Editor

9513 Posts
Su waye Shuwa Arab (II)

Su waye Shuwa Arab (II)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A yau za mu cigaba da kawo wa masu karatu jarihin Shiwa Arab, kamar yadda mu ka fara a makon da ya gabata. Amma Idda da Badejo (Babu Shekara) sun ayyana cewa, rayuwa kala uku suke yi saboda rabuwar su kashi uku; manoma da kuma makiyaya ko kuma waɗanda suka haɗa duka biyu. Makiyaya da manoma su ne mazauna ƙauyuka na dindin da kuma garuruwa na dinin. Waɗanda suka haɗa noma da kiwo kuma su suke irin waccar rayuwa ta tashi-mu-je-mu. Zamantakewa: Yanayin zamantakewar jama’ar Shuwa-Arab cike take da taimakekeniya. Suna rayuwa a irin salon nan…
Read More
‘Yan Sama Jannati uku na ƙasar Sin za su yi aiki a kumbon Shenzhou-15

‘Yan Sama Jannati uku na ƙasar Sin za su yi aiki a kumbon Shenzhou-15

Daga CMG HAUSA Ofishin kula da aikin binciken sararin samaniya na kumbo mai ɗauke da 'yan sama jannati na ƙasar Sin ya bayyana cewa, ofishin ba da umurni na ayyukan kumbon binciken sararin samaniya na ƙasar Sin, ya tsaida ƙuduri cewa, 'yan jannati uku wato Fei Junlong, da Deng Qingming, da Zhang Lu za su yi aiki a kumbon Shenzhou-15, ƙarƙashin jagorancin Fei Junlong. Gobe Talata ne, za a harba kumbon Shenzhou-15 cikin sararin samaniya daga cibiyar harbar kumbona ta Jiuquan dake arewa maso yammacin ƙasar Sin. Mai fassara: Zainab
Read More
Za ka yarda da manufar “kashin dankali”?

Za ka yarda da manufar “kashin dankali”?

Daga BELLO WANG Yau na ga wannan labari: Charles Onunaiju, wani masanin ilimin hulɗar ƙasa da ƙasa na Najeriya, ya ce asusun tarayyar Amurka na ci gaba da ƙara kuɗin ruwa, matakin da ke iya haifar da mummunan tasiri ga ƙasashe masu tasowa. Don neman shawo kan matsalar hauhawar farashin kayayyaki, asusun tarayyar Amurka ya ƙara kuɗin ruwa har sau 6, tun farkon shekarar 2022. Amma me ya sa matakin ya shafi sauran ƙasashe? Saboda wannan manufar za ta janyo dalar Amurka daga kasuwannin ƙasa da ƙasa, don su koma ƙasar Amurka. Hakan kuma zai sa a dinga canza kuɗaɗen…
Read More
Sin: Ya kamata Amurka ta dakatar da mayar da batun ciniki da kimiyya a siyasance

Sin: Ya kamata Amurka ta dakatar da mayar da batun ciniki da kimiyya a siyasance

Daga CMG HAUSA A baya bayan nan, hukumar sadarwa ta Amurka, ta fitar da sanarwa dake cewa, an haramtawa kamfanonin ƙasar Sin da dama sayar da kayayyakin da ake amfani da su a harkokin sadarwa da na sanya ido a Amurka. Da yake tsokaci game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labarai na yau Litinin cewa, matakin Amurka ci gaba ne da fakewa da batun tsaron ƙasa wajen keta hakkokin kamfanonin Sin, tare da amfani da ƙarfin iko ba bisa ƙa’ida ba. Zhao ya ce Sin na matuƙar adawa da…
Read More
2023: Bashir Machina ya sake kayar da Sanata Lawan a kotu

2023: Bashir Machina ya sake kayar da Sanata Lawan a kotu

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu A ranar Litinin Kotun Ɗaukaka Ƙara dake zamanta a Abuja ta amince da takarar sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa a ƙarƙashin Jam’iyyar APC, Hon. Bashir Sheriff Machina. Kotun ta tabbatar da hukuncin da Babbar Kotun Tarayyar da ke Damaturu ta yanke tun da farko inda ta bayyana Bashir Machina a matsayin halastaccen ɗan takarar sanatan APC a Yobe ta Arewa. Bugu da ƙari, Kotun ta yi watsi da ƙarar da Jam’iyyar APC ta shigar kan rashin amincewar da ta sanya ɗaukaka ƙarar. Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem wadda ta yanke hukuncin, ta ce Babbar…
Read More
Ƙaddamar da ayyukan haƙar man fetur a iyakar Bauchi da Gombe

