02
Dec
Daga BASHIR ISAH Matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta janye ƙarar da ta shigar kan ɗalibin nan Mohammed Aminu bayan da ta sha caccaka da tofin Allah wadai daga ɓangarori daban-daban. Lauyan Aisha, Fidelis Ogbobe ya ce Aisha ta janye ƙarar ne bayan da wasu manyan ƙasa suka sa baki cikin batun. Ya ce ta janye ƙarar ne ta hanyar kafa hujja da Sashe na 108 da ƙaramin sashe na 2(a) na Dokar Manyar Laifuka. Da yake yanke hukuncin kan batun, Alƙalin Babbar Kotun, Mai Shari'a Yusuf Halilu, ya yaba wa Aisha Buhari dangane da haƙuri da afuwar da ta…
