05
Feb
Daga WAKILINMU Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC, Alhaji Bola Ahmed Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyya ga shugannin ɗarikar Tijjaniyya da kuma iyalan mabiya ɗariƙar su 19 da aka kashe a ƙasar Burkina Faso. Rahotanni sun nuna cewa an kashe mutanen ne 'yan Nijeriya a ranar Laraba a kan hanyar su ta zuwa ƙasar Senegal domin ziyara. A wata sanarwa da mai taimakawa Asiwaju Tinubu a kan yaɗa labarai, Abdulaziz Abdulaziz ya sanyawa hannu, ɗan takarar shugaban ƙasar ya nuna baƙin cikin sa kan abinda ya faru. "Wannan abin baƙin ciki ne a ce mutane basu ji ba…
