Editor

9513 Posts
2023: Rundunar ’Yan Sanda ta ja kunnen dogarin matar Atiku bisa riƙe mata jaka

2023: Rundunar ’Yan Sanda ta ja kunnen dogarin matar Atiku bisa riƙe mata jaka

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta ja kunnen wata ’yar sanda da har yanzu ba a bayyana sunanta ba, saboda riƙe jakar Titi, matar ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar PDP a Babban Zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ’yar sandar da ta kasance dogari ga matar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar. Matar Atiku Titi, a ranar Laraba, 5 ga Oktoba, 2022, ta gabatar da wani shiri da ya mayar da hankali kan mata a Abuja kuma mijin nata ya raba hotuna daga taron, wanda ya nuna ta a tsaye da ’yar sanda tana riƙe da jaka a bayanta. Kafofin…
Read More
2023: Abacha ya yi ɓatan dabo a jerin ’yan takarar gwamnan Kano

2023: Abacha ya yi ɓatan dabo a jerin ’yan takarar gwamnan Kano

Daga AMINA YUSUF ALI Sunan Muhammad Abacha ya yi vatan dabo a cikin jerin sunayen 'yan takarar Gwamnan Kano a 2023 da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Nijeriya (INEC) ta saki a ranar Talatar da ta gabata.  Haka zalika, sunan ɗan takarar gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin jami'yyar LP, Bashir Ishaq Bashir shi ma ya yi layar zana a dai jadawalin na INEC. Amma sai aka maye gurbin sunansa da sunan wani Abdullahi Mohammed Raji. Shi kuma Assadiq Wali, sunansa shi ne ya fito a matsayin ɗan takarar na PDP a jihar Kano. Wannan ya sanya 'yan jam'iyya cikin…
Read More
2023: Bakin alƙalami ya bushe kan batun sauya ’yan takara, inji INEC

2023: Bakin alƙalami ya bushe kan batun sauya ’yan takara, inji INEC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta ce, ba za ta amince da janyewa ko sauya sheƙa ba bayan fitar da jerin sunayen ’yan takarar da za su tsaya takara a zaven 2023. Sai dai hukumar ta ce, za a iya yin maye gurbin ne kawai idan mutum ya mutu kamar yadda sashi na 34(1) na dokar zaɓe ya tanada ko kuma bisa umarnin kotun da ta dace. Gargaɗin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zace Barista Festus Okoye…
Read More
Ronaldo na da damar tafiya a duk lokacin da ya so – Man United

Ronaldo na da damar tafiya a duk lokacin da ya so – Man United

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta ce ta na a shirye idan har Cristiano Ronaldo zai sake jarraba barin ƙungiyar a watan Janairu, idan har ɗan wasan gaban ya gaza samun wuri a tawagar Erik Ten Hag, kamar yadda wasu majiyoyi suka bayyana. Ronaldo mai shekaru 37 ya yi zaman benci a wasan da Man United suka sha kashi 6-3 a hannun Man City a wasan hamayya da suka gwabza a gasar Firmiyar Ingila a ƙarshen makon da ya wuce, haka zalika bai fara a wasan da suka yi rashin nasara 4-0 a hannun Brentford…
Read More
Akwai matsala a tsaron bayan Liverpool – Klopp

Akwai matsala a tsaron bayan Liverpool – Klopp

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, Jurgen Klopp ya amsa cewa dole ne tawagarsa ta sake lale, tare da ƙara ƙaimi a kan yadda ta ke tsaron baya, dai dai lokacin da ƙungiyar wadda ta ƙarƙare a matsayin ta biyu a kakar da ta gabata, ga fama da rashin nasara a wannan kaka. Liverpool wadda yanzu haka ke matsayin ta 9 a teburin gasar Firimiya, bayan nasara a wasanni 2 kacal daga cikin 7 da ta doka a wannan kaka. Ƙungiyar dai na ci gaba da shan caccaka musamman daga magoya baya, ganin yadda…
Read More
An yi zirga-zirgar da ta haura miliyan 400 yayin bikin kafuwar jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin na bana

An yi zirga-zirgar da ta haura miliyan 400 yayin bikin kafuwar jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin na bana

