Editor

9513 Posts
An shirya darasin kimiyya na farko daga tashar binciken sararin samaniya ta Sin

An shirya darasin kimiyya na farko daga tashar binciken sararin samaniya ta Sin

Daga CMG HAUSA A yau ne, ƙasar Sin ta watsa darasi na farko game da kimiyya da aka shirya daga ɗakin gwaje-gwaje na Wentian na tashar binciken sararin samaniyar ƙasar Sin. Wannan shi ne aji na farko da 'yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 wato Chen Dong da Liu Yang da Cai Xuzhe suka gabatar, waɗanda aka harba su zuwa tashar binciken sararin samaniyar ƙasar a ranar 5 ga watan Yuni, don gudanar da aiki na tsawon watanni 6, kuma irinsa na 3 da ‘yan sama jannatin na ƙasar Sin suka gabatar daga sararin samaniya. Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa
Read More
Peng Liyuan ta aike da saƙon taya murna ga taron karrama waɗanda suka yi fice a fannin tallafa wa ilimin mata

Peng Liyuan ta aike da saƙon taya murna ga taron karrama waɗanda suka yi fice a fannin tallafa wa ilimin mata

Daga CMG HAUSA Mai ɗakin shugaban ƙasar Sin Peng Liyuan, ta aike da sakon taya murnar bikin karrama waɗanda suka yi fice, a fannin tallafa wa ilimin yara mata da mata na bana, wanda ya gudana a jiya Talata a birnin Paris na ƙasar Faransa, karkashin jagorancin hukumar raya ilimi kimiyya da al’adu ta MƊD UNESCO. Cikin wasiƙar, Peng Liyuan, wadda kuma ita ce jakadiyar musamman ta asusun UNESCO, mai lura da manufar ingiza ilimin yara mata da mata, ta ce alfanun samar da ilimi ga wannan rukuni na al’umma ya wuce batun bunƙasa rayuwar mata kaɗai, duba da cewa,…
Read More
Gamayyar magoya bayan APC ta tsige shugabanta na ƙasa

Gamayyar magoya bayan APC ta tsige shugabanta na ƙasa

Daga BASHIR ISAH Gamayyar ƙungiyoyin magoya bayan Jam'iyyar APC ta tsige shigabanta na ƙasa, Jelil Adewale Adeogun, saboda rashin gansuwa da salon shugabancinsa. Sun cimma matsayar tsige shugaban nasu ne a wajen taron da tsohon sakataren gamayyar, Malam Dattijo Danjuma Miya ya shirya ranar Talata a Abuja. Rashin tafiya da kowa na daga cikin dalilan da suka sanya gammayar tsige Adeogun. Tuni dai gamayyar ta zaɓi Dr. Ahmad Saleh a matsayin sabon shugabanta, Emmanuel Nwosu a matsayin sakatare, sannan Mubarak Mohammed a matsayin mataimakin sakatare. Sauran sun haɗa da Atir Solomon, shugaban shiyyar Arewa, Larai Kolo, ma'aji, Samira Ibrahim, shugabar…
Read More
A daina nuna wariya ga masu nakasa

A daina nuna wariya ga masu nakasa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Aminu (ba asalin sunansa ba ne), wani yaro ne mai kimanin shekaru takwas zuwa goma wanda Allah ya ƙaddarawa samun nakasa ta shanyewar kafafu tun yana ƙarami, wata majiya ta shaida min cewa cutar shan inna ce wato polio ta nakasa shi. Duk da kasancewar ya taso a gaban iyayensa kuma cikin babban gari ba ƙauye ba, amma na lura da yadda iyayensa kan fito da shi ƙofar gida yana bara. Duk lokacin da na fito da safe zan tafi aiki ta nan qofar gidansu nake wucewa. Mai yiwuwa ganin yadda nake kulawa da abubuwansa, ya…
Read More
Buhari ya rantsar da Ariwoola a matsayin alƙalin alƙalan Nijeriya

Buhari ya rantsar da Ariwoola a matsayin alƙalin alƙalan Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin Alƙalin Alƙalan Nijeriya. Shugaban ƙasar ya rantsar da Mai Shari’a Ariwoola a yau Larabar gabanin jagorantar Taron Majalisar Zartarwa a Fadar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja. Naɗin Ariwoola ya biyo bayan ajiye aikin da tsohon Alƙalin Alƙalai, Ibrahim Tanko Muhammad ya yi a watan Yuni, sakamakon rashin lafiya da ya yi ikirarin yana fama da ita. A watan Yuni ne dai Buhari ya rantsar da Ariwoola a matsayin Alƙalin Alƙalan Nijeriya na riƙo, inda ya ci gaba da zama wannan mataki har zuwa…
Read More
Ranar Malamai: Tica uban karatu, cuta ko cutarwa?

