‘Yan bindiga sun buƙaci a biya fansa da sabbin Naira bayan sace mutum 46 a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

‘Yan ta’adda kimanin 40 a kan babura ɗauke da muggan makamai sun yi awon gaba da mutane 46 a wasu sabbin hare-haren da suka kai ƙarshen makon da ya gabata a ƙananan hukumomin Funtua da Batsari na Jihar Katsina.

Maharan sun yi garkuwa da mutane 31 ciki har da mata da ƙananan yara dake kan hanyarsu ta zuwa makarantar sakandaren je-ka-ka-dawo dake ƙauyen Ƙarare a Ƙaramar Hukumar Batsari.

Daga cikin mutanen da suka sace har da wasu ɗalibai in ji wani ganau.

Ya ce maharan sun kashe mutum ɗaya a yayin da suka shiga garin suna harbi kan mai uwa dawabi.

Rahotanni sun nuna daga cikin yaran da aka yi garkuwa da su har da ɗalibai daga ƙauyen Ƙoƙiya waɗanda ke hanyarsu ta zuwa makaranta a ƙauyen.

Majiyarmu ta kuma ce daga baya maharan sun sako mutane huɗu daga ciki.

Sun kuma turo da saƙo cewa ba za su karɓi tsofaffin takardun kuɗi ba a matsayin kuɗin fansa.

“Daga baya mutum ɗaya ya tsere daga hannunsu, saboda haka yanzu mutum 23 na hannunsu, amma masu garkuwar ba su nemi kuɗin fansa ba tukuna,” inji shi.

Shugaban Ƙaramar Hukumar ta Batsari ya tabbatar da faruwar lamarin sai, dai ya musanta cewar akwai ‘yan makaranta cikin waɗanda maharan suka sace.

Idan za a iya tunawa, Manhaja ta kawo labarin yadda wasu ‘yan ta’adda suka kutsa kai cikin wani masallaci a ƙauyen Maigamji dake tsakanin Ƙaramar Hukumar Ɗandume zuwa Funtua inda suka harbi limamin, wato Imam Usha’u lokacin da yake jan sallar Isha’i.

Tsohon Kansilan gundumar Dangamji, Lawal Maigamji, ya bayyana wa manema labarai cewar maharan sun harbi limamin da ke jan sallar da wani mutum ɗaya, sannan suka sace mutum 18 daga masallacin a yayin harin.

Lawal ya ce, a halin yanzu mutanen biyu suna samun kulawa a Babbar Asibitin Funtua, sannan an yi sa’a mutum huɗu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su a masallacin sun tsere kafin ’yan bindigar su isa da su daji.

Da yake magana dangane da harin Ƙarare, kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, Sp Gambo Isa ya bayyana cewar sun samu rahoton harin sai dai yawan adadin mutanen da aka sace ya bambanta don haka suna gudanar da bincike don tantance haƙiƙanin yawan adadin mutanen da lamarin ya shafa

“Saboda haka muna gudanar da bincike domin tantance gaskiyar sannan an riga an fara aiki domin kuɓutar da mutanen waɗanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da su,” inji shi.

A ƙarshe, kakakin rundunar ya bayyana cewar jami’an ‘yan sanda na aiki tare da ‘yan banga don kuɓutar da sauran mutanen da aka yi garkuwar da su.