Editor

9513 Posts
Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta Ƙasa ta rufe makarantu 46 a Jihar Bauchi

Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta Ƙasa ta rufe makarantu 46 a Jihar Bauchi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta Ƙasa ta rufe makarantun koyarwa da cibiyoyin karatu masu samar da takardun shaidar karatu na NCE guda 46 dake koyarwa a faɗin Jihar Bauchi. Wannan rufewa ya biyo bayan wata wasiƙa ta ranar Laraba, 5 ga watan Satumba da hukumar ta aika wa kwamishinan Ilimi na jihar, Dokta Aliyu Usman Tilde, tana mai cewar, dukkan makarantun da rufewar ta shafa an basu wa’adin kwanaki talatin ne na bin umarni ko su fuskanci fushin doka. Wasiƙar, wacce babban sakataren hukumar Farfesa Paulinus Chijioke Okwelle ya sanya hannu, ta yi tuni…
Read More
Jega ya zargi Ngige da taɓarɓara yajin aikin ASUU

Jega ya zargi Ngige da taɓarɓara yajin aikin ASUU

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya zargi Ministan Kwadago Chris Ngige da taɓarɓarewar tattaunawa tsakanin malaman da ke yajin aiki da gwamnatin tarayya. Jega, wanda kuma tsohon shugaban ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ne ya yi wannan zargin yayin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Arise, a ranar Talata, 5 ga Oktoba, 2022. A cewarsa, Ministan ne ke da alhakin yajin aikin da aka kwashe watanni bakwai ana yi, bayan da ya mayar da lamarin ya zama na ƙashin kai. "Ministan Kwadago ba ya taimakawa al'amura,…
Read More
PDP ta karɓi mutane fiye da 25,000 daga wasu jam’iyyu a Bauchi

PDP ta karɓi mutane fiye da 25,000 daga wasu jam’iyyu a Bauchi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Ɗan takarar neman shugabancin tarayyar Nijeriya a ƙarƙashin tutar Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewar, jam’iyyar su ita ce mafi tsufa, mafi girma, kuma mafi ɗauke da yawan jama’a da za ta sake karɓan jagorancin ƙasar nan a zaɓen gamagari na watan Fabrairun shekarar baɗi, 2023. Gwarzon na Jam’iyyar PDP ya yi waɗannan kalamai ne ranar Laraba a filin wasan ƙwallo na tunawa da Marigayi Abubakar Tafawa Balewa yayin da yake karɓan mutane fiye da 25,000 waɗanda suka canja sheƙa daga wasu jam’iyyu zuwa jam’iyyar su, inda yake cewa Jam’iyyar PDP babu inda ba…
Read More
Kwamitin PCRC ya ba hukumar ‘yan sandan Kano mota don tabbatar da tsaro

Kwamitin PCRC ya ba hukumar ‘yan sandan Kano mota don tabbatar da tsaro

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano, Abubakar Lawal ya fara gudanar da ziyara domin karɓar ƙorafe-ƙorafen da jama'ar yankunan suke da shi akan harkar tsaro tare da karɓar koken nasu don magance shi cikin gaggawa. Daura wanda ya fara da shiyyar Area Command ta Metro ta hannun shugabancin kwamitin aikin tsaro da al'umma (PCRC) yayin da su ka bayar da wata mota domin tallafawa jami'an 'yan sandan wajen gudanar da ayyukan su tare da da kare rayuka da dukiyoyin jama'a. Shi ma a nasa jawabin shugaban kwamitin aikin tsaro da al'umma Alhaji Ahmad Sufi ya…
Read More
Kotu ta amince da buƙatar ASUU bisa sharaɗin malamai su koma aiki

Kotu ta amince da buƙatar ASUU bisa sharaɗin malamai su koma aiki

Daga BASHIR ISAH Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta a Abuja, ta umarci malaman jami'o'i ƙarƙarshin ƙungiyarsu ta ASUU, da su koma bakin aiki ba tare da ɓata lokaci ba. Kotun ta ba da umarnin ne bayan da ASUU ta shigar da ƙara tana neman izinin ɗaukaka ƙara kan umarnin da Kotun Ma'aitaka ta ba ta na ta janye yaijin aikin da take yi sannan malamai su koma bakin aiki. Kotun ta amince da buƙatar ASUU bisa sharaɗin ta yi wa Kotun Ma'aikata biyayya wajen kiyaye umarnin da ta ba ta kan ta janye yajin aikin nata. Daga nan, Kotun Ɗaukaka…
Read More
Kyautata zaton da al’umma ke yi min ya sa na fito takara a PRP – Hon. Ibrahim Garba

Kyautata zaton da al’umma ke yi min ya sa na fito takara a PRP – Hon. Ibrahim Garba

