Girman kan Amurka ya sake fuskantar koma baya

Daga CMG HAUSA

Da yake mai da hankali kan shawarar “OPEC+” ta rage yawan ɗanyen man da ake hakowa a kowace rana da ganga miliyan 2 daga watan Nuwamba, ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a a Amurka ta kara nuna fushin ‘yan ƙasar a ‘yan kwanakin nan.

Da farko dai gwamnatin Biden ta yi fatan manyan ƙasashen da ke hako mai a yankin Gabas ta Tsakiya, za su ƙara yawan man da suke haƙowa don magance tashin farashin mai da kuma taimakawa Amurka wajen shawo kan matsalar hauhawar farashin kayayyakin da take fuskanta, amma abin ya ci tura.

Jaridar “Capitol Hill” ta yi sharhi cewa, shawarar “OPEC+” ta raunata manufar Biden game da harkokin ƙasashen waje.

Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa