Kumbon Shenzhou-14 ya sauka cikin nasara

Daga CMG HAUSA

Kumbon Shenzhou-14 na kasar Sin ya sauka cikin nasara a filin saukar kumbuna na Dongfeng.

Jami’an sanya ido na likitoci sun tabbatar da cewa, ‘yan sama jannatin Chen Dong, Liu Yang, da Cai Xuzhe suna cikin koshin lafiya, kuma aikin na Shenzhou 14 ya samu cikakkiyar nasara.

Hukumar kula da harkokin binciken sararin samaniya ta kasar Sin (CMSA) ta bayyana cewa, da misalin karfe 11 da minti 1 na safiyar yau ne, kumbon Shenzhou-14 na kasar Sin, ya rabu da tashar sararin samaniyar kasar.

‘Yan sama jannati uku, wato Chen Dong, Liu Yang da Cai Xuzhe, sun shafe tsawon kwanaki 183, suna rayuwa da kuma aiki a tashar sararin samaniyar.

A cewar hukumar CMSA, gabanin rabuwar kumbon da tashar, ‘yan sama jannatin sun kammala ayyuka daban-daban, kamar mika ayyuka ga ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-15 a sararin samaniya, da tsara matsayin tashar sararin samaniyar, da rabawa da sauke bayanan gwaji, da sharewa da tura kayayyakin da aka ajiye a sararin samaniya, tare da tallafi daga ma’aikatan kimiyya da fasaha dake kasa.

A ranar 5 ga watan Yuni ne, aka aika da ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 guda 3 zuwa tashar sararin samaniyar, sun kuma yi nasarar kammala ayyuka da dama a cikin ‘yan watannin da suka gabata, ciki har da sa ido kan hadewar sassan tashar sararin samaniyar sau guda 5, da gudanar da ayyuka sau guda 3 a wajen tashar, da gabatar da darasin na kimiyya kai tsaye guda 1 daga tashar zuwa doron duniya, da kuma wasu gwaje-gwajen kimiyya.