Editor

9513 Posts
Bayan tsaikon wata takwas, jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya fara aiki

Bayan tsaikon wata takwas, jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya fara aiki

Daga BASHIR ISAH Bayan shafe watanni takwas ba ya aiki, jirgin saƙan Abuja-Kaduna ya fara aiki a ranar Litinin. Jirgin ya dakatar da aiki ne tun wata takwas da suka gabata sakamakon harin 'yan bindiga. Manhaja ta kalato cewa, an ga fasinjoji na shiga jirgin a tashar Idu cikin tsattsauran tsro a safiyar Litinin. Sai dai ba a samu tururuwar fasinja ba kamar yadda aka saba gani a baya a lokacin da jirgin ke loadin safe a tashar ta Idu. Manhaja ta gano an ɗauki matakan tsaro da dama, ciki har da kafa kyamarorin CCTV a sassa daban-daban domin sanya…
Read More
‘Yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 sun isa Beijing lafiya

‘Yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 sun isa Beijing lafiya

Daga CMG HAUSA Rahotannin da ofishin kula da aikin nazarin sararin samaniya, da kumbo mai dauke da mutane na kasar Sin ya fitar sun nuna cewa, ‘yan sama jannatin da suka kammala aiki cikin kumbo mai dauke da mutane samfurin Shenzhou-14, wato Chen Dong, da Liu Yang, da Cai Xuzhe, sun sauka birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin a asubar yau Litinin 5 ga wata lami lafiya, inda shugabanni da wakilai, na babbar hedkwatar kula da aikin gina tashar nazarin sararin samaniya ta kasar Sin suka tarye su, a filin saukar jiragen sama. Yanzu haka za a fara gwajin lafiyar…
Read More
Sahihanci shi ne tushen haɗin gwiwar Afirka da Sin

Sahihanci shi ne tushen haɗin gwiwar Afirka da Sin

Daga CMG HAUSA Abokaina, ko kuna son cin Avacado? Kun san a nan kasar Sin ba a noma wannan nau’in ‘ya’yan marmari, saboda haka kusan ba wanda ya san shi kafin shekaru fiye da 10 da suka wuce. Na tuna lokacin da na sayi Avacado a karon farko, ban san ya kamata a bari ya yi laushi ba kafin a ci shi. Sai na ci shi nan take bayan da na same shi, yayin da yake da tauri. Don haka ra’ayin da na samu game da Avacado a lokacin shi ne, wani nau’in ‘ya’yan marmari ne mai tsada, kuma maras…
Read More
An ƙaddamar da ginin sabuwar hedikwatar ECOWAS

An ƙaddamar da ginin sabuwar hedikwatar ECOWAS

Daga CMG HAUSA A jiya Lahadi ne aka aza tubalin ginin sabuwar hedikwatar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yankin Afirka ta yamma ko ECOWAS, a birnin Abuja fadar mulkin Najeriya, aikin da kasar Sin za ta tallafa wajen gudanar da shi. Ana sa ran ginin zai baiwa kungiyar damar tattare ayyukanta wuri guda, sabanin yadda a yanzu kungiyar ke da ofisoshi 3 a birnin Abuja. Shugabannin kasashen yammacin Afirka, ciki har da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, da takwarorinsa na Guinea Bissau da Saliyo, da kuma shugaban hukumar gudanarwar ECOWAS Omar Alieu Touray, da jakadan Sin a Najeriya Cui Jianchun,…
Read More
Ɓatagari sun sake ƙona ofishin INEC a Imo

Ɓatagari sun sake ƙona ofishin INEC a Imo

*Sau bakwai ana kai wa ofishin INEC hari a cikin wata huɗi - Kwamishina Daga WAKILINMU Ɓatagari sun sake ƙona wani ofishin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ke yankin Ƙaramar Hukumar Oru ta Yamma a Jihar Imo. Bayanin faruwar hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da hukumar ta fitar ranar Lahadi ta hannun kwamishinanta, Festus Okoye. A cewar Okoye, Kwamishinan INEC na Jihar Imo, Farfesa Sylvia Uchenna Agu, ya kai rahoton harin da aka kai ofishin da misalin ƙarfe 4.00 asuba ran Lahadi. Ya ce, ɓarnar da ta auku sakamakon harin ta taƙaita ne a zauren…
Read More
‘Yan bindiga sun harbi liman, sun sace mutum da dama a masallacin Katsina

