Editor

9513 Posts
Gwamnatin Kano ta janye dokar hana bin wasu tituna ga matuƙa baburan adaidaita sahu

Gwamnatin Kano ta janye dokar hana bin wasu tituna ga matuƙa baburan adaidaita sahu

Daga Ibrahim Hamisu, Kano Gwamnatin jihar Kano ta janye dokar taƙaita bin hanyoyin ga matuka babura masu kafa uku da aka fi sani da Adaidaita sahu a wasu titunan Kano, Shugaban Hukumar Karota Baffa Babba Ɗan agundi ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gabatar a ofisoshin sa. Ya ce “mun janye dokar ne saboda biyayyar da 'yan adaidaita suka yi ga dokar da kuma yadda al’umma suka koka akan ta."
Read More
Ko da gaske ne ƙasar Sin barazana ce?

Ko da gaske ne ƙasar Sin barazana ce?

Daga LUBABATU LEI Kafar yada labaran kimiyya ta kasar Amurka da ake kira Protocol, ta wallafa wani rahoton da babbar ’yar jarida Kate Kaye ta bayar, bisa binciken da ta gudanar a kwanan baya, inda ta tona yadda Eric Schmidt, tsohon babban jami’in kamfanin Google, ya ci kazamar riba ta hanyar yayata ra’ayin nan na wai “kasar Sin na haifar da babbar barazana ga Amurka ta fannin fasaha.” An ce, a yayin da yake kan kujerar shugabancin kwamitin tsaron kasar Amurka ta fannin fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam, ya yi ta bayyana wa gwamnatin kasar damuwar yadda Amurka din ta…
Read More
Gwamnati ta amince a fara amfani da harshen Hausa wajen koyar da ‘yan firamare

Gwamnati ta amince a fara amfani da harshen Hausa wajen koyar da ‘yan firamare

Daga BASHIR ISAH Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ta amince da Dokar Harshe ta Ƙasa wadda ta ba da damar koyar da harshen uwa a makarantun firamare a faɗin ƙasa. Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya bayyana wa manema labarai hakan bayan kammala taron mako-makon da Majalisar ta saba shiryawa ranar Laraba a Abuja. Ya ce da samuwar wannan doka, hakan na nufin daga yanzu da harshen uwa za a riƙa koyar da 'yan firamare daga aji ɗaya zuwa shida. Ya ƙara da cewa, yanzu wannan mataki ya samu shiga tsare-tsaren gwamnati amma zai ɗauki lokaci kafin ɗabbaƙa shi. Wannan…
Read More
Tsohon Shugaban Ƙasar Sin Jiang Zemin ya rasu

Tsohon Shugaban Ƙasar Sin Jiang Zemin ya rasu

Daga CMG HAUSA Jiang Zemin, wato tsohon babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma tsohon shugaban kasar, ya rasu da tsakar ranar yau Laraba da karfe 12:13 a birnin Shanghai. Yana da shekaru 96 a duniya. Rahotanni sun ce kafin rasuwarsa ya sha fama da ciown sankarar jini da mutuwar wasu sassan jiki. Kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS), da zaunannen kwamitin majalissar wakilan jama’ar kasar Sin, da majalissar gudanarwar kasar, da kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar, da hukumar kolin rundunar sojoji ta JKS da jamhuriyar jama’ar kasar Sin suka…
Read More
Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka

Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka

Daga IBRAHIM YAYA Wani batu dake kara janyo hankalin duniya shi ne, matsalar sauyin yanayi. Abin da ya sa MDD ta shirya taruka a lokuta daban-daban, da nufin ganin an kawar da wannan matsala dake kokarin gagarar kwandila. Guda daga cikinsu shi ne taron COP27, na sassa da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD, da aka kammala a Masar ba da dadewa ba. A karshen wannan taro, an cimma matsayar kafa wani asusun musamman da nufin agazawa kasashen da wannan matsala da fi shafa. Baya ga kasancewar taron wani ginshiki mai muhimmanci na tabbatar da adalci.  Duk…
Read More
Gwamnati za ta fara bai wa ma’aikata magidanta hutun jego

