƙa bin hanyoyi daban-daban a Surulere da kewaye. “A matsayina na wakilinku kuma mai magana da yawunku, Ina…
Read More
Gwamnatin Jihar Katsina ta janye ƙarar da take wa tsohon gwamnan jihar

Gwamnatin Jihar Katsina ta janye ƙarar da take wa tsohon gwamnan jihar

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta janye ƙarar da ta shigar gaban kotu, inda take zargin tsohon gwamnan jihar Ibrahim Shehu Shema da kuma tsohon shugabannin ƙananan hukumomin jihar Ibrahim Lawal Ɗankaba bisa zargin karkatar da Naira biliyan 11 daga asusun ƙananan hukumomin jihar. Daraktan yaɗa labarai na ma'aikatar shari'a Abdulrahman Umar ya bayyana haka lokacin da yake yi wa manema labarai bayani dangane da lamarin. Ya bayyana cewar janye ƙarar ya biyo bayan wata takarda da gwamnatin jihar ta aike wa kotun da aka shigar da ƙarar gabanta. Ya ci gaba da cewa kotu ta amince…
Read More
Girgizar ƙasar Turkiyya: An gano gawar Christian Atsu

Girgizar ƙasar Turkiyya: An gano gawar Christian Atsu

Daga BASHIR ISAH An gano gawar tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafar ƙasar Ghana, Christian Atsu, wanda girgizar ƙasa ta rutsa da shi a Turkiyya. Kafar yaɗa labarai ta Turkiyya ta rawaito cewa, an gano gawar ɗan wasan ne ranar Asabar a ƙarƙashin ɓuraguzan ginin da ya rushe kamar yadda manajansa ya bayyana. Da fari rahotanni sun nuna an ceto marigayin kwana ɗaya da aukuwar iftila'in, amma a ƙarshe ya zamana ba gaskiya ba ne. Sai a ranar Asabar manajan marigayin a Turkiyya, Murat Uzunmehmet, ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta DHA cewar an gano gawar marigayin a ƙarƙashin ɓuraguzan…
Read More
An bankaɗo asirin wani kamfanin Isra’ila da ya shahara wajen sauya zaɓen ƙasashe

An bankaɗo asirin wani kamfanin Isra’ila da ya shahara wajen sauya zaɓen ƙasashe

Wasu kamfanonin yaɗa labaran ƙasashe, sun yi haɗin gwiwa wajen bankaɗo ayyukan wani kamfani da aka yi wa laƙabi da Team George wanda ya ƙware wajen murɗa zaɓe da kuma yada farfagandar da za ta tayar da tarzoma a zaɓuɓɓukan ƙasashen duniya. Bayan kafar yaɗa labaran da ta gudanar ta gano cewa kamfanin na shirin Murɗa labarai sama da 30 afaɗin duniya, cikin ƙasashen da ke shirin zaɓe a baya-bayan nan. Kamfanin mallakin tsohon sojan ƙasar ta Isra’ila Tal Hanan mai shekaru 50, ya ƙware wajen murɗa zaɓuɓɓuka ta hanyar shiga rumbunan tattara sakamakon zaɓen hukumomin zaɓe da kuma aringizo…
Read More
Mata sun koka da rashin armashin Ranar Masoya saboda ƙarancin Naira

Mata sun koka da rashin armashin Ranar Masoya saboda ƙarancin Naira

Daga AMINA YUSUF ALI Bincike ya nuna cewa, ƙarancin tsabar Naira ya yi matuƙar rage armashi ga bikin ranar masoya na bana. A ranar Larabar da ta gabata, 14 ga Fabrairu, 2023, ne dai wasu mata ma'aikata mazauna Birnin Tarayyar Abuja suka koka da yadda ƙarancin takardun Naira ya hana su samun kyautar Ranar Masoya daga mazajensu da kuma samun damar fita shagalin raya soyayya.  Wani ɓangare kuma na matan da suka zanta da manema labarai sun bayyana yadda ƙarancin takardun Nairar ya hana su samun damar fita yawon shaƙatawa da mazajensu a ranar masoya.  Ita dai ranar masoya wani…
Read More
Ku jure zafin ƙarancin Naira don zai wuce – Roƙon Buhari ga ’yan Nijeriya

Ku jure zafin ƙarancin Naira don zai wuce – Roƙon Buhari ga ’yan Nijeriya

*An bankaɗo Naira Tiriliyan 2.1 da aka ɓoye Daga AMINA YUSUF ALI Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana adadin yawan Nairorin da aka ɓoye waɗanda gwamnatinsa ta bankaɗo tun da CBN ya fara dokar canjin fasalin takardun Naira a Nijeriya. Sannan kuma ya roƙi 'yan Nijeriya a kan su zama masu haƙurin jure wahalhalun da dokar ta samar. A cewar Buhari, gwamnaninsa ta samu nasarar bankaɗo aƙalla Naira tiriliyan 2.1 aka ɓoye ba a bankuna ba. Tun daga lokacin da gwamnatin ta sanya dokar sauya fasalin kuɗi.  Shugaban ƙasar ya yi wannan jawabi a ranar Alhamis ɗin 16 ga watan Fabrairu, 2023…
Read More
Bankuna sun zama gurare mafi hatsari a Nijeriya, inji Birtaniya

Bankuna sun zama gurare mafi hatsari a Nijeriya, inji Birtaniya

*Ta gargaɗi ’yan ƙasarta da su guji zuwa bankuna Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙasar Birtaniya ta sake fitar da wata sanarwar bada shawara ga 'yan ƙasarta mazauna Nijeriya game da zuwa bankuna da ziyartar wasu jihoji a faɗin Nijeirya, na biyu a cikin watanni huɗu. A cikin bayanin da aka sabunta ranar Laraba, Ofishin Harkokin Waje, FCDO, ya yi gargaɗi ga ’yan ƙasar Birtaniya a Nijieriya game da zuwa wuraren da akwai bankuna da ATM. An yi nuni da cewa sake fasalin Naira da babban bankin Nijeriya ya yi tare da fitar da sabbin takardun kuɗi na N200, N500 da…
Read More