Editor

9513 Posts
Sallamar Kanu aka yi ba wanke shi ba – Malami

Sallamar Kanu aka yi ba wanke shi ba – Malami

Ofishin Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari'a, ya ce sake Nnamdi Kanu da aka yi ba wanke shi aka yi ba an sallame shi ne kawai. Ofishin ya yi wannan ƙarin hasken ne don kawar da sahakku a tsakanin 'yan ƙasa kan hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ɗauka dangane da shari'ar Nnamdi Kanu. Hadimin Ministan Shari'a, Dakta Umar Jibrilu Gwandu ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ran Alhamis. Ya ce, jama'a su sani sallama kawai kotun ta yi wa Kanu amma ba wanke shi ba, domin kuwa shari'a ba ta ƙare ba. Kazalika, ofishin ya ce…
Read More
Kotu ta saki shugaban ’yan ta’adda, Nnamdi Kanu

Kotu ta saki shugaban ’yan ta’adda, Nnamdi Kanu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kotun ɗaukaka Ƙara ta Tarayyar Nijeriya da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin sakin shugaban ƙungiyar nan ta a ’yan ta’adda, wato IPOB, Nnamdi Kanu, ƙungiyar da a baya wata kotu ta tava ayyana a matsayin ta ’yan ta’adda. A ranar Alhamis Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta wanke Nnamdi Kanu daga laifin da Gwamantin Nijeriya ke zargin sa aikatawa na tayar da zauna tsaye da ta’addanci da kuma jagorantar haramtacciyar ƙungiya. Lauyansa, Ifeanyi Ejiofor, ya sanar ta shafinsa na Facebook cewa, “Mun yi nasara, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta wanke ta kuma saki Nnamdi Kani.” A…
Read More
Kwamitin Ƙolin Jam’iyyar JKS ya kira taron waɗanda ba ‘yan jam’iyyar ba

Kwamitin Ƙolin Jam’iyyar JKS ya kira taron waɗanda ba ‘yan jam’iyyar ba

Daga CMG HAUSA Kwanan nan kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin, ya kira wani taro na mutanen da ba ‘yan jam’iyyar ba ne a birnin Beijing, inda aka saurari ra’ayoyi, da shawarwari daga wajensu, kan daftarin tattaro ra’ayoyi, na rahoton babban taro karo na 20 na jam’iyyar. Babban sakataren kwamitin ƙolin jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin, Xi Jinping ne ya jagoranci taron, inda ya gabatar da wani muhimmin jawabi dake jaddada cewa, a sabon zamanin da muke ciki, kuma bisa sabbin buƙatu, ya dace jam’iyyar kwaminis da sauran wasu jam’iyyun ƙasar su ƙara haɗin-kai, don haɓaka nuna kishin ƙasa,…
Read More
Sin ta harba sabon tauraron ɗan Adam na nazarin yanayi

Sin ta harba sabon tauraron ɗan Adam na nazarin yanayi

Daga CMG HAUSA Da sanyin safiyar Alhamis din nan ne ƙasar Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam na aikin lura da yanayi, da ayyukan rage aukuwar bala’u, da aiwatar da matakan gaggawa masu nasaba da yanayi da dai sauransu. An harba sabon tauraron samfurin S-SAR01 ne daga cibiyar harba kumbuna ta Taiyuan, wadda ke lardin Shanxi na arewacin ƙasar da karfe 7 saura mintuna 7 na safe, ta amfani da rokar Long March-2C. Tuni kuma tauraron ya shiga falakin sa kamar yadda aka tsara. Kaza lika sassan da za su yi amfani da ingantattun hotuna da bayanan da…
Read More
Tsarin gwamnatin Sin na ba da jiyya ga dukkanin mazauna ƙauyuka

Tsarin gwamnatin Sin na ba da jiyya ga dukkanin mazauna ƙauyuka

Daga MINA Abokai, ko akwai wahalar samun jiyya a wuraren dake da nisa daga birane a wurin ku? Tun bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin, kullum gwamnatin ƙasar na ƙoƙarin daidaita wannan matsala. Yau ma “Duniya a zanen MINA” na bayyana muku tsarin gwamnatin Sin na ba da jiyya ga dukkanin ƙauyuka. Saurayin dake cikin zanen sunansa Marghulam Abdukrem, ya karanta ilmin likitanci a kyauta bisa tallafin gwamnati a fannin ilmin likitanci a watan Yuli, kuma bayan da ya kammala karatun, an tura shi zuwa ƙauyen Kokbash dake garin Baishtugman, na birnin Aksu dake jihar Xinjiang, a matsayin likitan wurin.…
Read More
Gwamna Wike ya naɗa ƙarin hadimai 28,000