BABANGIDA S GORA a Kano Ɗan takarar kujerar majalisar tarayya a ƙaramar hukumar Birni dake Jihar Kano ƙarƙashin inuwar Jam'iyyar PRP, Hon. Ibrahim Garba, ya ce babu abinda ya ja hankalinsa kamar yadda jama'a suke kiraye-kiraye gare shi da ya tsaya ma su takara don ceto al'ummar daga hannun 'yan sari. Hon. Ibrahim Garba ya bayyana haka ne a wata zantawa da manema labarai a Kano makonni biyu da suka gabata yayin da yake ma magoya bayan sa babban albishir na irin ƙudurinsa idan ya samu dama a zaɓen 2023 mai ƙaratowa. Ibrahim ya qara danganta alaƙar Jam'iyyar PRP da…
Read More
Ba za mu sake rattaɓa hannu da ASUU kan yarjejeniyar da ba za ta aikatu ba – Buhari

Ba za mu sake rattaɓa hannu da ASUU kan yarjejeniyar da ba za ta aikatu ba – Buhari

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce, ba za su sake rattaɓa hannu da Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) kan yarjejeniyar da ba za ta haifar da ɗa mai ido ba. Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne sa'ilin da yake gabatar da kasafin 2023 ga Majalisar Tarayya a ranar Juma'ar da ta gabata a Abuja. Da yake jawabi, Buhari ya ce an ware wa malaman jami'a kaso mai tsoka daga kasafin da ya kai sama da biliyan N450 domin cim ma buƙatunsu. Shugaban ya ce gwamnati na sa ran malaman jami'o'i su fahimci halin da ƙasa ke ciki a…
Read More
Daftarin da ya shafi Jihar Xinjiang na da nufin daƙile ci gaban ƙasar Sin

Daftarin da ya shafi Jihar Xinjiang na da nufin daƙile ci gaban ƙasar Sin

Daga CMG HAUSA Majalisar kare haƙƙin bil Adama ta MƊD, ta yi watsi da wani daftari da ya shafi jihar Xinjiang, wanda wakilin Sin ya bayyana a matsayin wani yunƙuri na amfani da hukumomin kare haƙƙin ɗan Adam, domin tsoma bakin cikin harkokin cikin gidan Sin, da amfani da batutuwan da suka shafin Xinjiang domin daƙile ci gaban ƙasar. Chen Xu, shugaban tawagar ƙasar Sin a ofishin MƊD dake Geneva ne ya bayyana haka, inda ya ce Amurka da wasu ƙasashe ne suka shirya tare da gabatar da daftarin, suka kuma miƙa shi a matsayin matsalar dake buƙatar gyara, a…
Read More
Sin ta yi kira da a taimaka wa gwamnatocin ƙasashen Afirka wajen inganta ƙarfinsu na amfani da albarkatun halittu

Sin ta yi kira da a taimaka wa gwamnatocin ƙasashen Afirka wajen inganta ƙarfinsu na amfani da albarkatun halittu

Daga CMG HAUSA Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MƊD Dai Bing ya bayyana cewa, ana samun albarkatun halittu masu yawa a nahiyar Afirka, kuma akwai kyakkyawar makoma a wannan fanni, sai dai ya kamata ƙasa da ƙasa su taimakawa gwamnatocin ƙasashen Afirka, wajen inganta ƙarfinsu na amfani da albarkatun halittu, da kuma sa ƙaimi ga kafa tsarin darajar albarkatun duniya bisa adalci. Dai Bing ya bayyana hakan ne a jiya, a gun muhawara na kwamitin sulhu na MƊD kan batun yaƙi da ƙungiyoyin ɓata gari da ‘yan ta’adda, waɗanda suke tattara kuɗi ta hanyar fasa ƙaurin albarkatun halittu. A cewarsa,…
Read More
Ƙasar Sin ta miƙa ɗakin adana magunguna na zamani ga Zimbabwe

Ƙasar Sin ta miƙa ɗakin adana magunguna na zamani ga Zimbabwe

Daga CMG HAUSA Ƙasar Sin ta miƙa wani ɗakin adana magunguna na zamani da darajarta ta kai miliyoyin daloli ga gwamnatin ƙasar Zimbabwe, domin bunƙasa ƙarfin ƙasar na adana magunguna da inganta tsarin bayar da kiwon lafiya. Dakin adana magungunan, wanda ƙasar Sin ta gina tare da samar da kuɗin aikin, ya laƙume dalar Amurka miliyan 22, kuma an yi masa mazauni ne a asibitin Sally Mugabe dake birnin Harare, wanda shi ne asibiti mafi girma na biyu a ƙasar. Da yake jawabi yayin bikin ƙaddamarwar da mika ɗakin, shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya yabawa ƙasar Sin bisa taimakon da…
Read More