Editor

9513 Posts
Jam’iyyun siyasa a Nijar sun taya murnar buɗe babban taron wakilan JKS karo na 20

Jam’iyyun siyasa a Nijar sun taya murnar buɗe babban taron wakilan JKS karo na 20

Daga CMG HAUSA A yayin da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20 ke gudana, jam'iyyun siyasar Nijar sun aike da wasiƙu, zuwa ga kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta ƙasar Sin, da babban sakataren kwamitin ƙolin jam’iyyar Xi Jinping, domin taya murnar nasarar da aka cimma ta gudanar da babban taron. Shugaban riko na jam'iyyar PNDS-Tarayya mai mulkin Nijar, kuma babban wakilin shugaban ƙasar, Foumakouye Gado ya bayyana cewa, a ƙarƙashin jagorancin babban sakatare Xi Jinping, ƙasar Sin ta samu gaggaruman nasarori a fannonin zamanantar da al'ummar ƙasar, kana ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar…
Read More
Ƙasar Sin ta taimakawa mutane dubu ɗari dake ƙauyuka a Uganda damar kallon shirye-shirye ta tauraron ɗan Adam

Ƙasar Sin ta taimakawa mutane dubu ɗari dake ƙauyuka a Uganda damar kallon shirye-shirye ta tauraron ɗan Adam

Daga CMG HAUSA A ranar Asabar din da ta gabata ce, ƙasar Sin ta yi nasarar kammala aikin kafa na’urar kama shirye-shiryen talabijin ta tauraron dan-adam a ƙauyuka 900 dake ƙasar Uganda a hukumance, waɗanda a baya suke fuskantar ƙalubalen hanyoyin sadarwa. Ministan watsa labarai, sadarwa da fasaha da ba jagoranci na ƙasar Uganda Chris Baryomunsi ne, ya jagoranci bikin miƙa aikin da aka gudanar a ƙauyen Katabi dake gundumar Wakiso a tsakiyar ƙasar. Ya yaba wa ƙasar Sin bisa tallafin fasaha da take bai wa Uganda. Yana mai cewa, tallafin zai taimaka wajen samar da ci gaba ga al’ummomin…
Read More
Ranar ’ya’ya mata: Ƙungiyar Rotary ta ɗauki nauyin karatun yara kurame 40

Ranar ’ya’ya mata: Ƙungiyar Rotary ta ɗauki nauyin karatun yara kurame 40

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Larabar da ta gabata ne kwamitin ƙarfafa wa ’ya’ya mata da haɗin gwiwar ƙungiyar Rotary da ke Abuja da ƙungiyoyi masu zaman kansu (NGO) suka ɗauki nauyin karatun da yara kurame 40 da ba su zuwa makaranta. Ƙungiyoyi masu zaman kansu sun ƙaddamar cigaban ƙwararrun matasa, cigaban ƙarfafawa da LexF H Humanity. Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, ƙungiyoyin masu zaman kansu sun kuma bayar da gudummawar kayayyaki ga ɗaliban. An bai wa ’yan mata ɗari da ashirin kwamfukar tafi-da-gidanka kowacce, maza 180 kuma an ba su wasu kayyayaki. An kuma…
Read More
Zugacoin na daga cikin kamfanoni ukun kan gaba a harkar kuɗin yanar gizo a duniya – Farfesa Jibia

Zugacoin na daga cikin kamfanoni ukun kan gaba a harkar kuɗin yanar gizo a duniya – Farfesa Jibia

Daga WAKILINMU Wani tsohon malami a tsangayar koyar da kimiyyar siyasa a Jami'ar Bayero da ke Kano, Farfesa Aliyu Abdullahi Jibia, ya ce kuɗin kasuwanci na yanar gizo mai suna Zugacoin ɗaya ne daga cikin kamfanoni 3 da suka fi shahara a harkar kuɗin yanar gizo a duniya. Aliyu Jibia, ya bayyana haka ne a yayin da Jaridar Hausa Daily Post ta yi bikin karrama shugaban gidauniyar Samzuga, wanda ya assasa Zugacoin da Green Zugacoin. Ya kara da cewa, “Archbishop Farfesa SamZuga, jami’in diflomasiyya ne a tsarin International Society OF Diplomats and Global Emissary Council, wanda shine shugaban tattalin arziki…
Read More
Kamfanin takin Dangote zai bunƙasa noma a Nijeriya – NACCIMA

