Editor

9513 Posts
Sojojin Nijeriya sun kashe mayaƙan ISWAP da ke ƙera boma-bomai a tafkin Chadi

Sojojin Nijeriya sun kashe mayaƙan ISWAP da ke ƙera boma-bomai a tafkin Chadi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu hare-hare ta sama da jiragen yaƙin rundunar sojojin saman Nijeriya NAF suka kai, sun kashe ‘yan ta’adda 24 na ƙungiyar Da’esh ta yammacin Afirka ISWAP. Jaridar PRNigeria ta tattaro, ya faru ne a ranar Lahadi, a Tumbun Hamma, ɗaya daga cikin wuraren da aka gano sansanonin horar da ƙungiyar ISWAP a tafkin Chadi. ‘Yan ta’addan da aka kakkaɓe, kamar yadda wata majiyar leƙen asiri ta tsaro ta shaida wa PRNigeria, suna gudanar da aikin sarrafa makamai da IED, suna horo a wurin na tsawon kwanaki shida a jere. A wani labarin makamancin haka,…
Read More
Nijeriya ta gano mutum 100 masu taimaka wa Boko Haram

Nijeriya ta gano mutum 100 masu taimaka wa Boko Haram

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Kula da Al'amuran Cikin Gida na Nijeriya, Rauf Aregbesola ya ce gwamnatin Nijeriya ta gano mutum 100 masu taimaka wa ƙungiyar Boko Haram da kuɗaɗe da take tafiyar da ayyukanta. Ya kuma ce mutanen suna da alaƙa da aƙalla ƙasashe goma. Aregbesola wanda ya bayyana haka a ranar Lahadi ya ce yanzu haka gwamnati ta kama mutum 48 cikin 100, waɗanda ɓangaren tattara bayanan sirri na hada-hadar kuɗin ƙasar ya ambato. Kuma a cewarsa tuni aka fara tuhumar wasu daga cikin su. A cikin shekarun da suka gabata dai gwamnatin Nijeriya ta ce…
Read More
Shugabar matan jam’iyyar PDP ta sauya sheƙa zuwa APC a Yobe

Shugabar matan jam’iyyar PDP ta sauya sheƙa zuwa APC a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu Shugabar matan jam'iyyar PDP a jihar Yobe, Hajiya Hauwa Abore tare da magoya bayan ta sun sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC a Jihar Yobe. Da take bayar da dalilan da suka sanya ta sauya sheƙar, Hajiya Hauwa ta ce ita da mabiyanta sun yanke shawara shigowa jam'iyyar APC ne sakamakon ci gaban da Gwamnatin Jihar Yobe ta samar haɗi da aiwatar da ayyukan inganta rayuwar al'ummar jihar- a ƙarƙashin Gwamna Mai Mala Buni, su ne suka ja ra'ayin ta tare da ba ta ƙwarin gwiwar sauya sheƙa. Har wa yau, tsohuwar shugabar matan jam'iyyar…
Read More
Za a gudanar da taron tunawa fa Jiang Zemin a ranar Talata mai zuwa

Za a gudanar da taron tunawa fa Jiang Zemin a ranar Talata mai zuwa

Daga CMG HAUSA Kwamitin tsare-tsaren jana’izar Jiang Zemin, ya fitar da sanarwa da ke cewa, za a gudanar da taron tunawa da marigayin a ranar Talata 6 ga watan nan, a babban dakin taruwar jama’a dake birnin Beijing. Da yammacin Alhamis din nan ne kuma, jirgin sama na musamman ya dauko gawar Jiang Zemin daga birnin Shanghai zuwa Beijing. Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping, da wasu manyan jagororin JKS, da kusoshin gwamnati, suka isa filin jirgin sama domin tarbar gawar marigayin. Bisa wani labari daban da aka bayar, an ce, a jiya ne, mambobin kwamitin sulhun MDD suka…
Read More
Jirgin C919 na Ƙasar Sin ya samu amincewar ƙara ƙera shi

Jirgin C919 na Ƙasar Sin ya samu amincewar ƙara ƙera shi

Daga CMG HAUSA Babban jirgin saman fasinja samfurin C919 da kasar Sin ta kera da kanta, ya karbi takardar shaidar kara kera shi ranar Talata, matakin dake nufin ana iya kara kera jirgin saman da yawaKamfanin kera jiragen sama na kasar Sin (COMAC), wanda ya kera jirgin na C919, ya karbi takardar shaidar ce daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman kasar Sin (CAAC) dake yankin gabashin kasar. A shekarar 2017 ne dai, jirgin saman ya kammala gwajin tashinsa na farko cikin nasara, ya kuma samu irin wannan takardar shaida a karshen watan Satumba, abin da ke nuni da cewa,…
Read More
Xi Jinping ya yi shawarwari da shugaban Majalisar Zartaswar Turai

Xi Jinping ya yi shawarwari da shugaban Majalisar Zartaswar Turai

Daga CMG HAUSA A safiyar yau Alhamis ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da shugaban majalisar zartaswa ta Turai Charles Michel a babban dakin taruwar jama'a da ke birnin Beijing. Xi Jinping ya bayyana cewa, dangantakar da ke tsakanin Sin da Turai ta dade da ci gaba, wadda ta dace da muradun bangarorin biyu da na kasashen duniya. Game da ci gaban dangantakar, Xi ya gabatar da ra’ayoyi guda hudu, na farko shi ne tabbatar da sanin juna yadda ya kamata, na biyu shi ne warware sabane-sabane yadda ya kamata, na uku shi ne inganta hadin…
Read More
Kotu ta ba da umarnin tsare Babban Hafsan Sojoji, Faruk Yahaya

Kotu ta ba da umarnin tsare Babban Hafsan Sojoji, Faruk Yahaya

Daga WAKILINMU Wata Babbar Kotu mai zamanta a Minna, babban birnin Jihar Neja, ta ba umarni kamo Babban Hafsan Sojoji, Janaral Faruk Yahaya bisa zargin cin mutuncin kotun. Alkalin Kotun, Mai Shari'a Halima Abdulmalik ce ta ba da wannan umarni. Kazalika, umarnin kamun ya shafi har da Manjo Janar Stevenson Olugbenga Olabanji. Alkali Halima wadda ita ce alƙalin-alƙalan jihar, ta ce buƙatar kamo Yahaya ta taso ne sakamakon wata shari'a da ke gabanta. Kotun na buƙatar a kamo Yahaya da Olabanji a ajiye su a Gidan Gyaran Hali na Minna saboda rashin bin umarninta a ranar 12 ga Oktoban 2022.…
Read More
Tarin kura-kurai a littafin ‘Halayyar Zamani’

Tarin kura-kurai a littafin ‘Halayyar Zamani’

Daga SANI AHMAD GIWA Littafin 'Halayyar Zamani' ɗaya ne daga cikin jerin littafan Adabin Kasuwar Kano, mai ɗauke da shafuka 148, wanda suka haɗu suka ja zaren labarin. Fa'iza S. Muhammad ce ta ƙaga labarin, inda maɗaba'ar Megacraft wadda ba a bayyana adireshinta ba ita ta wallafa shi, farashin da ake fansar shi a kasuwar littafai Naira 300 ne kacal. Bayan fansar wannan littafin a kasuwa, abin da zai biyo baya kuwa ai sharhin bayan karatu ne, a yunƙurin ya Allah ko dai yabo ko suka mai ma’ana a kan yadda manazarci ya ga littafin, ya kuma kalle shi, ko…
Read More
Turawa na ɗaukar ado da kwalliya da muhimmanci – Khuraira Musa

Turawa na ɗaukar ado da kwalliya da muhimmanci – Khuraira Musa

"Ilimi da gaskiya za su iya kai mutum ga nasarar da ba ya zato" Daga ABUBAKAR M. TAHEER A yau shafin Mata A Yau ya yi wa mata tanadin firar da suka fi so, wato kwalliya da masu yin ta, inda muka samu tattaunawa da ƙwararriya a ɓangaren ado. Hajiya Khuraira Musa 'yar Nijeriya ce da ta ke sana'ar ado da kwalliya a Ƙasar Amurka. Bafulatana 'yar ƙaramar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, sai dai ta girma a ƙaramar Hukumar Bassa dake Jihar Fulatu. A cikin wannan tattaunawa da wakilin Manhaja ya yi da ita, ta kawo Irin ƙalubale…
Read More
Kotu ta tura ɗalibin da ake tuhuma da cin zarafin Aisha Buhari gidan yari

Kotu ta tura ɗalibin da ake tuhuma da cin zarafin Aisha Buhari gidan yari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babbar Kotun Birnin Tarayya Abuja mai lamba 14, ta tura wani ɗalibin Jami’ar Tarayya da ke Dutse a Jihar Jigawa, Aminu Mohammed zuwa gidan gyaran hali na Suleja da ke Jihar Neja bisa zargin rubutun cin zarafin Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari a shafinsa na Tuwita. An gurfanar da ɗalibin ne a Abuja a ranar Talata 29 ga watan Nuwamba, 2022 bisa laifin zamba ta yanar gizo inda aka hana belinsa duk da cewa ya ƙi amsa laifin da ake tuhumarsa da shi. Idan ba a manta ba, Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, jami’an tsaro ne…
Read More