Editor

9513 Posts
NDLEA ta kama ƙasurgumin mai safarar ƙwayar Tiramol a Nijeriya

NDLEA ta kama ƙasurgumin mai safarar ƙwayar Tiramol a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar NDLEA ta kama ƙasurgumin ɗan harƙalla kuma mai safarar ƙwayar Tiramol a Nijeriya. Kakakin hukumar Femi Babafemi ya bayyana a wata sanarwar cewa hukumar ta kama Ugochukwu Chukwukadibia shugaban kamfanin motocin na Autonation Motors Ltd, da rumbun damin ƙwayar tiramol da kuɗin sa ya kai Naira biliyan 8.8. ”An kama ƙwayoyin tiramol sama da miliyan 13 danƙare a gidan Ugochukwu, wani ƙasurgumin attajiri da ke zama a Lekki, Jihar Legas, da kuɗin su suka kai Naira biliya. 8.8. Wannan kamu da EFCC suka yi ya zo kwanaki kaɗan bayan hukumar ta cafke wani…
Read More
Yau kotu za ta yanke hukunci kan ƙarar da ASUU ta ɗaukaka

Yau kotu za ta yanke hukunci kan ƙarar da ASUU ta ɗaukaka

Daga WAKILINMU Wannan Juma'ar ake sa ran Kotun Daukaka Kara za ta yanke hukuncin kan buƙatar da Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) na jingine umarnin da Kotun Ma'aikata ta ba ta na ta janye yajin aikin da take yi. Ganin ba ta gamsu da umarnin da Kotun Ma'aikatan ta bayar kan malaman jami'o'i su koma bakin aiki ba, ya sanya ASUU garzayawa Kotun Ɗaukaka Ƙara don ci gaba da neman buƙatunta a wajen gwamnati. Lauyan ASUU, Femi Falana (SAN), ya ce daidai ne ɗaukaka kara da ƙungiyar ta yi kan umarnin kotun, saboda a cewarsa, umarnin ya saba mata. Falana ya…
Read More
Maulidi: Gwamnati ta ayyana Litinin mai zuwa ranar hutu

Maulidi: Gwamnati ta ayyana Litinin mai zuwa ranar hutu

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin mai zuwa a matsayin ranar hutun gamari domin bikin Maulidin Annabi Muhammad (SAW) na bana. Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan, inda ya yi amfani da wannan dama wajen taya al'ummar Musulmi na gida da waje murnar zagayowar wannan rana. Rana 12 ga watan Rabi'ul Awwal al'ummar Musulmi kan yi bikin mauldi, wanda a bana ranar ta faɗa a Asabar wanda hakan ya sa gwamnatin ayyana Litinin mai zuwa ranar hutu. Daga nan, Aregbesola ya yi kira ga 'yan Nijeriya da su yi amfani da wannan…
Read More
Mutum 450 sun samu horon koyon sana’o’in hannu a cikin shirin Sanatan Kebbi ta Arewa

Mutum 450 sun samu horon koyon sana’o’in hannu a cikin shirin Sanatan Kebbi ta Arewa

Daga JAMIL GULMA a Kebbi A cikin shirinsa na yaƙi da zaman banza, Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa ya horar da matasa maza da mata 450 sana'o'in hannu da suka haɗa da yadda a ke yin takalmi da bel da kuma alabai (wallet) a ƙananan hukumomin Argungu da Augie da kuma Arewa. Da yake jawabi wajen bikin yaye waɗannan matasan a garin Argungu a madadin Sanata Dokta Yahaya, Alhaji Sama'ila Dantagago ya ce dalilan da suka sanya Sanata ɗaukar wannan matakin shi ne saboda rage zaman banza da dogara ga gwamnati wanda idan mutum…
Read More
Nnamdi Kanu ya rubuta wa Buhari wasiƙa

Nnamdi Kanu ya rubuta wa Buhari wasiƙa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jagoran Ƙungiyar 'Yan a-ware ta IPOB da ke tsare, Nnamdi Kanu, ya aika takardar ƙorafi ga Shugaba Muhammadu Buhari inda ya nemi gwamnati ta sake shi cikin gaggawa. Gwamnatin Nijeriya na tuhumarsa da laifuka guda 11, ciki har da cin amanar ƙasa da ta'addanci, da mallakar haramtattun makamai, da kuma ƙoƙarin tunzura jama'a don haifar da yamutsi. A cikin wasiƙar wadda rukunin lauyoyinsa ƙarƙashin jagorancin Mike Ozekhome mai lambar SAN suka fitar, Nnamdi Kanu ya buƙaci Shugaba Buhari ya bada umarnin sakin sa daga hannun hukumar tsaron farin kaya ta DSS don bin wata…
Read More
An kama mai shekara 40 da ya yi wa ‘yar shekara uku fyaɗe har ta mutu a Kano

