Editor

9513 Posts
ASUU ta umarci malamai su koma bakin aiki ba tare da ɓata lokaci ba

ASUU ta umarci malamai su koma bakin aiki ba tare da ɓata lokaci ba

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) ta janye yajin aikin da take yi a hukumance tare da bai wa mambobinta umarnin su koma bakin aiki ba tare da wani jinkiri ba. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da shugaban ASUU na ƙasa, Emmanuel Osodeke ya fitar a ranar Alhamis bayan kammala taronsu a Abuja. Shugabannin ƙungiyar sun gudanar sa taron nasu ne domin sanin mataki na gaba da ya kamata su ɗauka biyo bayan umarnin da kotu ta ba su a makon jiya na su koma bakin aiki. ASUU ta shafe wata takwas tun bayan da ta soma…
Read More
Jakadan Sin a Nijeriya ya halarci dandalin Abuja na 2022

Jakadan Sin a Nijeriya ya halarci dandalin Abuja na 2022

Daga CMG HAUSA Jakadan ƙasar Sin a Tarayyar Najeriya Cui Jianchun, ya bayyana cewa, hulɗar da ke tsakanin Sin da Najeriya na ta bunƙasa a shekarun baya-bayan nan, kuma sassan 2 na ƙara inganta amincewar juna ta fuskar siyasa, kana haɗin gwiwarsu ta fuskar tattalin arziki, ya haifarwa jama’ar su alherai. Baya ga haka kuma, ƙasashen 2 sun riƙa kyautata taimakawa juna ta fuskar tsaro tsakanin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, tare da yin mu’amalar al’adu a tsakaninsu. Ya ce ƙasar Sin na son ci gaba da aiwatar da manyan tsare-tsaren ci gaba da bunƙasa na 5GIST tsakaninta da Najeriya, bisa…
Read More
Shugaban Rwanda na fatan ci gaba da bunƙasa alaƙar da ke tsakanin Rwanda da Sin

Shugaban Rwanda na fatan ci gaba da bunƙasa alaƙar da ke tsakanin Rwanda da Sin

Daga CMG HAUSA A kwanakin baya ne, shugaban ƙasar Rwanda Paul Kagami, ya bayyana yayin wata zantawa ta musamman da wakilin CMG cewa, yayin da ake inganta shirin raya ƙasar Rwanda na tsawon shekaru 20 daga shekarar 2000 zuwa 2020, ƙasar Sin ta taimaka matuƙa a fannonin zamanintar da abubuwan more rayuwa, da kiwon lafiya da ilimi da sauransu. Muna godiya matuka ga ƙasar Sin. Ƙasar Rwanda za ta kara mayar da hankali wajen samar da ci gaba mai ɗorewa nan da shekaru 30 dake tafe, muna kuma fatan za mu ci gaba da haɗin kai a wannan fanni. Ya…
Read More
Ƙasashe 143 sun kaɗa ƙuri’ar yin tir da mamayar Rasha a Ukraine

Ƙasashe 143 sun kaɗa ƙuri’ar yin tir da mamayar Rasha a Ukraine

Majalisar Ɗinkin Duniya ta kaɗa ƙuri’ar yin tir da Rasha kan mamaye wasu sassan Ukraine da ta yi, matakin da shugaban Amurka Joe Biden ya ce saƙo ne mai ƙarfi ga takwaransa Vladmir Putin. Ƙasashe 143 ne suka goyi bayan ƙudurin na yin tir da Rasha a zauren Majalisar Ɗinkin Duniyar, inda 5 suka hau kujerar na ƙi, sauran ƙasashe 35 kuma suka ƙauracewa zaman, wadanda suka haɗa da Chana, Indiya, Afirka ta Kudu da kuma Pakistan, duk da matsin lambar da Amurka ta riƙa musu kan su yi tir da Rashan. Ƙudurin dai ya yi tir da matakin Rasha,…
Read More
Likitocin ƙasar Sin sun gudanar da bita ga takwarorinsu na Saliyo game da yaƙi da cutar Malaria

Likitocin ƙasar Sin sun gudanar da bita ga takwarorinsu na Saliyo game da yaƙi da cutar Malaria

Daga CMG HAUSA Likitocin ƙasar Sin dake aiki a Saliyo, sun gabatar da bita ta musamman game da matakan kandagarki, da magance cutar zazzabin cizon sauro ko malaria ga likitocin ƙasar. Yayin bitar ta jiya Alhamis, wadda aka gudanar a asibitin sada zumunta na Sin da Saliyo, jagoran tawagar likitocin na Sin Zhan Xinjie, wanda kwararre ne a fannin gwaje gwajen cututtuka, ya gabatar da maƙala game da cutar ta Malaria, da nau’o’in sauro dake baza ta a sassan duniya daban daban, inda kuma ya yi fashin baƙi game da dabarun gano cutar da ake amfani da su a ɗakunan…
Read More
‘Yan sandan Jihar Kano sun yi ram da matashin da ya hallaka abokinsa

