Editor

9513 Posts
Majalisa za ta binciki sojojin ruwa bisa ƙone jirgin da suka kama da ɗanyen man sata

Majalisa za ta binciki sojojin ruwa bisa ƙone jirgin da suka kama da ɗanyen man sata

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Wakilai ta yanke shawarar bincikar jami’an Rundunar Sojojin Ruwa bisa zargin su da bankawa tare da ƙone jirgin ruwan da suka kama maƙare da ɗanyen man Nijeriya na sata. Hakan ya biyo bayan amincewa da ƙudirin gaggawa kan muhimmancin qasa da ɗan majalisar wakilai Onofiok Luke (PDP- Akwa-Ibom) ya gabatar a zaman majalisar da aka yi ranar Laraba a Abuja. Taken ƙudirin nasa shi ne: ‘Akwai buƙatar a gaggauta gudanar da bincike kan yadda aka ƙona jirgin mai da ake zargin jami’an tsaro na da hannu wajen satar mai’. Hon. Luke ya gabatar…
Read More
Matawalle ya rufe tashoshin yaɗa labarai huɗu bisa zargin yaɗa taron PDP

Matawalle ya rufe tashoshin yaɗa labarai huɗu bisa zargin yaɗa taron PDP

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwanatin Jihar Zamfara ta bada umarnin gaggawa na rufe tashoshin yaɗa labarai guda huɗu da ke Gusau, babban birnin jihar. Jawabin rufe tashoshin ya fito ne daga bakin kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Ibrahim Dosara, a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ranar Asabar. Dosara ya bayyana cewar tashoshin da lamarin ya shafa sun haɗa da Tashar Talabijin ta NTA da Radio Pride FM da Al'umma TV da kuma Tashar Talabijin ta Gamji TV. Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, rufewar ya biyo bayan wani rikicin siyasa da ya yi sanadin mutuwar wasu mutum…
Read More
An buɗe babban taron wakilan JKS karo na 20

An buɗe babban taron wakilan JKS karo na 20

Daga CMG HAUSA An buɗe babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin JKS karo na 20, da misalin ƙarfe 10 na safiyar yau Lahadi a Beijing, fadar mulkin ƙasar Sin. Wakilan jam’iyyar, gami da waɗanda aka ba su goron gayyata na musamman sama da 2300 sun halarci taron, tare da wasu da ba ’yan jam’iyyar kwaminis din ba da sauransu. Za kuma a rufe taron a ranar 22 ga wata. A wajen taron, za a saurara, gami da duba rahoton aiki na kwamitin ƙolin JKS na 19, da duba rahoton aikin da kwamitin ladabtarwa na kwamitin ƙoli na JKS…
Read More
An rantsar da sabon Gwamnan Ekiti

An rantsar da sabon Gwamnan Ekiti

Daga BASHIR ISAH An rantsa da Abiodun Oyebanji a matsayin sabon Gwamnan Jihar Ekiti wanda hakan ya kawo ƙarshen gwamnatin Kayode Fayemi a jihar. A ranar Lahadi Alƙalin Alƙalan Jihar Ekiti, Mai Shari'a Oyewole Adeyeye ya rantsar da Oyebanji da mataimakiyarsa, Misis Monisade Afuye inda za su ci gaba da riƙe ragamar mulkin jihar nan da shekaru huɗu masu zuwa. Taron rantsarwar ya samu mahalarta daga nesa da kusa, ciki har da Gwamna Rotimi Akeredolu da Gwamna Gboyega Oyetola na Jihar Osun da tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose da sauran baƙi masu yawan gaske. Oyebanji, wanda kafin wannan lokaci shi…
Read More
Xi ya yi bayani kan muhimman nasarori uku da aka cimma cikin shekaru 10 da suka gabata

Xi ya yi bayani kan muhimman nasarori uku da aka cimma cikin shekaru 10 da suka gabata

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Lahadi cewa, cikin shekaru 10 da suka gabata, an samu wasu manyan nasarori 3 masu matukar muhimmanci, wandada suka shiga tarihin JKS da al’ummar ƙasar. Xi Jinping ya bayyana yayin buɗe babban taron mambobin JKS karo na 20 cewa, “Mun cika shekaru 100 da kafuwar JKS, gami da mun shiga wani sabon zamani na gurguzu mai sigar ƙasar Sin, kuma mun fatattaki ƙangin talauci baki ɗaya, kana mun kammala ginin al’umma mai matsakaicin ci gaba ta kowanne ɓangare, wato dai, mun cika burinmu na farko a lokacin da…
Read More
Zan kawo ƙarshen matsalar tsaro a bana – Buhari

