27
Nov
Daga AMINA YUSUF ALI "Abin ya sha kanmu, je ki CBN ki kai kukanki!" Wannan ita ce amsar da mahukuntan wani banki suka ba wa wata mata bayan da kuɗaɗenta har Naira 91,900 suka ɓace ɓat, daga asusun ajiyarta na bankin. Ita dai wannan mata mai suna Rebecca Jolaoso, 'yar kasuwa ce 'yar asalin garin Ibadan. Rebecca ta zayyyana yadda Bankin Polaris ya kasa yi mata wani kataɓus bayan Naira 91,900 zuwet ta fita daga asusun ajiyarta na bankin Polaris ba bisa ƙa'ida ba. Duk kuwa tana tare da katin cirar kuɗinta a tare da ita. Rebecca ta bayyana cewa,…
