06
Feb
*Ya ce, salon yaƙi da cin hanci da bunƙasa arziki ne*Mun daidaici wannan lokacin ne da gayya, inji shi Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana jimaminsa kan yadda ’yan Nijeriya ke shan azaba sakamakon canjin fasalin manyan takardun Naira, yana mai bayyana cewa, shan azabar ya zama wajibi matuƙar Nijeriya ta na son ta kawo ƙarshen matsalar annobar cin hanci da rashawa da ta yi kaka-gida a ƙasar da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasar. Kalaman na Shugaban Ƙasa sun fito ne daga bakin Ministar Kuɗi da Tsare-tsaren Ƙasa, Hajiya Zainab Ahmed, bayan kammala zaman…
