Editor

9513 Posts
Ƙungiyar ɗalibai ta nemi afuwar Aisha Buhari kan kama Aminu Muhammad

Ƙungiyar ɗalibai ta nemi afuwar Aisha Buhari kan kama Aminu Muhammad

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar ɗalibai ta Ƙasa (NANS) ta nemi afuwar uwargidan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Aisha kan tsare wani ɗalibin jami’ar tarayya da ke Dutse Jigawa, Aminu Mohammed da jami’an ’yan sanda suka yi. Idan za a iya tunawa cewa, Hukumar SSS ta ce ta kama Aminu kan wani rubutu da ta wallafa a shafinsa na sada zumunta na yanar gizo da ta yi zargin ɓata sunan uwargidan shugaban Nijeriya, Aisha Muhammadu Buhari. A cewar rahotanni, Aminu Adamu Muhammed ya yi a watan Yunin 2022, inda ya wallafa a shafinsa na Tiwita cewa ‘Buhari ta ƙara nauyi sosai…
Read More
Kotu ta ɗaure Sufeto-Janar, Alkali Baba a kurkuku

Kotu ta ɗaure Sufeto-Janar, Alkali Baba a kurkuku

Daga WAKILINMU Babbar Kotun Tarayya mai zamanta Abuja, ta tura Sufeto-Janar na 'Yan Sanda, Usman Alkali Baba, zuwa kurkuku na wata uku. Kotun ta yanke wa Baba hukuncin ne saboda rashin bin umarninta. Da yake yanke hukuncin, Alƙalin Kotun, Mai Shari'a M. O. Olajuwon, ya ba da umarnin a ajiye Sufeto-Janar ɗin na tsawon wata uku har sai ya yi ɗa'a ga umarnin da da kotu ta ba tun ran 21 ga Oktoban 2011. Alƙalin ya ce idan bayan ƙarewar wata uku Baba bai aikata abin da ya kamata ba, za a sake tsare shi zuwa wani lokaci har sai…
Read More
Sin ta nuna kyakkyawar alƙiblar yaƙi da mummunan tasirin sauyin yanayi

Sin ta nuna kyakkyawar alƙiblar yaƙi da mummunan tasirin sauyin yanayi

Daga SAMINU HASSAN A ’yan shekarun baya-bayan nan, hankulan duniya na kara karkata ga zaƙulo dabarun dakile ƙalubalen sauyin yanayi, ƙarƙashin haɗin gwiwar dukkanin sassan ƙasa da ƙasa. Kuma a bana, yunkurin ƙasashen duniya a wannan fanni ya ƙarfafa, sakamakon taron COP27 na ɓangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MƊD da aka gudanar a baya bayan nan a ƙasar Masar, wanda ya kasance babban dandali ga ɗaukacin masu ruwa da tsaki, na hada ƙarfi da ƙarfe wajen lalubo dabarun gaggawa na shawo kan ƙalubalen sauyin yanayi. Ma’anar sauyin yanayiSauyin yanayi na nufin sauyi mai tsawo na…
Read More
Ya kamata Birtaniya ta waiwayi tarihi domin ɗaukar darasi

Ya kamata Birtaniya ta waiwayi tarihi domin ɗaukar darasi

Daga FA'IZA MUSTAPHA A cikin wannan mako ne ake sa ran shugaban Tarayyar Turai, Charles Micheal, zai ziyarci ƙasar Sin, bisa gayyatar da shugaba Xi Jinping ya yi masa. Wannan wani babban ci gaba ne a dangantakar dake tsakanin Sin da Turai, inda a karon farko, yawan cinikayya a tsakaninsu cikin shekarar da ta gabata, ya zarce dala biliyan 800, kana jari tsakanin ɓangarorin biyu, ya zarce dala biliyan 270. Lallai wannan ya shaida yadda cinikayya da kyakkyawar dangantaka tsakanin ɓangarorin biyu ke kyautata da kara farfaɗowa tare da haifar da ɗimbin sakamako da ribar moriyar juna. Sai dai a…
Read More
Shugaban Ƙasar Sin ya sha alwashin ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasarsa da Rasha a fannin makamashi

Shugaban Ƙasar Sin ya sha alwashin ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasarsa da Rasha a fannin makamashi

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya ce ƙasar sa a shirye take ta ƙarfafa haɗin gwiwa da Rasha a fannin makamashi. Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, cikin sakon da ya aike ga taron dandalin cinikayyar makamashi na Sin da Rasha karo na 4, ya ce haɗin gwiwa a fannin makamashi muhimmin jigo ne na haɗin gwiwar sassan 2, kuma muhimmin ƙarfi dake iya tabbatar da isasshen makamashi a duniya. Cikin wasiƙar tasa, shugaban na Sin ya ƙara da cewa, yayin da ake fuskantar haɗurra da ƙalubale daga sassan waje, Sin da Rasha sun…
Read More
Me mata suke so a wajen maza?

