Editor

9513 Posts
Ƙungiyoyi sun yi ƙorafin an yi wa ƙananan yara 84,000 rijistar zaɓe a Filato

Ƙungiyoyi sun yi ƙorafin an yi wa ƙananan yara 84,000 rijistar zaɓe a Filato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gamayyar ƙungiyoyin farar hula CSOs, guda goma da ke aiki domin tabbatar da sahihin zaɓe a Nijeriya, sun buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta, INEC, da ta gaggauta yin bincike kan rijistar masu zaɓe a Jihar Filato. Ƙungiyar, a wata sanarwa da ta fitar a Abuja ranar Laraba, ta ce ta gano sama da ƙananan yara dubu 84 da suka yi wa rijistar zabe a ƙananan hukumomi 17 da ke jihar. Vanguard ta rawaito cewa ƙungiyoyin lura cewa, INEC, bisa la'akari da sashe na 19 (1) na dokar zaɓe, 2022, ta wallafa rajistar masu…
Read More
Tsohon Shugaban Jami’ar Gusau, Farfesa Garba zai sha ɗaurin shekara 35

Tsohon Shugaban Jami’ar Gusau, Farfesa Garba zai sha ɗaurin shekara 35

Daga SUNUSI MUHAMMAD a Gusau Wata Babbar Kotun Tarayya dake zama a Abuja ta yanke wa tsohon Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Gusau, Farfesa Magaji Garba, hukuncin ɗauri na tsawon shekara 35. Mai shari’a Maryam Hassan Aliyu, wadda ta yanke hukuncin ta ce an samu Farfesa Garba ne da laifuka biyar da suka jiɓanci amfani da ƙarya wajen karɓar kuɗi da kuma zamba. Hukumar EFCC ce ta gurfanar da tsohon shugaban jami’ar gaban kotu ranar 12 ga watan Oktoba tana zargin sa da tatsar kuɗi daga wani mutum bisa alƙawarin ba shi kwangilar katange jami’ar, wadda kuɗinta ya kai Naira…
Read More
Matsalar ƙarancin abinci da ke kunno kai

Matsalar ƙarancin abinci da ke kunno kai

A bayyane ya ke cewa illar da ambaliyar ruwa ta 2022 da ta addabi sassa daban-daban na Nijeriya ta fifa ƙasar cikin wani irin hali. Don haka, ba abin mamaki ba ne cewa Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya faɗakar da ’yan Nijeriya da su tashi tsaye don havaka farashin abinci da haɗari a 2023 saboda wannan ambaliya da tsadar taki. Cibiyar hada-hadar kuɗi ta duniya ta ce ƙara samun sauyin yanayi a cikin daidaiton farashin kasuwa da kuma cigaba da dogaro da kuɗaɗe da babban bankin ƙasar ke bai wa giɓin kasafin kuɗi na iya ƙara taɓarɓarewar…
Read More
Jirgin Abuja-Kaduna: Za a hana yin waya a jirgin ƙasa

Jirgin Abuja-Kaduna: Za a hana yin waya a jirgin ƙasa

*An soke zirga-zirgar dare*Akwai tsare-tsare na sarari da ɓoye – Ministan Sufuri*Za a ƙara kuɗin tikiti da albashin ma’aikata, inji Ministan Sufuri*Ni da iyalina za mu riƙa hawa jirgin saboda tabbacin tsaronsa, inji Ministan Ruwa*Mu na aiki kan samar sababbin manufofi – Shugaban Hukumar Daraktoci Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa, akwai yiwuwar ta hana amfani da waya a cikin jiragen ƙasan Abuja zuwa Kaduna, wanda aka dakatar da zirga-zirgarsu tun bayan harin da aka kai wa jirgin fasinjojin a cikin watan Maris da ya gabata. Shugaban Hukumar Daraktoci na Kamfanin Sufurin Jiragen Ƙasa…
Read More
2023: Ba za a sake barin gwamnoni hana ’yan adawa taro ba – Sufeto Janar

2023: Ba za a sake barin gwamnoni hana ’yan adawa taro ba – Sufeto Janar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Usman Baba Alƙali, ya bayyana cewa, babu wani gwamna da za a sake bari ya hana jam’iyyun siyasa na adawa gudanar da taro a jihohinsu. IGP Baba ya yi wannan maganar ne ranar Laraba a taron jam’iyyun siyasa na 2022 a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya. Sufeto Janar ɗin, wanda ya samu wakilcin Dandaura Mustapha, Mataimakin Sufeto Janar na Hukumar ’Yan Sanda (DIG), ya ce, an umarci kwamishinonin jihohi da su tabbatar an bai wa kowane ɓangare damar gudanar da yaƙin neman zaɓe. Baba ya ƙara da cewa, yayin da…
Read More
Ma’aunin talauci na Nijeriya

