11
Oct
Daga BELLO WANG Wasu abokaina ‘yan Najeriya, wadanda suka taba zama a ƙasar Sin, su kan ambaci yadda zaman rayuwa a cikin biranen Sin ya burge su, yayin da muke hira. Sai dai na kan tunatar da su cewa, ba abun mamaki ba ne, ganin irin saurin ci gaba da aka samu a kauyukan ƙasar Sin. Kauyena yana lardin Anhui dake gabashin ƙasar Sin, wani wuri ne dake cikin duwatsu. Yayin da nake ƙarami, ba na son komawa kauyen tare da iyayena, saboda hanyar ba ta da kyau: a kan kwashe sa’o’i 10 a cikin jirgin kasa, sa’an nan a…