Me mata suke so a wajen maza?

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a filinmu na zamantakewa daga jaridarku mai farin jin ta Blueprint Manhaja. Kamar yadda a baya muka yi maƙala a game da abinda maza ke so gurin mata. A wannan makon kuma muna tafe da tambayar wai me mata suke so wajen maza? Tambayar nan mai tsauri ce kuma mai faɗi kamar dai maudu'inmu na makon da ya gabata. Wato wai me maza suke so a wajen mata? Inda muke sa ran shi ma na wannan makon za mu yi sukuwa mu yi zamiya mu cimma matsaya kamar makon…
Read More
Matashi ya nemi kotu ta hana iyayen budurwarsa aurar da ita

Matashi ya nemi kotu ta hana iyayen budurwarsa aurar da ita

Wani matashi ya yi ƙarar iyayen budurwarsa a gaban Babbar Kotun Shar’iar Musulunci da ke Hotoro a Kano yana neman kotun ta hana su aurar da ita ga wani matashi daban. Tunda farko matashin mai suna Imam Mukhtar Dala ya yi ƙarar budurwarsa Muhasin Auwal Dala da mahaifinta A.A. Dala da kakanta Sani Mai Alawayyo da kuma aminin babanta, Alhaji Audu, inda ya nemi kotu ta dakatar da auren da ake ƙoƙarin yi wa Muhasin ɗin saboda shi ne ya yi hidimar da zai aure ta. Haka kuma ya nemi a hana Muhasin Dala zuwa wurin kowane mutum don ɗaura…
Read More
Nijeriya ta gargaɗi ’yan ƙasar masu zuwa Amurka da Birtaniya su yi hattara da ɓarayi

Nijeriya ta gargaɗi ’yan ƙasar masu zuwa Amurka da Birtaniya su yi hattara da ɓarayi

Daga WAKILINMU Gwamnatin Nijeriya ta shawarci ’yan ƙasar da su zama masu kula da kayansu sosai duk lokacin da suka tashi tafiya zuwa ƙasashen Amurka da Birtaniya da sauransu, gudun faɗawa tarkon barayi. Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohammad ne ya yi wannan gargaydi ran Litinin a Abuja. Ministan ya ce abin damuwa ne ganin yadda ’yan Nijeriya masu zuwa Amurka da Birtaniya da sauransu, ke faɗawa tarkon ɓarayi inda suke sace musu kudi fasfo. Ya ce, “Waɗanda abin ya shafa a baya-bayan nan su ne waɗanda suka tafi Birtaniya wanda akasarinsu aka sace musu kayayyakinsu a manyan shaguna,…
Read More
An ɗaure ɗan sanda da ya sace kuɗin lalitar da ya tsinta

An ɗaure ɗan sanda da ya sace kuɗin lalitar da ya tsinta

An yanke wa wani tsohon ɗan sanda mai suna Mohammad Ghalayini hukuncin ɗaurin watanni 22 a gidan yari bisa samunsa da laifin satar Naira 36,000 (Fam 80) a wata lalitar da ta ɓata da aka miƙa ga ’yan sanda. A cewar rahotannin BBC a ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, 2022, an samu Ghalayini da laifin sata da kuma karkatar da tsarin shari'a bayan da wani ɗan sanda ya kai rahoton vacewar kuɗaɗen a watan Satumba, sannan aka ɗaure shi a watan Oktoba. Ba a ba shi izinin yin aiki ga 'yan sanda, hukumomin ’yan sanda na gida, Ofishin 'Yan…
Read More
Ɗan banga ya harbe mahaifinsa yayin gwada maganin bindiga

Ɗan banga ya harbe mahaifinsa yayin gwada maganin bindiga

Wani ɗan banga ya baƙunci lahira a yayin da yake gwada maganin bindiga a Jihar Adamawa. Magidancin da ya sha maganin bindiga ya ɗora bindigarsa ce a cikinsa sannan ya tursasa wa ɗansa mai shekara 19 ya harba ta. Harba bindigar da ɗan ya yi ke da wuya ta tashi da mahaifin, ta kuma yi sanadiyyar mutuwarsa. Kakakin ’yan sanda na Jihar Adamawa, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis a Ƙaramar Hukumar Jada ta jihar. Jami’in ya ce, su na gudanar da bincike kuma duk wanda ke da hannu a…
Read More