Gwamnati za ta fara bai wa ma’aikata magidanta hutun jego

Daga WAKILINMU Gwamnatin Tarayya ta amince ta soma bai wa ma'aikatanta magidanta hutun jego na kwana 14 a duk lokacin da matansu suka haihu. Shugabar ma'aikatan gwamnati ta ƙasa, Dr Folasade Yemi-Esan ce ta bayyana haka cikin sanarwar da ta fitar ranar Litinin. Sanarwar ta ce bai wa ma'aikatan hutun jegon daidai yake da tanade-tanaden Kundin Dokokin Ma'aikatan Gwamnati na 2021. Gwamnati ta ce hutun na kwanakin aiki 14 ne amma ban da ranakun Asabar da Lahadi, kuma sau ɗaya a cikin shekara biyu. Yemi-Esan ta ce, sanarwar hakan ta fara aiki ne daga ranar 25 ga Nuwamban 2022.
Read More
A daina cin zarafin ‘ya’yan riƙo da masu aikatau

A daina cin zarafin ‘ya’yan riƙo da masu aikatau

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Akwai wata matsala da ta daɗe tana damu na a rai da ta shafi game da yadda wasu mutane ke ɗaukar 'ya'yan da ba nasu ba cikin su ba, a wulakance, musamman ma dai 'ya'yan riƙo da suke ɗauko su daga ƙauye ko gidajen 'yan uwa, don su taimaka musu, ko kuma marayu ne da iyayen su suka rasu. Akwai kuma batun yaran aiki da ake ɗauko su daga ƙauye ko daga gaban iyayen su, don su yi aiki a gidajen masu kuɗi ko ma'aikata, don su taya su aikin kula da gida da yara, a…
Read More
Siyasar Bana a Nijeriya: Me ya kamata mu yi?

Siyasar Bana a Nijeriya: Me ya kamata mu yi?

Daga NAFI'U SALISU Shakka babu lokaci ya yi da ya kamata al’ummar ƙasata Nijeriya mu dawo cikin hayyacinmu. Dole mu yi karatun ta-nutsu domin ƙwatar ‘yancinmu a siyasance, da hikimance, hakazalika a ilmance. Sanin kanmu ne cewa, Nijeriya ƙasa ɗaya ce, al’umma ɗaya, sannan ƙasarmu ta kasance babbar ƙasa da ke ƙunshe da arziki, wanda da shi ne wasu ‘yan tsirarun mutane suke abinda suka ga dama. Zuwa yanzu Nijeriya tana da shekaru 62 da samun ‘yancin kai daga Turawan Burtaniya (wato Turawan Mulkin-mallaka), waɗanda zuwansu Nijeriya ya yi matuƙar basu mamaki. Domin sun same mu cikin suttura da addininmu…
Read More
Ganduje ya haramta a adaidaita-sahu a Kano

Ganduje ya haramta a adaidaita-sahu a Kano

Daga WAKILINMU Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya haramta zirga-zirgar adaidaita-sahu a wasu manyan titunan Kano. Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Kano (KAROTA), wannan doka za ta fara aiki ne daga ranar Laraba, 30 ga Nuwamba. Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da ta fito ta hannun mai magana da yawun hukumar KAROTA, Nabilusi Na’isa, wanda aka raba wa manema labarai ranar Talata. Titunan da aka haramta wa ’yan adaidaita-sahun bi sun haɗa da Babbar Hanyar Ahmadu Bello, hanyar Mundubawa zuwa Gazawa da kuma hanyar Tal’udu zuwa Gwarzo. Gwamnatin jihar ta maye gurbin adaidaita-sahun da motoci bas-bas guda…
Read More
Kwamishina ta buƙaci a hukunta Aisha Buhari kan badaƙalar gana wa ɗalibi azaba

Kwamishina ta buƙaci a hukunta Aisha Buhari kan badaƙalar gana wa ɗalibi azaba

Daga BASHIR ISAH Kwamishina a Hukumar Kula da Harkokin ’Yan Sanada (PSC), Najatu Mohammed, ta yi kira da a hukunta matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, kan badaƙalar kamawa da gana wa Aminu Mohammed azaba da jami’an tsaro suka yi. Da kuma kama tsohuwar hadimar Aisha Buhari kan soshiyal midiya, Zainab Kazeem wadda ita ma aka lakaɗa mata duka kan zargin fallasa sirri. Aminu Mohammed matashi ne kuma ɗalibi a Jami’ar Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa. Najatu ta faɗa wa jaridar Daily Nigerian cewa abin da Aisha ta yi ɗaukar doka ne a hannu, don haka ta buƙaci jami’an tsaro…
Read More