Ranar Malamai: Tica uban karatu, cuta ko cutarwa?

Daga AMINA HASSAN ABDUSSALAM Idan na kalli halin da malaman jami'a suke, sai na ga kamar haka malaman Sakandire da firamare suke, sai dai su ba su da murya mai amo irin ta ASUU. Zan fara da yanayin koyo da koyarwa a makarantun ƙasa da na tsakiya. Yaushe rabon da a tura malamai bita don inganta koyo da koyarwa idan ka cire ire-iren bitar da ƙasashen waje ke yi ta hanyar tallafa wa ilimi a Najeriya?Kashi 80% na makarantun babu kayan aiki, kayan aiki ba wai yana nufin kayan record ɗin malami kaɗai ba, ɗaliban ba su da litattafai (textbooks)…
Read More
’Yan bindiga sun yi ajalin kuɓutaccen fasinjan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna a hanyar Zamfara

’Yan bindiga sun yi ajalin kuɓutaccen fasinjan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna a hanyar Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu ’yan bindiga sun kashe ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin ƙasa Abuja zuwa Kaduna da aka sako kwanan nan akan hanyar Funtua zuwa Gusau da ke kan hanyarsa ta komawa mahaifarsa a Jihar Kebbi a ranar Asabar. Wanda aka kashe ɗin wanda ba a bayyana sunansa ba ya shafe sama da watanni shida a hannun ’yan ta’adda bayan harin da aka kai kan hanyar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga Maris, 2022. An kashe sa ne a hanyarsa ta zuwa mahaifarsa a Jihar Kebbi tare da ’yan uwansa waɗanda hukumomi a Jihar Kaduna…
Read More
NAFDAC ta yi gargadin a guji amfani da wasu magungunan tari na yara

NAFDAC ta yi gargadin a guji amfani da wasu magungunan tari na yara

Daga BASHIR ISAH Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NAFDAC), ta yi gargadin a daina sayarwa da kuma amfani da wasu magungunan tari na yara da aka gano suna da illa. Ta ce shagunan magungunan da ke da irin wannan magani su hanzarta tattara su sannan su mika wa ofishin NAFDAC mafi kusa. Shugabar Hukumar, Farfesa Moji Adeyeye ce ta yi wannan gargadi a wajen wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata. Gargadin nata na zuwa ne biyo bayan gano wasu gurbatattun magungunan tari guda hudu da aka yi a kasar Gambiya wanda suka yi…
Read More
Dalilan da suka jawo kiki-kaka tsakanin Gwamnati da ASUU

Dalilan da suka jawo kiki-kaka tsakanin Gwamnati da ASUU

Daga SAIDU AHMAD DUKAWA (Phd) Ga dalilai guda tara (9) daga cikin dadlilan da suka janyo kiki-kaka tsakanin Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU). Zan saka su a sigar mahawara domin sauƙin fahimta ga mai karantawa. Da fatan wannan gudunmawar za ta taimaka wajen lalubo bakin zaren ta yadda za a magance matsalar. Gwamnati: Ba za mu cire ku daga tsarin IPPIS ba, saboda tun daga ranar da muka fara amfani da shi muke samun rarar kuɗi daga abinda muke biya na albashi. ASUU: Ba duka rarar da kuke gani ce ta samu daga toshe kofar zurarewar…
Read More
Yajin Aiki: Rassan ASUU na kaɗa ƙuri’a don ɗaukar matakin ƙarshe

Yajin Aiki: Rassan ASUU na kaɗa ƙuri’a don ɗaukar matakin ƙarshe

Daga BASHIR ISAH A matsayin wani mataki na neman cimma matsaya dangane da yajin aikin Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU), rassan ƙungiyar na kaɗa ƙuri'a a tsakaninsu. Majiya mai ƙarfi daga shugabancin ASUU ta ce, za a kaɗa ƙuri'ar ne tsakanin Talata da Laraba. A cewar majiyar, bayan kaɗa ƙuri'a za a tattara sakamakon a miƙa wa uwar ƙungiya don ɗaukar makin ƙarshe. “Mun samu umarnin haka ne bayan tattaunawar da muka yi da Shugaban Majalisar Wakilai a ranar Litinin. Shugaban Majalisar ya shigo a daidai lokacin da ake da buƙatar haka. "Rassan ƙungiyar za su kaɗa ƙuri'a tsakanin yau (jiya…
Read More