Editor

9513 Posts
Ƙidaya: ‘Yan Nijeriya miliyan 250 na iya tsunduma cikin fatara, inji Majalisar Ɗinkin Duniya

Ƙidaya: ‘Yan Nijeriya miliyan 250 na iya tsunduma cikin fatara, inji Majalisar Ɗinkin Duniya

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi iƙirarin cewa, aƙalla 'yan Nijeriya miliyan 250 na iya tsintar kansu a cikin tsananin halin ƙaƙa-nikayi na fatara a nan gaba. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Gidauniyar Majalisar Ɗinkin Duniya Kan Yawan Jama'a (UNFPA) a Nijeriya a yayin da Wakiliyar Ƙasa ta Gidauniyar, Ulla Mueller, ke gabatar da jawabi a wajen taron bin ba'asi da Majalisar Wakilai ta Nijeriya ta shirya kan ƙidayar jama'a da ƙasar za ta gudanar a 2023 a ɗakun taro na ƙasa da ƙasa dake Cibiyar Shehu Musa Yar'Adua a Abuja, Babban Birnin…
Read More
Lokaci yana ƙure wa Nijeriya kan hatsarin yawan jama’a, inji Gidauniyar Bill Gates

Lokaci yana ƙure wa Nijeriya kan hatsarin yawan jama’a, inji Gidauniyar Bill Gates

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Gidauniyar Melinda and Bill Gates ta bayyana cewa, lokaci yana ƙure wa Tarayyar Nijeriya kan hatsarin da ta ke fuskanta game da yawan jama'a, idan aka yi la'akari da yadda cigaban ƙasar ke yin tafiyar hawainiya. Gidauniyar ta bayyana hakan ne a wajen taron da Majalisar Wakilai ta Nijeriya ta shirya ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, a, wanda aka gudanar ranar 21 ga Nuwamba,2022, a ɗakin taro na Shehu Musa Yar'Adua dake Abuja. Daraktan Ƙasa a Nijeriya na Gidauniyar Gates, Jeremie Zoungrana, wanda ya aike da jawabin fatan alheri a wajen…
Read More
Gwamnati ta jinkirta dawo da aikin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Gwamnati ta jinkirta dawo da aikin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta sanar da jinkirta dawo da zirga-zirgar jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja da ta ayyana yi a ranar Litinin ɗin nan. Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a jiya Lahadi. Ministan ya mayarwa da ’yan Nijeriya murnarsu ciki a yayin rangadin da ya kai kan layin dogon da ke Kaduna domin tabbatar da matakin shirye-shiryen da aka kammala gabanin dawo da jigilar. Ministan wanda bai fayyace ainihin ranar da za a dawo da jigilar ba, ya ce jinkirin da za a fuskanta ba zai wuce na tsawon…
Read More
INEC ta za fara ba da katin zaɓe na dindindin

INEC ta za fara ba da katin zaɓe na dindindin

Daga MAHDI M. MUUHAMMAD Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta sanar da ranar fara ba da katin zaɓe na dindindin tare da ƙara gargaɗar masu karya dokokin zaɓe gabanin zaɓen 2023. Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zave na hukumar na ƙasa, Festus Okoye Esq, ya fitar da ranar Asabar a Abuja. Hukumar ta yi zamanta ne a ranar Asabar 26 ga watan Nuwamba, 2022, inda ta tattauna kan batutuwa da dama da suka haɗa da kwanan wata da tsarin karɓar katin zaɓe na dindindin (PVC)…
Read More
Na’urar ROV ta ƙasar Sin ta kammala nutson mita 4,308 a ƙarƙashin teku

Na’urar ROV ta ƙasar Sin ta kammala nutson mita 4,308 a ƙarƙashin teku

Daga CMG HAUSA Cibiyar kula da binciken kimiyyar zurfin teku da ayyukan injiniya ta ƙasar Sin ko IDSSE, wadda ke ƙarƙashin cibiyar nazarin kimiyya ta ƙasar Sin, ta ce na’urar nutso cikin teku mai zurfi ta ƙasar Sin ko ROV, ta kammala nutson mita 4,308 a tekun kudancin Sin. IDSSE wadda ta bayyana hakan a ranar Alhamis, ta ce an yi dakon na’urar ROV da jirgin ruwan dakon na “Exploration-2”, kuma na’urar ROV ta gudanar da ayyuka yadda ya kamata bisa ingancin ƙirar ta, wanda hakan ya nuna na’urar na da ikon gudanar da binciken kimiyya da injiniyanci a ƙarƙashin…
Read More
Sin na ƙara faɗaɗa cibiyoyin samar da makamashi mai tsafta

