03
Feb
Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga 'yan Nijeriya da su ba shi kwana bakwai domin kawo ƙarshen matsalar ƙarancin kuɗin da ake fuskanta a ƙasa sakamakon canjin kuɗin da CBN ya yi. A wata sanarwa da ya fitar, mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Femi Adesina, ya ce Buhari ya bayyana haka ne yayin ganawarsu da ƙungiyar gwamnoni ta Progressive Governors Forum ranar Juma'a a Fadar Shugaban Ƙasa. Gwamnonin sun ziyarci Buharin ne domin tattauna mafita dangane da ƙarancin kuɗin da ake fama da shi a ƙasa baki ɗaya wanda a cewarsu lamarin na barazana…
