Editor

9513 Posts
Gwamnoni sun ƙalubalanci Buhari ya bayyana sunayen gwamnonin da ke wawushe kuɗaɗen ƙananan hukumomi

Gwamnoni sun ƙalubalanci Buhari ya bayyana sunayen gwamnonin da ke wawushe kuɗaɗen ƙananan hukumomi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu gwamnonin sun ƙalubalanci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya bayyana sunayen gwamnonin jihohin da ya zarga da satar kuɗaɗen da ake bai wa ƙananan hukumomin jihohinsu duk wata. Idan za a iya tunawa cewa, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya zargi wasu gwamnoni da wawushe kuɗaɗen da ke tura wa ƙananan hukumomi daga Gwamnatin Tarayya. Ya koka da yadda gwamnonin ke yi wa matakin ƙananan hukumomi rashin adalci. Shugaban ya yi tsokaci ne kan ‘ayyukan damfara’ da wasu gwamnoni suka yi wajen rabon kuɗaɗen da aka ware domin gudanar da ƙananan hukumomi. Ya ce, ba za…
Read More
Naƙasa ba kasawa ba ce: Tsarabar Ranar Naƙasassu ta Duniya

Naƙasa ba kasawa ba ce: Tsarabar Ranar Naƙasassu ta Duniya

Daga MUJAHEED ABULLAHI KUDAN Tun daga shekarar 1992, Majlisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar 3 ga watan Disamba ta kowace shekara a matsayin Ranar Naƙasassu ta Duniya. An ware ranar ne bisa manufar fahimtar batutuwan da suke ɗamfare da naƙasa da kuma tallafa wa matsayi da haƙƙoƙin naƙasassu. Bugu da ƙari, daga cikin manufofin ranar, akwai sake wayar da kan al’umma game da irin alfanun da ke akwai wajen damawa da naƙasassu cikin duk sha’anonin zamantakewa da siyasa da tattalin arziƙi da duk al’amuran rayuwar yau da kullum. A kowace shekara, irin wannan rana tana da taken da ake mayar…
Read More
Ɗalibi Aminu zai gana da Buhari bayan sako shi daga kurkuku

Ɗalibi Aminu zai gana da Buhari bayan sako shi daga kurkuku

Daga BASHIR ISAH An sako ɗalibin nan, Aminu Mohammed Adamu, wanda aka tsare tare da maka shi a kotu don ya soki matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari. Rahotannin da Manhaja ta samu sun nuna, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai gana da Aminu kafin daga bisani a miƙa shi ga ‘yan uwansa. Idan dai ba a manta ba, kimanin makonni biyu da suka gabata jami’an tsaro suka damƙe ɗalibin inda suka ɗauke shi zuwa Abuja sakamakon sukar da ya yi wa Aisha Buhari a shafinsa na Tiwita, inda ya ce Aisha ta ci kuɗin talakawa ta yi ɓul-ɓul. A ranar Talatar…
Read More
INEC za ta fara raba Katin Zaɓe 12 ga Disamba

INEC za ta fara raba Katin Zaɓe 12 ga Disamba

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta ce, ta rarrabe tsarin karɓar Katin Zaɓe (PVC) zuwa matakin gundumomi daga ranar 6 ga Janairun 2023. Kazalika, hukumar ta ce daga ranar 12 ga Disamba, 2022 za ta soma raba wa waɗanda suka yi rajista Katin Zaɓe a dukkan ƙananan hukomimi 774 da ake da su a faɗin ƙasa. INEC ta bayyana hakan ne cikin sanarwar da ta fitar Juma’ar da ta gabata, inda ta ce an cimma matsayar haka ne a wajen taron da ta gudanar kwanan nan a Legas. Sanarwar wadda ta sami sa hannun…
Read More
Suturar mutum uku Aisha ke sakawa saboda ƙiba – Solomon Dalung

Suturar mutum uku Aisha ke sakawa saboda ƙiba – Solomon Dalung

Daga BASHIR ISAH Tsohon Ministan Matasa da Wasannin Motsa Jiki, Solomon Dalung, ya ce a halin yanzu, suturar da za ta wadaci mutum uku matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari ke sakawa saboda ƙiba. Dalung wanda ya riƙe muƙamin Minista a wa'adin farko na Shugaba Buhari, ya faɗi hakan ne a sa'ilin da yake tsokaci dangane da tsare ɗalibi Aminu Mohammed da aka yi don ya soki Aisha Buhari a kafar Tiwita. Ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da aka yaɗa wanda jaridar Daily Nigeria ta samu gani. A cewar Ministan, babu abin da ɗalibin da aka kama ɗin ya…
Read More
Kwaleji ta haramta wa masu juna-biyu da raino shiga harabarta a Ibadan

