Shugabar matan jam’iyyar PDP ta sauya sheƙa zuwa APC a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu

Shugabar matan jam’iyyar PDP a jihar Yobe, Hajiya Hauwa Abore tare da magoya bayan ta sun sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC a Jihar Yobe.

Da take bayar da dalilan da suka sanya ta sauya sheƙar, Hajiya Hauwa ta ce ita da mabiyanta sun yanke shawara shigowa jam’iyyar APC ne sakamakon ci gaban da Gwamnatin Jihar Yobe ta samar haɗi da aiwatar da ayyukan inganta rayuwar al’ummar jihar- a ƙarƙashin Gwamna Mai Mala Buni, su ne suka ja ra’ayin ta tare da ba ta ƙwarin gwiwar sauya sheƙa.

Har wa yau, tsohuwar shugabar matan jam’iyyar PDP ta buƙaci dukkan mabiyanta su mara mata baya kuma su biyota domin ciyar da jihar Yobe gaba; ta ce hakan shi ne burin kowane ɗan kishin jihar kana kuma ta jinjina wa Gwamna Buni bisa ga yadda gwamnatinsa ke ƙarfafa matasa da mata.

Haka kuma, ta yaba wa Gwamna Buni dangane da muhimman ayyukan raya jihar da ci gaban al’ummar jihar, waɗanda ya aiwatar da suka ƙunshi gina hanyoyin mota, makarantu, asibitoci tare da ɗakunan shan magani.

Ta ce ayyuka ne waɗanda suka cancanci a yaba wa gwamnatin jihar tare da bata cikakken haɗin kai da goyon baya domin samun wanzuwarsu da samar da wasu sabbi.

Hajiya Hauwa Abore ta yi kira na musamman ga baki ɗayan al’ummar jihar Yobe su fito ƙwansu da ƙwarƙwata su marawa Gwamnatin Mai Mala Buni baya, inda kuma ta sha alwashin aiki tukuru wajen jawo hankalin mata su zabi yan takarar da jam’iyyar APC ta tsayar a jihar a kowane mataki domin samun gagarumar nasara a babban zaɓen 2023.