Ƙaddamar da ayyukan haƙar man fetur a iyakar Bauchi da Gombe

Assalam alaikum. Da farko dai muna maraba da wannan sabon aiki da za a ƙaddamar a Arewa, wanda a ranar Talata ne ake sa ran shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, zai ƙaddamar da ayyukan bunƙasa haƙar man fetur a yankin Kolmani da ke iyakar jihohin Bauchi da Gombe. Kamfanin samar da man fetur na Nijeriyar, NNPCL, ya ce shekara biyu da suka wuce ne aka tabbatar da gano tarin arzikin man fetur mai yawan da za a iya sayarwa a yankin. Wannan ne karon farko da ake haƙo man fetur a Arewacin Nijeriya. Bayanai sun nuna cewa akwai ƙarin wasu rijiyoyin…
Read More
Samun fetur a Arewa albarka ce, inji shugaban ’yan kasuwar manja a Gombe

Samun fetur a Arewa albarka ce, inji shugaban ’yan kasuwar manja a Gombe

Daga MOHAMMED ALI a Gombe Tun bayan bikin ƙaddamar da samun man fetur na farko a tarihin Arewa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi kwanan nan a Komaila da ke kan iyakar jihohin Bauchi da Gombe, wasu wasu mutane suke ta cece-kucen cewa wai siyasa ce kawai don a zaɓi jam'iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa a 2023. Sai dai kuma, shugaban ƙungiyar masu sana’ar cinikin manja na Jihar Gombe, Alhaji Usman Musa Chanji, ya ce sam batun ba haka ya ke ba, babu siyasa a ciki, mai makon haka ma, babban albarka ne wanda ’yan arewa…
Read More
Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci a gaggauta sakin ɗalibin da aka tsare kan sukar Aisha Buhari

Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci a gaggauta sakin ɗalibin da aka tsare kan sukar Aisha Buhari

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International, ta yi kira da a gaggauta sako ɗalibin nan na Jami'ar Tarayya da ke Dutse, Aminu Adamu Muhammed, wanda jami'an tsaro suka kama shi don ya soki matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari. Rahotanni sun ce, jami'an tsaron da ake zargin DSS ne suka damke matashin a ranar 8 ga Nuwamban2022 biyo bayan wasu kalamai da ya wallafa a shafinsa na Tiwita a kan Aisha Buharin. Saƙon da Muhammad ya wallafa a wannan rana ya nuna hotunan Aisha a yanayi na can baya da kuma yanzu, inda ya rubuta, "su…
Read More
Mahaifiyar ɗalibar Yauri da aka yi garkuwa da ita ta mutu saboda takaici

Mahaifiyar ɗalibar Yauri da aka yi garkuwa da ita ta mutu saboda takaici

Daga WAKILINMU Mahaifiyar ɗaya daga cikin ɗaliban Sakandiren Gwamnati a Yauri da aka yi garkuwa da su lokutan baya, ta rasu. Majiyarmu ta ce, takaicin sanin 'yarta na ɗauke da cikin masu garkuwar na daga cikin dalilan da suka yi ajalin matar. Majiyar ta ƙara da cewa, ana kyautata zaton mahaifiyar ta kwanta dama ne saboda tsananin damuwa da ta shiga sakamakon cikin da 'yan bindigar suka yi wa 'yarta bayan da suka yi garkuwa da ita. Yarinyar da lamarin ya shafa na ɗaya daga cikin ɗaliban makarantar su 11 da suka rage a hannun 'yan bindigar daga cikin ɗalibai…
Read More
An karrama mawallafin jaridun Manhaja, Blueprint a Kaduna

An karrama mawallafin jaridun Manhaja, Blueprint a Kaduna

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Rotary da ke Kaduna, ta karrama mawallafin jaridun Manhaja da Blueprint kuma mamallakin tashar We FM da ke Abuja, Alhaji Mohammed Idris Malagi (Kaakaki Nupe), da lambar yabo. Ƙungiyar ta karrama Alhaji Malagi ne saboda irn gudunmawarsa da ya bayar ga cigabanta. An miƙa wa Kaaki Nupe lambar ne a Kaduna a wajen taron asusun neman tallafi don amfanin marasa galihu da miƙa kyaututtuka da ƙungiyar ta shirya. A cewar Ƙungiyar, ta miƙa wa Alhaji Malagi lamabr ne domin nuna godiyarta dangane da gudunmawar da yake ba ta, da kuma ƙarfafa masa ci gaba da hakan.…
Read More