An kama mai shekara 40 da ya yi wa ‘yar shekara uku fyaɗe har ta mutu a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jami'an tsaro sun kama wani dattijo mai shekara 40 da ake kira Baba Idi sakamakon zargin da ake yi masa na yi wa wata ƙaramar yarinya mai shekara uku fyaɗe, abin da ya yi sanadin rasuwarta a Kano. Kamar yadda wani ɗan'uwan marigayiyar ya bayyana, Yasmin ta rasu ne ranar Alhamis 29/09/2022 da ƙarfe 4 na yamma a dalilin fyaɗen da aka yi mata ranar Talata. Wanda ake zargin ya yi fyaɗen, Baba Idi, yana zaune ne a Lungun Alhaji Halliru a unguwar Gama, Ƙaramar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano. Rahotanni sun tabbatar da…
Read More
Abin tausayi irin na George Floyd da ya riƙa wakana a Amurka abin kunya ne gare ta

Abin tausayi irin na George Floyd da ya riƙa wakana a Amurka abin kunya ne gare ta

Daga CMG HAUSA Kwanan baya, wakilin ƙasar Sin ya bayyana matuƙar damuwa a yayin taron majalisar kare haƙƙin ɗan Adam ta MƊD karo na 51 dangane da yadda hukumomi masu ruwa da tsaki na ƙasar Amurka da wasu ƙasashe suke nuna wa ‘yan ƙananan ƙabilun bambanci yayin da suke aiwatar da doka, ya kuma buƙace su da kalli kansu yadda ya kamata dangane da mummunar matsalar wariyar launin fata da nuna bambanci tsakanin ƙabilu, su aiwatar da sanarwa da tsarin ayyuka na Durban, a ƙoƙarin kauce wa sake abkuwar abin tausayi da ya wakana kan George Floyd. Shekara guda bayan…
Read More
Firaministan Habasha ya ƙaddamar da ɗakin adana kayan kimiyya da fasaha da ƙasar Sin ta samar

Firaministan Habasha ya ƙaddamar da ɗakin adana kayan kimiyya da fasaha da ƙasar Sin ta samar

Daga CMG HAUSA Firaministan ƙasar Habasha Abiy Ahmed, ya ƙaddamar da wani katafaren gidan adana kayan kimiyya da fasaha da ƙasar Sin ta samar, a Addis Ababa, babban birnin ƙasar. Gidan adana kayan kimiyya da fasaha na Afirka mai shiffar Kubba, ya zama wani dandali da za a iya tunani a kuma ƙirƙiro sabbin fasahohi na kimiyya, don tallafawa ci gaban ƙasar Habasha. Yana mai cewa, gidan zai taka muhimmiyar rawa wajen canja ƙasar Habasha zuwa tsarin tattalin arziki na zamani. A wani ɓangare na bikin ƙaddamar da gidan, ƙasar dake gabashin Afirka, ta kuma karɓi bakuncin taron kwaikwayon tunanin…
Read More
Ƙoƙarin Sin na neman samun jituwa tsakanin ɗan Adam da muhallin duniya

Ƙoƙarin Sin na neman samun jituwa tsakanin ɗan Adam da muhallin duniya

Daga BELLO WANG Kogin Yangtse, wani kogi ne na ƙasar Sin, wanda tsawonsa ya kai fiye da kilomita 6300, ko kuma mu ce kogi ne mafi tsawo na 3 a duniya. An taba samun mutane fiye da dubu 200, da suke gudanar da aikin kamun kifi a kogin Yangtse. Amma sannu a hankali, kifayen da ke cikin kogin ya ragu, sakamakon yawan sun kifi fiye da kima, da shigar da gurbataccen ruwa cikin kogin, lamarin da ya sanya masunta cikin wani yanayi na kunci. Sai dai daga bisani, an fara aiwatar da wata doka ta tsawon shekaru 10, ta hana…
Read More