Ma’aunin talauci na Nijeriya

Assalam alaikum. Ina yi wa jaridar Blueprint Manhaja fatan alheri. Wani sabon rahoto ya tabbatar da cewa aƙalla ’yan Nijeriya miliyan 133 ne ke fama da talauci. Wannan na ƙunshe ne a cikin sabuwar ƙididdigar Talauci ta Nijeriya da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar kwanan nan a Abuja. Sabuwar alƙalumman talauci na wakiltar kusan kashi 63 cikin 100 na al'ummar ƙasar. An gudanar da binciken tsakanin Nuwamba 2021 da Fabrairu 2022. Ambaliyar ruwa ta baya-bayan nan a faɗin ƙasar, wacce ta lalata gidaje da rayuwa da kuma nitsewar filayen noma a jihohi da dama na tarayyar ƙasar, mai…
Read More
Ƙalubalen yaran da ba sa zuwa makaranta

Ƙalubalen yaran da ba sa zuwa makaranta

Dangane da ƙaruwar yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya, wanda a halin yanzu aka ƙiyasta su miliyan 20, Tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana lamarin a matsayin wani abu mai matuƙar tayar da hankali. A cewarsa, samun irin wannan adadi mai yawa na yara ba tare da tsarin ilimi ba, zai haifar da tarnaƙi ga ƙaruwar masu tada ƙayar baya da ’yan ta’adda a nan gaba. Tsohon shugaban, wanda ya yi magana a wani taron ƙoli na ilimi na manyan makarantu na ƙasa da Majalisar Wakilai ta shirya, a wani ɓangare na ƙoƙarin magance ƙalubalen…
Read More
Shugabannin ƙasashen Afirka da na ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa sun nuna alhinin rasuwar Jiang Zemin

Shugabannin ƙasashen Afirka da na ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa sun nuna alhinin rasuwar Jiang Zemin

Daga CMG HAUSA Shugabannin kasashen Afirka, da manyan jami’an kungiyoyin kasa da kasa, sun ci gaba da gabatar da sako zuwa ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, inda suke nuna matukar alhini ga rasuwar Jiang Zemin. A cikin sakon sa, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce, marigayin ya jagoranci kasar Sin wajen aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, da kama hanyar raya tattalin arziki yadda ya kamata, al’amarin da ya shaidawa duniya cewa, kasa za ta iya cimma burin raya tattalin arzikinta ta hanyar dogaro da kan ta. Buhari ya ce, nasarorin da…
Read More
An yi “bikin fina-finan ƙasar Sin” a hedikwatar UNESCO

An yi “bikin fina-finan ƙasar Sin” a hedikwatar UNESCO

Daga CMG HAUSA Yau Asabar, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, da tawagar kasar dake hukumar UNESCO, wato hukumar kyautata ilimi da kimiyya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya, sun gudanar da “bikin nuna fina-finan kasar Sin” a hedikwatar hukumar, inda aka gabatar da ra’ayin kafa al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, da yadda kasar Sin take kokarin zamanantar da kanta. Wannan shi ne karo na farko da aka nuna fina-finai sama da 50 a “bikin nuna fina-finan kasar Sin” a wata kungiyar kasa da kasa. Shugaban CMG, Mista Shen Haixiong ya gabatar da jawabin…
Read More
An gudanar da dandalin matasan Sin da Afirka kan ayyukan sa kai

An gudanar da dandalin matasan Sin da Afirka kan ayyukan sa kai

Daga CMG HAUSA A ranar Juma’a ne an gudanar da dandalin matasan Sin da Afirka kan ayyukan sa kai, wanda aka yiwa take da “Hadewa, da karfafa gwiwar matasa masu ayyukan sa kai, domin gina ci gaban hadin gwiwar Sin da Afirka." Masu gabatar da makala sun yi musayar ra’ayi, game da ci gaban Sin, da hadin gwiwar kasa da kasa a fannin ayyukan sa kai da matasa ke gudanarwa, da manufofin nahiyar Afirka masu nasaba da bunkasa ci gaban matasa, da ma kwarewar nahiyar a fannin ayyukan sa kai na matasa. A cewar mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar matasan kasar…
Read More