Gwamna Wike ya naɗa ƙarin hadimai 28,000

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya naɗa ƙarin hadimai na musamman har mutum 28,000 gabanin zaɓen 2023. Naɗin na zuwa ne kwana ɗaya bayan da Gwamnan ya naɗa masu ba shi shawara na musmaman su 14,000 da wasu ma'aikatansa 319 a unguwanni da kuma 40 a yankunan ƙananan hukumomin faɗin jihar. Hadimi na musamman ga Gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Kelvin Ebiri, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce naɗin sabbin hadiman ya fara aiki nan take. Da alama dai Gwamna Wike ya yi waɗannan naɗe-naɗen ne domin…
Read More
Martin Cooper: Wanda fara ƙirƙiro Wayar-salula

Martin Cooper: Wanda fara ƙirƙiro Wayar-salula

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babu shakka batun wayar salula abu ne da ya dabaibaye Duniya a halin yanzu. Da dai kafin zuwan wayar Salula, Mutane suna rayuwarsu ne hankalinsu a kwance, amma yanzu da wayar Salula ta zama ruwan-dare game Duniya, babu wanda ya ke so ya rayu ba tare da ita ba. To shin zargi zamu yi ko kuma godiya ga wanda ya ƙirƙiro mana da wannan abu, wanda ya ke cinye wa mutane kuɗi? To imma dai zargin ne ko kuma yabon, to wanda za a zarga ko kuma a yaba shine Dakta Martin Cooper. Shi dai Dr.…
Read More
Marubuci na iya saka rigar kowa ta zauna daram a jikinsa – Hassana Matazu

Marubuci na iya saka rigar kowa ta zauna daram a jikinsa – Hassana Matazu

"Haɗakar marubuta za ta ɗaga darajar adabi" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Gamayyar wasu haziƙan marubutan adabi su goma da suka ƙulla ƙawancen aikin rubuta wani littafi mai suna 'Da Jininsa A Jikina' na ci gaba da samun nasara a aikin da suka sa a gaba, na kafa tarihi da farfaɗo da kasuwar littattafan adabin Hausa. A yayin da aiki ke tafiya cikin salon jan hankali da nuna ƙwarewa ta ma'abota fasaha da sarrafa harshe, marubutan da ke aikin na sa ran nan da ƙarshen wannan shekara bugaggen littafin zai shiga hannun masu karatu. Ɗaya daga cikin marubutan wannan tauraron littafi…
Read More
Aikin jarida ya ba ni damar faɗakar da jama’a – Halima Ben Umar

Aikin jarida ya ba ni damar faɗakar da jama’a – Halima Ben Umar

“Shirin 'Mata A Yau' ya canza rayuwar iyalai da dama” Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Sunan Hajiya Halima Ben Umar ba ɓoyayye ba ne a gidaje da dama na Nijeriya da maƙotan ƙasashe, musamman inda ake amfani da harshen Hausa, saboda rawar da ta ke takawa wajen gabatar da shirin ‘Mata A Yau’, wanda tashar talabijin na Arewa 24 ke gabatarwa. Tsohuwar ’yar jarida, ýar gwagwarmaya, kuma uwa, wacce gudunmawarta a harkokin cigaban al'umma ya ratsa birane da ƙauyuka, kuma har yanzu ta ke nuna kishi da jajircewa wajen faɗakar da ýaýa mata muhimmancin inganta rayuwarsu da ta iyalinsu. Wakilin Blueprint…
Read More
Asusun CFRD na ƙasar Sin ya amsa sunansa

Asusun CFRD na ƙasar Sin ya amsa sunansa

Daga IBRAHIM YAYA Galibi ana kafa asusu ne da nufin inganta fannoni na ilimi ko harkokin ci gaban mata da ƙananan yara ko raya harkar lafiya da agazawa waɗanda bala’o’i suka shafa da makamantansu. Kamar sauran irin waɗannan asusu da kasashe ko al’ummomi ko ƙungiyoyi masu zaman kansu ke kafawa, shi ma asusun raya yankunan karkara na ƙasar Sin ko CFRD a takaice, ya amsa manufofin kafa shi, duba da irin managartan ayyukan da yake gudanarwa a ciki da wajen ƙasar. Ayyuka na baya-bayan da asusun ya gudanar a ƙasar Habasha, ya samu yabo da jinjina, a daidai lokacin da…
Read More