Editor

9513 Posts
Buhari ya kori manajan NIRSAL saboda zargin sa da almundahana

Buhari ya kori manajan NIRSAL saboda zargin sa da almundahana

Daga AMINA YUSUF ALI Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya sauke Manajan Daraktan Hukumar ba da Agajin Ibtila'i da Tallafin Noma (NIRSAL), Aliyu Abdulhameed, a kan zargin yin almundahana. Rahotanni sun bayyana cewa, Shugaban qasar ya kori Abdulhameed daga aiki a yammacin ranar Alhamis 2, ga watan Disamba 2022, inda aka fatattake shi daga ofishin nasa jim kaɗan bayan nan. Abdulhameed dai ana zarginsa da laifin karkatar da wasu kuɗaɗen hukumar tun daga lokacin da aka naɗa shi muƙamin a shekarar 2015 zuwa yau. Haka zalika, rahotanni sun sake bayyana cewa, a halin yanzu tuni gwamnatin ta baza komar neman madadinsa.…
Read More
Ɗalibi Aminu ya kawo ƙarshen faɗansa da Aisha Buhari bayan ganawarsa da Shugaban Ƙasa

Ɗalibi Aminu ya kawo ƙarshen faɗansa da Aisha Buhari bayan ganawarsa da Shugaban Ƙasa

Daga BASHIR ISAH Yanzu dai ya tabbata fadan da ke tsakanin matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, da ɗalibin nan Aminu Mohammed Adamu, ya ƙare. Hakan ya biyo bayan ganawar da Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi da Aminu ɗin ne bayan da aka sako shi daga gidan maza. Aminu, wanda ɗalibi ne a Jami'ar Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa, ya gamu da fushin Aisha ne bayan da ya caccake ta a shafinsa na Tiwita inda ya ce ta ci kuɗin talakawa ta yi ɓul-ɓul. Lamarin da ya sanya jami'an tsaro na DSS suka bi sawun ɗalibin har makarantarsu suka…
Read More
An tallafa wa wanda lakarsa ta tsinke da miliyan N1 a Jigawa

An tallafa wa wanda lakarsa ta tsinke da miliyan N1 a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Ƙaramar Hukumar Buji a Jihar Jigawa, ta ba da tallafin Naira miliyan ɗaya ga wani matashi da ya samu matsala a lakarsa sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi kwanan baya. Tallafin ɓangare ne na ƙoƙarin da ƙaramar hukumar ke yi wajen ganin ta inganta rayuwar nakasassu da marasa lafiya a yankin. Matashin, Ahmad Karanjau, ya haɗu da tsautsayin ne a kan hanyar Abuja zuwa Benin. Shugaban Ƙaramar Hukumar, Alhaji Abdullahi Sulaiman Yayari, ya tabbatar da cewa Hukumar Buji za ta ci gaba da tallafa wa Ahmad wanda a halin yanzu yake kwance…
Read More
‘Yan bindiga sun buɗe wuta cikin wani masallaci a Katsina

‘Yan bindiga sun buɗe wuta cikin wani masallaci a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina 'Yan bindiga sun yi dirar mikiya a wani masallaci dake garin Maigamji a Ƙaramar Hukumar Funtua a dai-dai lokacin da ake gabatar da Sallar Issha'i. Wani mazaunin garin ya shaida wa majiyar Manhaja cewa, da zuwan ɓarayin ana tsaka da Sallah sai suka buɗe wuta inda nan take suka harbi mutane biyu ciki har da wanda rahotanni suka ce shi ne limamin dake jan Sallar. Wanda yanzu haka suna karɓar magani a babban asibitin garin funtua. Rahotannin dai sun bayyana cewar, maharan sun yi awon gaba da mutane da dama. Harin na zuwa ne bayan…
Read More
Turai ta san ra’ayin Amurka kan dangantakar dake tsakaninsu

Turai ta san ra’ayin Amurka kan dangantakar dake tsakaninsu

Daga CMG HAUSA A kwanakin baya ne, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya gama ziyararsa ta kwanaki 3 a kasar Amurka. Shugaba Macron ya ziyarci Amurka a wannan karo don sa kaimi ga kasar Amurka da ta gyara dokar rage hauhawar farashin kaya bisa la’akari da kamfanonin Turai. Amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba, inda ya koma Turai ta bacin rai, duk da dangantakar dake tsakanin Turai da Amurkar. Shugaba Macron ya ziyarci Amurka a wannan karo don neman dawo da moriyar Turai. A watan Agusta na bana, shugaban kasar Amurka Joseph Biden, ya sa hannu kan dokar rage…
Read More
Kwalejin Confucius ta yi bikin cika shekaru 10 da fara aiki a Saliyo