‘Yan sandan Jihar Kano sun yi ram da matashin da ya hallaka abokinsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani matashi mai suna Ibrahim Khalil da ke Unguwar Ƙofar Mazugal cikin Ƙaramar Hukumar Dala a birnin Kano. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan yayin zantawarsa da manema labarai a Talatar da ta gabata a Kano. SP Kiyawa ya ce, lamarin ya faru ne sakamakon samun wani rashin jituwa tsakanin marigayin da wani mai suna Salisu Bala ɗan kimanin shekaru 18. Wanda ya bugi Ibrahim har ya kai ga ya rasa ransa kamar yadda SP Abdullahi Haruna kiyawa…
Read More
Salah ya kafa tarihin zura ƙwallaye uku cikin sauri a gasar Zakarun Turai

Salah ya kafa tarihin zura ƙwallaye uku cikin sauri a gasar Zakarun Turai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Liverpool Mohamed Salah ya kafa tarihin shiga sahun waɗanda suka yi nasarar cin ƙwallaye 3 a wasa guda cikin sauri a gasar kofin zakarun Turai, bayan da ya zura ƙwallayen 3 wato 'hattrick' cikin mintuna 6 da shiga fili a karawarsu da Rangers daren Laraba. Ƙwallayen na Salah dai ya goge tarihin Bafetimbo Gomis na Lyon wanda ya taɓa nasarar zuwa ƙwallaye 3 cikin mintuna 8 yayin wasansu da Dinamo Zagreb a 2011 ƙarƙashin makamanciyar gasar Yayin wasan na daren Laraba da ya gudana a Ibrox Liverpool ta tashi wasa 7…
Read More
Jami’an KAROTA sun cafke direban Adaidaita Sahu ɗan damfara a Kano

Jami’an KAROTA sun cafke direban Adaidaita Sahu ɗan damfara a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano KAROTA, ta ce ta cafke wani magidanci ɗan damfara bayan ya damfari wata kuɗi har Naira 600.000 Hakan na ƙunshe ne ta wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Malam Nabulusi Abubakar Ƙofar Na’isa ya fitar a daren Talata da ta gabata. Sanarwar ta ce, jami’an hukumar ta KAROTA, sun sami nasarar kama magidancin ne mai suna John Bandes a kan titin Obasanjo da ke cikin birnin Kano. “A makon da ya gabata ne wata budurwa mai suna Jenifer Paul ta shigar da ƙorafi a…
Read More
NIMET da NIHSA sun yi gargaɗin fuskantar ƙarin ambaliyar ruwa a sassan Nijeriya

NIMET da NIHSA sun yi gargaɗin fuskantar ƙarin ambaliyar ruwa a sassan Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya NIMET da takwararta ta NIHSA da ke hasashen zubar ruwan sama, sun yi gargaɗi kan yiwuwar fuskantar matsananciyar ambaliyar ruwa a jihohin shiyyar Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Yammacin qasar nan da kwanaki ƙalilan masu zuwa. Darakta Janar na hukumar NIMET, Farfesa Mansur Bako Matazu ya ce hasashensu ya nuna yiwuwar samun mamakon ruwan sama a yankunan 2 wanda zai zama ƙari kan ɓallewar wasu madatsun ruwan ƙasar, lamarin da zai haifar da gagarumar ambaliya. Hasashen hukumomin biyu na zuwa ne a daidai lokacin da jihohin Benuwai…
Read More
ASUU ta janye yajin aiki

ASUU ta janye yajin aiki

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) ta janye yajin aikinta don bai wa mambobinta damar komawa bakin aiki. Duk da dai kungiyar ba ta ba da sanarwar hakan a hukumance ba, amma jaridar Punch ta tattaro cewar an cimma matsayar janye yajin aikin ne bayan tattaunawar da shugabannin ƙungiyar na ƙasa suka yi a Abuja. Majiyar Punch ta tabbatar cewa, 'Lallai an janye yakin aikin." Sai dai majiyar ta ce a saurari shigaban ASUU na ƙasa domin ƙarin bayani da safiyar Juma'a. Da alama dai ƙungiyar ta janye yajin aikin ne domin biyayya ga umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara inda…
Read More