Sin na ƙara faɗaɗa cibiyoyin samar da makamashi mai tsafta

Daga CMG HAUSA Ƙasar Sin na ƙara faɗaɗa kafa turakun samar da nau’o’in makamashi da ake iya sabunta amfani da su, tun daga farkon shekarar nan ta bana, yayin da mahukuntan ƙasar ke yunkurin wanzar da ci gaba, ba tare da gurbata muhalli ba. Alƙaluman hukumar kula da makamashi ta ƙasar sun nuna cewa, ya zuwa ƙarshen watan Oktoba da ya shuɗe, Sin ta kafa jimillar cibiyoyin samar da lantarki da ya kai kusan kilowatt biliyan 2.5, adadin da ya nuna ƙaruwar kaso 8.3 bisa dari a shekara ɗaya. Cikin jimillar, adadin lantarki ta ƙarfin iska ya ƙaru da kaso…
Read More
Sakamakon binciken jin ra’ayin jama’a: Sama da kashi 80 na masu amsa tambaya a duniya na kiran da a kauce wa samun ƙaruwar sabbin masu harbuwa da cutar COVID-19

Sakamakon binciken jin ra’ayin jama’a: Sama da kashi 80 na masu amsa tambaya a duniya na kiran da a kauce wa samun ƙaruwar sabbin masu harbuwa da cutar COVID-19

Daga CMG Hausa A halin yanzu dai ana ci gaba da samun ɓullar cutar numfashi ta COVID-19 a faɗin duniya. Tun daga farkon wannan shekara, adadin waɗanda suka mutu a duk duniya sakamakon cutar ya zarce miliyan ɗaya, kuma har yanzu kwayar cutar tana ci gaba da canzawa. A ‘yan kwanakin da suka gabata, sashen CGTN na babban rukunin gidan rediyo da talibijin na ƙasar Sin wato CMG, ya ƙaddamar da wani bincike tsakanin masu amfani da yanar gizo a duk faɗin duniya, wanda sakamakon sa ya nuna cewa, sama da kashi 60% (60.44%) na waɗanda suka amsa tambayoyi, sun…
Read More
A hau jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna gaba-gaɗi, ba fargaba, inji Ministan Sufuri

A hau jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna gaba-gaɗi, ba fargaba, inji Ministan Sufuri

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Ministan Sufurin Nijeriya, Mu'azu Jaji Sambo, ya yi kira ga 'yan Nijeriya masu sha'awar hawa jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna da su yi shirin hawa gaba-gaɗi ba tare da wata fargaba ba, yana mai cewa, an yi kyakkyawan tanadi, don kare rayuka da lafiyar fasinjoji a yayin da zirga-zirgar jingin ta dawo. Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a yau Lahadi, ciki har da Blueprint Manhaja, yayin duba irin shirin da Gwamnatin Tarayya ta yi na sake buɗe zirga-zirgar jiragen ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna. "Ina so…
Read More
Najeriya na gab da rasa jiragen saman da Shugaban Ƙasa ke amfani da su saboda tarin bashi – Rahoto

Najeriya na gab da rasa jiragen saman da Shugaban Ƙasa ke amfani da su saboda tarin bashi – Rahoto

Daga WAKILINMU Alamu masu ƙarfi sun nuna Najeriya na gab da rasa jiragen saman da Shugaban Ƙasa ke amfani da su saboda bashin da ya yi mata katutu. Rahoton da jaridar Punch ta wallafa ranar Lahadi ya nuna hakan na shirin faruwa ne saboda bashin da wasu kamfanoni ke bin ƙasar wanda ta ƙagara biya. Jiragen da lamarin ya shafa da su ake amfanin wajen jigilar Shugaban Ƙasa da mataimakinsa da iyalansu haɗi da manya jami'an gwamnatin ƙasar. Kwamanda mai kula da jiragen, Air Vice Marshal Abubakar Abdullahi ne ya bayyana haka a lokacin da yake kare kasafinsa a Majalisar…
Read More
DA ƊUMI-ƊUMI: Sai da Lambar ‘Yan Ƙasa za a riƙa hawa jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna

DA ƊUMI-ƊUMI: Sai da Lambar ‘Yan Ƙasa za a riƙa hawa jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da samar da tsarin yin amfani da Lambar 'Yan Ƙasa (NIN) ga kowane fasinja dake sha'awar hawa jirgin Abuja zuwa Kaduna. Ministan Sufuri na Nijeriya, Mu'azu Jaji Sambo, ne ya bayyana hakan a yau Lahadi lokacin da ya ke zagayawa da 'yan jarida, ciki har da Blueprint Manhaja, don duba irin shirye-shiryen da aka yi, don dawo da zirga-zirgar, wacce aka dakatar da ita ranar 28 ga Maris, 2022, sakamakon harin ta'addanci da aka kai masa har aka kashe wasu fasinjoji kuma aka yi awon gaba da wasu. Ministan…
Read More