20
Feb
Daga BASHIR ISAH Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu tare da Ƙungiyar Gwamnoni (PGF), sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi biyayya ga umarnin Kotun Ƙoli kan batun canjin kuɗi. Kiran na zuwa ne a lokacin da Adamu ya yi zama da gwamnonin na APC ranar Lahadi a Abuja kan 'yar tsamar da ke tsakanin gwamnonin da Fadar Shugaban Ƙasa a jam'iyyar. Da fari Kotun Ƙoli ta bai wa CBN umarnin dakatar da aiwatar da wa'adin daina amfani da tsoffin kuɗi, wato N200, N500 da kuma N1,000 amma Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya ce babu gudu…