Zan kawo ƙarshen matsalar tsaro a bana – Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa zai miƙa wa shugabanni masu zuwa a 2023 ƙasar ba gara ba zago, inda ya tabbatar da cewa, gwamnatinsa za ta kawar da duk wani nau’in ta’addanci. Shugaban Ƙasar a ranar Talata, 11 ga Oktoba, 2022, ya bayar da tabbacin ne a taron Bayar da Lambar Yabo ta Ƙasa na shekarar 2022 da aka gudanar a ɗakin taro na ƙasa da ƙasa da ke Abuja, inda aka karrama ’yan Nijeriya sama da 400 da wasu baqi bakwai da yabo na ƙasa daban-daban. “Za mu cigaba da…
Read More
Na goyi bayan sayar da NNPC, inji El-Rufai

Na goyi bayan sayar da NNPC, inji El-Rufai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce, Gwamnatin Nijeriya ta gaza a ɓangaren mai da iskar gas, don haka ya kamata ta janye kanta daga fannin. El-Rufai ya ce, babu amfani gwamnati ta ci gaba da harkar mai, tunda duk abin da yi a ɓangaren, ciki har da cefanar da NNPC, haƙa ba ta cimma ruwa ba. “Harafin L da aka ƙara a sunan NNPC babu abin da ya sauya; har yanzu kuɗaɗenmu suke ci, suna cewa, an samu riba, amma ba mu ga ko sisi ba. “NNPC babbar matsala ce a Nijeriya, wadda dole mu…
Read More
Nijeriya a matsayin ƙasar da ke fama da yunwa a duniya

Nijeriya a matsayin ƙasar da ke fama da yunwa a duniya

Rahotanni daga Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa sama da mutane miliyan 113 a faɗin ƙasashe 53 ne suka fuskanci matsananciyar yunwa a shekarar da ya gabata tare da rikici, annobar sauyin yanayi da kuma matsalolin tattalin arziki wanda ke haddasa rikicin abinci. Aƙalla ’yan Nijeriya miliyan 25 ne ke fama da yunwa, yayin da mutane miliyan 9.3 ke fama da matsanancin ƙarancin abinci, dai-dai lokacin da ƙasar ke tsaka da fama da tashen-tashen hankula na masu ɗauke da makamai. Nijeriya na fuskantar rikici daga kowane ɓangare, wanda ke ke daƙile hanyoyin cigaban ƙasar. Ba wai helkwatar talauci ta duniya…
Read More
Kada a bari ASUU ta sake shiga yajin aiki a ƙasar nan, kiran Gbajabiamila ga Gwamnati

Kada a bari ASUU ta sake shiga yajin aiki a ƙasar nan, kiran Gbajabiamila ga Gwamnati

Daga BASHIR ISAH Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya a kan kada ta Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) ta sake shiga yajin aiki a ƙasar nan. Gbajabiamila ya faɗi haka ne a martanin da ya yi ranar Juma'a dangane da janye yajin aiki na wata takwas da ASUU ta yi kwanan nan. Ya ce har yanzu ba a warware matsalolin da ke tsakani ba, don haka ya buƙaci gwamnati da ƙungiyoyi da sauran 'yan ƙasa da a soma tattaunawa kan makomar manyan makarantun gwamnatin ƙasar nan. Ya ƙara da cewa, "Ina godiya ga takwarorina na Majalisar…
Read More
Wakilin Sin ya buƙaci a ƙara zurfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe masu tasowa

Wakilin Sin ya buƙaci a ƙara zurfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe masu tasowa

Daga CMG HAUSA Jiya Jumma’a zaunannen wakilin ƙasar Sin dake MƊD Wang Hongbo ya bayyana cewa, gudanar da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe masu tasowa, muhimmiyar dabara ce, a daidai lokacin da suke kokarin raya ƙasa bisa fifikonsu na musamman, don haka ƙasar Sin tana tsayawa tsayin daka domin goyon bayan haɗin gwiwar, kuma ta yi kira ga ƙasa da ƙasa da su haɗa kai domin kara zurfafa haɗin gwiwar. Wang Hongbo ya faɗi haka ne yayin babban taron MƊD karo na 77 game da batun “sabuwar ajandar raya birane” da “raya harkokin ƙasa da ƙasa”, inda ya yi tsokaci cewa,…
Read More