Kwalejin Confucius ta yi bikin cika shekaru 10 da fara aiki a Saliyo

Daga CMG HAUSA Jiya ne, kwalejin Confucius dake jami'ar kasar Saliyo, ya yi bikin cika shekaru 10 da fara aiki a kasar. Darektar kwalejin Confucius na jami'ar Saliyo Jing Man, ta bayyana cewa, tun daga shekarar 2012 zuwa yanzu, kwalejin ya kafa sassan koyarwa guda 20, yayin da adadin daliban da suka yi rajista ya karu cikin sauri. Ta kara da cewa, tasirin kwalejin Confucius da ke kasar Saliyo ya karu, kuma a yanzu haka, kwalejin na taka muhimmiyar rawa wajen inganta harshen Sinanci da al'adun kasar Sin a kasar. Jing ta ce, kwalejin zai ci gaba da baiwa dalibai…
Read More
Kumbon Shenzhou-14 ya sauka cikin nasara

Kumbon Shenzhou-14 ya sauka cikin nasara

Daga CMG HAUSA Kumbon Shenzhou-14 na kasar Sin ya sauka cikin nasara a filin saukar kumbuna na Dongfeng. Jami'an sanya ido na likitoci sun tabbatar da cewa, 'yan sama jannatin Chen Dong, Liu Yang, da Cai Xuzhe suna cikin koshin lafiya, kuma aikin na Shenzhou 14 ya samu cikakkiyar nasara. Hukumar kula da harkokin binciken sararin samaniya ta kasar Sin (CMSA) ta bayyana cewa, da misalin karfe 11 da minti 1 na safiyar yau ne, kumbon Shenzhou-14 na kasar Sin, ya rabu da tashar sararin samaniyar kasar. 'Yan sama jannati uku, wato Chen Dong, Liu Yang da Cai Xuzhe, sun…
Read More
Hajjin 2023: Saudiyya za ta gana da NAHCON ta kafar ‘Zoom’

Hajjin 2023: Saudiyya za ta gana da NAHCON ta kafar ‘Zoom’

Daga BASHIR ISAH A matsayin wani mataki na shirye-shiryen Hajjin 2023, Ma'aikatar Hajji da Umarah ta Saudiyya ta sanar da Hukumar Hajji ta Nijeriya (NAHCON) cewa, za su yi tattaunawa ta musamman ta kafar 'Zoom' ya zuwa ranar 21 ga Disamban 2022. Sanarwar na ƙunshe ne cikin wasiƙar da Saudiyya ta aike wa NAHCON ɗin ta hannun Ma'aikatar Harkokin Waje. Sanarwar ta ce, tattaunawar wani tsani ne na ƙoƙarin cimma rattaba hannu a Yarjejeniyar Fahimtar Juna tsakanin ƙasashen biyu dangane da abin da ya shafi Hajjin 2023. A cewar sanarwar, tattaunawar za ta gudana ne da misalin ƙarfe 10:30 na…
Read More
Bashir Baba: Mutuwa rigar kowa

Bashir Baba: Mutuwa rigar kowa

Daga ADAMU NASIRU EL-HIKAYA Ban gama ajiye alƙalamin ta’aziyyar rasuwar ɗan jarida Muhammad Isa ba da ya zo bayan rasuwar Danladi Ndayebo, sai ga labarin rasuwar Malam Bashir Baba. Duk waɗannan mutanen ’yan jarida ne da su ka yi aiki tuƙuru kuma ba lalle sun tara abun duniya ba. Mutuwa babban darasi ne kuma tunatarwa cewa duk mai numfashi a cikin talikkai to lalle kuwa wataran sai ya ɗanɗani ɗacin mutuwa. Iyaye ne ko kakanni, dattawa ne ko matasa, maza ne ko mata duk kowa lokaci ya ke jira in kuma lokacin ya yi ba makawa sai tafiya. Na ma…
Read More
An cafke matar da ta jefa jaririnta cikin masai a Jigawa

An cafke matar da ta jefa jaririnta cikin masai a Jigawa

Daga ABUBAKAR M TAHEER Rundunar 'Yan Sanda ta Jihar Jigawa ta sanar da kama wata mata mai suna Balaraba Shehu bayan Jefa jaririn da ta haifa a masai da niyyar binne shi. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Tsurma da ke Ƙaramar Hukumar Kiyawa, Jihar Jigawa, inda aka gano jaririn aka garzaya da shi Asibitin Dutse inda a nan aka tabbatar da mutuwarsa. Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Shiisu Lawan Adam, shi ne ya sanar da hakan ga manema labarai. Ya ce, "Mun samu labarin jefar da jariri a masai inda jami'anmu suka garzaya domin bincike da kuma kama matar.…
Read More