10
Oct
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Malamai ta Nijeriya (NUT) ta yi kira ga gwamnonin jihohin da malaman makaranta ke bi bashi da su yi amfani da ɗan lokacin da ya rage musu a kan karagar mulkin su biyan haƙƙoƙin. Sakatare-Janar na ƙungiyar, Dokta Mike Ike-En ne ya yi wannan kira ranar Talata a Abuja albarkacin zagayowar Ranar Malamai ta Duniya wadda za a yi ranar Laraba. A cewar Ike-Ene, akwai gwamnoni da dama da ba su kammala biyan bashin albashin da malaman firamare da na sakandare ke bi a jihohinsu ba. Don haka ya ce, akwai buƙatar gwamnonin da lamarin…
