Daga BASHIR ISAH
Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ta amince da Dokar Harshe ta Ƙasa wadda ta ba da damar koyar da harshen uwa a makarantun firamare a faɗin ƙasa.
Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya bayyana wa manema labarai hakan bayan kammala taron mako-makon da Majalisar ta saba shiryawa ranar Laraba a Abuja.
Ya ce da samuwar wannan doka, hakan na nufin daga yanzu da harshen uwa za a riƙa koyar da ‘yan firamare daga aji ɗaya zuwa shida.
Ya ƙara da cewa, yanzu wannan mataki ya samu shiga tsare-tsaren gwamnati amma zai ɗauki lokaci kafin ɗabbaƙa shi.
Wannan mataki in ji ministan, ana buƙatar ya shafi harsunan da ake da su a faɗin ƙasar.