Kamfanin takin Dangote zai bunƙasa noma a Nijeriya – NACCIMA

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban ƙungiyar 'yan kasuwa, masana'antu, ma'adinai da aikin gona ta Nijeriya (NACCIMA) Olusola Obadimu, ya ce, kamfanin takin urea na Dangote zai bunƙasa cigaban noma a ƙasar. Obadimu ya bayyana haka ne ranar Asabar a Legas ta hanyar wani rahoto daga ziyarar ban girma da ya kai kamfanin takin Dangote da ke unguwar Ibeju Lekki. Ya bayyana cewa, aikin zai kuma tabbatar da samar da abinci da kuma samar da guraben ayyukan yi ga ’yan Nijeriya da sauran ’yan Afirka kai tsaye da kuma a fakaice. “Babban maqasudin ziyarar shi ne don jin daɗin tasirin aikin…
Read More
Kira ga matasa a kan bangar siyasa

Kira ga matasa a kan bangar siyasa

A yanzu haka an buga kugen siyasa, masu neman ƙuri'un jama’a za su fara bazama neman goyon bayansu da kuma ƙuri'unsu. A irin wannan lokacin ne ’yan siyasa suke amfani da matasa domin jan hankalin jama’a su zaɓe su da kuma yin barazana ga waɗanda suka tabbatar ba za su zaɓe su. A duniyar dimokuraɗiyya kuma (musamman a Nijeriya) babu abin da ’yan siyasa suke amfani da shi wajan yaudarar al’umma a wannan zamani face sai sun danganta shi da rayuwar matasa, kasancewar babu wani buri da matasa suke buƙata face suga sun tsinci rayuwarsu cikin sauƙi da samun ingancin…
Read More
Rufe kafofin yaɗa labarai: Ka hanzarta gyara kuskuren da ka aikata, kiran NUJ ga Matawalle

Rufe kafofin yaɗa labarai: Ka hanzarta gyara kuskuren da ka aikata, kiran NUJ ga Matawalle

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), ta yi kira ga Majalisar Tsaron Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar, Bello Muhammad Matawalle, da ta janye matakin da ta ɗauka na rufe wasu kafofin yaɗa labarai a jihar. Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi, ƙungiyar ta ce an jiyo Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, lbrahim Dosara na cewa, kafafen da lamarin ya shafa su ne; Tashar NTA da Gamji TV da Umma TV da kuma Pride FM. A cewarsa, an ɗauki matakin da aka ɗauka a kan kafafen ne saboda saɓa dokar aiki da suka yi, inda…
Read More
Garƙame kafofin yaɗa labarai: BON ta yi tir da matakin Matawalle

Garƙame kafofin yaɗa labarai: BON ta yi tir da matakin Matawalle

Daga BASHIR ISAH Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labarai ta Nijeriya (BON), ta nuna kaɗuwarta da kuma Allah wadai da matakin da Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ɗauka na garƙame wasu kafofin yaɗa labarai huɗu mallakar gwamnati da masu zaman kansu a jihar. Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi mai ɗauke da sa hannun Sakatarenta, Dr. Yemisi Bamgbose, kuma a matsayin martani ga matakin na Matawallen ya ɗauka, BON ta ce a dokance Gwamnan ba shi da ikon da zai ba da umarnin rufe kafafen, kuma hakan da ya yi tamkar cin mutunci ne da kuma yin…
Read More
Yukren, ba ma fatan yaƙin duniya na uku

Yukren, ba ma fatan yaƙin duniya na uku

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA An yi yaƙin duniya na ɗaya da na biyu inda a ka yi asarar rayuka da dukiya don haka sam ba a fatan yaƙin duniya na uku. Yaƙin duniya na ɗaya daga 1914-1918 ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji miliyan 9 inda farar hula miliyan 5 su ma su ka rasa ran su. Yaƙin ya shafi kusan dukkan sassan duniya kama daga Amurka, Turai, Afurka, Daular Othman, Daular Rasha da sassan Asiya. Shi kuma yaƙin duniya na biyu da ya fara daga 1939-1945 ya tattara dukkan duniya kuma ya faro ne a sanadiyyar mamaye ƙasar Poland da…
Read More
Ɓatan Naira tiriliyan biyar: Majalisa ta fara binciken hukumomi 252

Ɓatan Naira tiriliyan biyar: Majalisa ta fara binciken hukumomi 252

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kwamitin Kula da Asusun Buƙatu na Majalisar Dokokin Tarayya, ya fara binciken kashe Naira tiriliyan 5 da Hukumomi 252 suka yi tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021. Binciken na zuwa ne bayan gano hukumomi da dama na karɓar kuɗaɗe daga Asusun ba tare da sahalewar kwamitin da doka ta ba wa damar sa ido a kai ba da Majalisar Dattawan ta yi. Shugaban Kwamitin, Sanata Mathewa Urhoghide ya ce, “muna so mu ga yadda aka kashe waɗannan kuɗaɗen ne, saboda akwai ruɗani akan tsarin fitar da kuɗin. Ya kuma ce, Majalisar za ta aika da sammacin tiso…
Read More