Kwaleji ta haramta wa masu juna-biyu da raino shiga harabarta a Ibadan

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wata Kwalejin Kimiyya da ke Ibadan ta haramta wa ɗalibai mata masu juna biyu da masu shayarwa kawo jarirai zuwa ajujuwa da ɗakunan kwanan ɗalibai. An bayyana hukuncin na kwalejin ne a cikin ƙa'idar ɗabi'a da majalisar gudanarwa ta sa hannu. Makarantar ta ce, za a dakatar da ɗaliban da ke tare da juna a bainar jama'a a harabar jami'ar har tsawon zango ɗaya. Adewole Soladoye, mai magana da yawun kwalejin, ya tabbatar da tsauraran ƙa'idojin. “Makarantar ba gidan jinya ba ce. Shin daidai ne a kawo jarirai a cikin ajujuwan lacca? Lallai abin shagaltuwa ne.…
Read More
A bar ce-ce-ku-ce kan yawan shekarun Tinubu, mulki ba dambe ba ne – Masari

A bar ce-ce-ku-ce kan yawan shekarun Tinubu, mulki ba dambe ba ne – Masari

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana cewar gwamnonin Arewa suna goyon bayan ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Jam'iyyar APC ba don ya ba su muƙamai ba idan ya yi nasarar lashe zave a shekara ta 2023. Masari ya faɗi haka ne a zantawarsa da DCL Hausa inda ya bayyana cewar gwamnonin na goyon bayan ɗan takarar jam'iyyar na su ne don ƙasar nan ta ci gaba. "Ai ba muƙami muke nema ba yadda ƙasar za ta ci gaba muke magana, gwamnan Kebbi yana takarar Sanata,wane muƙami kuma zai nema? Gwamnan Zamfara zai sake…
Read More
Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai fara aiki ran Litinin, cewar Gwamnati

Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai fara aiki ran Litinin, cewar Gwamnati

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta ba da sanarwar jirgin ƙasan Abuja–Kaduna zai dawo da aiki ya zuwa ranar Litinin, 5 ga Disamba. Shugaban Hukumar Kula da Jiragen Ƙasa ta Nijeriya (NRC), Fidet Okhiria ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) hakan ranar Alhamis. Ya ce, yanzu an kammala duk wani shiri da ya kamata don jirgin ya dawo ya ci gaba da aiki. Sai dai Okhiria, ya shawarci masu sha'awar su bi jirgin da su sabunta manhajar sayen tikitin jirgin da ke wayoyinsu daga ranar 3 ga Disamba don cimma nasara. Ya ƙara da cewa, za a…
Read More
Azal: Boka ya bindige wanda ya zo neman maganin bindiga

Azal: Boka ya bindige wanda ya zo neman maganin bindiga

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar ’Yan Sandan Jihar Enugu ta cafke wani boka da ya kashe wanda yazo wurinsa neman maganin harbin bindiga a lokacin da ya ke gwada maganin a kansa. Bokan ɗan asalin jihar yana ɗaya daga cikin mutane 17 da aka kama aka kuma gabatar da su bisa laifin haɗa baki, kisan kai, fashi da makami, kwace manyan motoci, garkuwa da mutane, da kuma mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba a ’yan kwanakin nan a jihar. An bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, 29 ga watan Nuwamba, 2022, ta hannun jami’in…
Read More
Hukumar EFCC za ta fara gwanjon motocin da ta ƙwace

Hukumar EFCC za ta fara gwanjon motocin da ta ƙwace

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Yaƙi da Masu yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC) ta sanar da yin gwanjon motoci sama da 800 da sauran kayayyakin da ta ƙwace a hannun waɗanda ake zargi a aikata laifi. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Juma’a 2 ga watan Disamba, 2022. A cewar sanarwar, hukumar ta ce, za a yi gwanjon ne a faɗin ofisoshin shiyya-shiyya da ke faɗin ƙasar nan. Ya ƙara da cewa, a duk ranar gwanjon, za a fara aikin ne daga ƙarfe 9 na safe zuwa 3 na…
Read More