05
Oct
Daga CMG HAUSA Sashen dake lura da mahakar mai ta Daqing, dake ƙarƙashin babban kamfanin albarkatun man fetur na ƙasar Sin, ya ce kawo yanzu, mahakar ɗanyen mai ta Daqing, ta samar da jimillar ɗanyen mai da yawan sa ya kai sama da tan biliyan 2.4, tun fara aikin ta a shekarar 1959. Mahakar man dai na kan gaba, wajen samar da albarkatun mai a ƙasar Sin, ta kuma samar da kaso 40 bisa ɗari, na ɗaukacin albarkatun man da ake hakowa a ƙasar Sin a tsawon wannan lokaci. Cikin shekaru sama da 60, mahakar Daqing ta gudanar da aiki…