Daga CMG HAUSA Ma’aikatar raya al’adu da yawon shakatawa ta ƙasar Sin, ta ce bisa alƙaluman ƙididdiga, adadin zirga-zirgar da aka yi a cikin gida, yayin bikin ranar tunawa da kafuwar jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin ta bana, ta kai miliyan 422. Kuma cikin ranakun hutun mako guda na wannan biki, an tattara kuɗaɗen shiga da yawan su ya kai kuɗin Sin RMB yuan biliyan 287.2, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 40.45. Alƙaluman sun nuna yadda a yayin hutun, masu yawon bude ido suka fi yin gajerun tafiye-tafiye, yayin da masu shakatawa na cikin gida suka fi ziyartar lambunan shan iska na…
Read More
Za a ƙaddamar da cibiyar watsa labaru ta taron wakilan JKS karo na 20 a ranar 12 ga watan Oktoba

Za a ƙaddamar da cibiyar watsa labaru ta taron wakilan JKS karo na 20 a ranar 12 ga watan Oktoba

Daga CMG HAUSA Za a ƙaddamar da cibiyar watsa labaru ta babban taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta Sin wato JKS karo na 20, a ranar Larabar makon gobe wato 12 ga watan Oktoban nan, tare da karɓar ‘yan jarida a hukumance. An kafa sashen karɓar ‘yan jarida, ta cibiyar, a otel din Nikko New Century dake nan birnin Beijing. Cibiyar watsa labaru ta taron, za ta samar da hidima ga ‘yan jarida daga yankin Hong Kong, da na Macau, da na Taiwan, da kuma na ƙasashen waje, da za su watsa labaru game da taron, a fannonin samar musu takardun…
Read More
FIRS ta gargaɗi hukumomi da ma’aikatun gwamnati kan katsalandan a harkar haraji

FIRS ta gargaɗi hukumomi da ma’aikatun gwamnati kan katsalandan a harkar haraji

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar tattara haraji ta Nijeriya (FIRS) ta gargaɗi hukumomin gwamnati a kan tsoma baki a harkar haraji. Wato ɗora haraji, karɓar harajin da bibiyar waɗanda ba sa biyan harajin. Wannan jawabi dai ya fito daga shugaban zartarwa na hukumar FIRS, Mista Muhammad Nami. Kamar yadda yadda kamfanin dillancin labarai ya rawaito. Mista Nami ya ya yi ƙarin jan kunne ga hukumomi da ma'aikatun a kan yadda suke ɗaukar ma'aikatan da za su dinga karɓar harajin da gwamnatin tarayya take bin kamfanoni da mutane, masana'antu bankuna, da sauran cibiyoyin gudanar da kasuwanci ba bisa tsarin doka ba.…
Read More
Sin tana sa lura ga yanayin da ake Ciki a Burkina Faso

Sin tana sa lura ga yanayin da ake Ciki a Burkina Faso

Daga CMG HAUSA Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Mao Ning, ta ce Sin tana sa lura game da yanayin da ake ciki a ƙasar Burkina Faso bayan da aka yi juyin mulkin soji a ƙasar, kana tana son yin ƙoƙari tare da sassan ƙasa da ƙasa, wajen taimakawa ƙasar kaiwa ga cimma samun zaman lafiya da bunkasuwa. Mao ta bayyana hakan ne a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Asabar. Jami’ar ta kara da cewa, Sin ta lura da yadda Burkina Faso, ta sanar da ci gaban ta, da bin jadawalin wucin gadi da ƙungiyar ECOWAS…
Read More
Ku guji amfani da ‘yan daba don tada tarzoma yayin zaɓe – CP Abubakar Lawal

Ku guji amfani da ‘yan daba don tada tarzoma yayin zaɓe – CP Abubakar Lawal

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano CP Abubakar Lawan ya gana da shugabannin jam'iyyun siyasa da suke zaune a Jihar Kano a kan shirye-shiryen da ake yi na fara yaƙin neman zaven 2023. Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Talata. Ya ce kwamishinan 'yan sandan Jihar Kano CP Abubakar Lawan "ya yi godiya a gare su bisa amsa kiran da suka yi domin tattaunawa a kan gayyatar. Haka zalika ya umarci shugabannin jam'iyyun da su…
Read More