07
Dec
*Ya fitar da sabbin dokokin hada-hadar kuɗi Daga WAKILINMU Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya taƙaita yawan kuɗin da mutum zai iya cirewa a na’urar POS a rana ɗaya zuwa N20,000, a banki kuma ba za su wuce N100,000 ba a mako guda. Hakan na ɗaya daga cikin irin matakan da babban bankin ya ce zai fito da su domin taƙaita yawon tsabar kuɗi a hannun mutane. Ana sa ran wannan tsari ya soma aiki ya zuwa ranar tara ga watan Janairu, 2023. Wannan na zuwa ne a lokacin da CBN ke shirye-shirye sakin sabbin takardun Naira da aka sake wa…