‘Yan bindiga sun harbi liman, sun sace mutum da dama a masallacin Katsina

Daga WAKILINMU Rundunar 'Yan Sanda ta Jihar Katsina ta ce, ta ceto wasu mutum shida waɗanda 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su ranar Asabar a yankin Karamar Hukumar Funtua a jihar. Ta ce waɗanda aka ceton suna daga cikin mutum 19 da aka yi garkuwa da su a lokacin da suke tsaka da sallar Issha a Masallcin ƙauyen Maigamji. Bayanan da Manhaja ta samu sun ce, kafin yin awon gaba da waɗanda suka kwashe sai da ɓarayin suka ji wa limamin masallacin da wani mutum guda rauni da harbin bindiga. Binciken Manhaja ya gano an sako biyu daga cikin…
Read More
Ana gallaza wa ɗalibai Musulmai a jami’o’i mallakin Kiristoci a Nijeriya – MURIC

Ana gallaza wa ɗalibai Musulmai a jami’o’i mallakin Kiristoci a Nijeriya – MURIC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Kare Muradun Musulmai a Nijeriya (MURIC) ta yi zargin ana gallaza wa ɗalibai Musulman da ke karatu a jami’o’i musu zaman kansu mallakin Kiristoci a ƙasar nan. Ƙungiyar ta faɗi hakan ne a cikin wata sanarwa wacce Shugabanta, Farfesa Ishaq Akintola ya sa wa hannu, ta kuma fitar a ranar Alhamis. A cikin sanarwar, MURIC ta zargi jami’o’in da nuna gaba da tsana da kuma tsangwama ga Musulmi da kuma adddinin Musulunci ta hanyar yadda ake tirsasa ɗalibai Musulmai zuwa Coci da kuma hana su sa hijabi da sauransu. “Mun samu rahotanni da yawa kan…
Read More
Ƙungiyar Sakkwatawa, Kabawa da Zamfarawa na ƙara bunƙasa a Legas – Shugaban ƙungiyar

Ƙungiyar Sakkwatawa, Kabawa da Zamfarawa na ƙara bunƙasa a Legas – Shugaban ƙungiyar

Daga DAUDA USMAN a Legas Shugaban Ƙungiyar Al'ummar Sakkwatawa Kabawa da Zamfarawa mazauna Legas na shiyyar ƙaramar hukumar Ojoromi Ajegunle da ke cikin garin Legas, Alhaji Adamu Abubakar Ajegunle ya bayyana cewa, ƙungiyarsa ta ’yan asalin Sakkwato, kebbi da Zamfara mazauna legas na ƙara bunƙasa. A halin yanzu wannan ƙungiyar ta su tana ƙara samun nasarori a wajen gudanar da ayyukanta tare da bunƙasa harkokin ƙungiyar a Legas da kewayanta gaba ɗaya. Shugaban ƙungiyar na shiyyar ƙaramar hukumar Ojoromi a Legas, Alhaji Adamu Abubakar ya faɗi haka ne a lokacin da ya ke yin tsokaci bisa ga nasarori da ƙungiyar…
Read More
Miyetti Allah za ta iya kawo ƙarshen hare-haren ’yan bindiga – Sarkin Musulmi

Miyetti Allah za ta iya kawo ƙarshen hare-haren ’yan bindiga – Sarkin Musulmi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah (MACBAN), na iya ba da gudunmawa wajen magance matsalar hare-haren ’yan bindiga a ƙasar nan. Sarkin Musulmi, ya ce shugabancin MACBAN na iya taimaka wa wajen kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga da ke garkuwa da mutane a Nijeriya. Ya bayyana haka ne a lokacin rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar MACBAN a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja. A cewar sarkin, “kowa ya san Fulani suna tashi daga wani waje zuwa wani. Suna zuwa ko’ina suna yin aure. Kuma mu masu son zaman…
Read More
Babban burina shine Tijjaniyya ta kafa jami’arta – Shehi Tijjani Auwalu

Babban burina shine Tijjaniyya ta kafa jami’arta – Shehi Tijjani Auwalu

Daga BILKISU YUSUF ALI Shehi Tijjani Sani Auwalu malamin masanin Islama ne kuma tsayayye, wanda ya kasance komai ya saka a gaba sai ya ga tabbatuwarsa. A ranar 24 ga Nuwamba, 2022, Majalisar Shura ta Ɗariƙar Tijjaniya ta tabbatar da naɗinsa a matsayin Shugaban cibiyar Majma’u Ahbabu Shehi Ibrahim Inyas na Ƙasa. Wakiliyar Blueprint Manhaja, BILKISU YUSUF ALI, ta samu tattaunawa da shi. Ga yadda hirar ta kasance: MAHAJA: Mene ne taƙaitaccen tarihinka? AUWALU: Sunana Tijjani ɗa ga Maulanmu Shehu Tijjani Sani Auwalu kuma ɗa ga Sayyada Aisha ‘yar Sheikh Ibrahim Niass. An haife ni a Kano a shekarar 1973.…
Read More