11
Oct
Daga WAKILINMU Hukumar Tsaro ta NSCDC ta sanar da kama wani ɗan shekara 20 kan zargin yi wa yarinya mai shekara 13 fyaɗe a Jihar Nasarawa. Kakakin NSCDC reshen jihar, DSC Jerry Victor ya ce, mutumin da ya yi wa yarinyar fyaɗe ya sanya ta samu juna biyu a Lafiya, babban birnin jihar. Haka kuma, NSCDC ta ce, ta kama wasu mutum biyu daban da zargin lalata da wata ’yar shekara 13. Da ya ke gabatar da su a gaban manema labarai, DSC Jerry Victor, ya ce, an kama mutanen ne a wurare daban-daban na jihar. “Waɗanda ake zargi sun…
