Editor

9513 Posts
A na ci gaba da ɗaukar shirin ‘Zo Mu Zauna’ Zango na uku

A na ci gaba da ɗaukar shirin ‘Zo Mu Zauna’ Zango na uku

DAGA MUKHTAR YAKUBU A yanzu haka dai an ci gaba da ɗaukar shirin fim ɗin 'Zo Mu Zauna' mai dogon zango wanda a ke shaska shi a tashar Rarara da ke Kan YouTube wanda fitaccen marubucin labarai, kuma Furodusa Naziru Alkanawy yake ɗaukar nauyin shirya shi. Ko da yake tun bayan kammala zango na biyu mutane da suke bibiyar shafin na YouTube na Rariya domin kallon fim ɗin suke ta tambaya a rashin ganin fim ɗin, wanda hakan ya sa a ke tambayar ko dai fim ɗin an jingine shi ya tafi hutun dole? A yanzu dai an ci gaba…
Read More
Yajin aikin ASUU: Jami’o’i masu zaman kansu a Nijeriya suna ta samun ƙarin ɗalibai

Yajin aikin ASUU: Jami’o’i masu zaman kansu a Nijeriya suna ta samun ƙarin ɗalibai

Daga AMINA YUSUF ALI A halin yanzu dai jami'o'i masu zaman kansu a Nijeriya sun ƙara tumbatsa sakamakon ɗalibai da suke rigegeniyar shiga sakamakon rufe jami'o'in gwamnati da aka yi sanadiyyar yajin aikin ASUU. Idan za a iya tunawa, tun 14 ga watan Fabrairu, 2022 ne aka tsayar da duk wata hada-hada ta koyarwa ko koyo a jami'o'in Nijeriya mallakar gwamnati saboda yajin aikin da ƙungiyar Malamai da ma'aikatan jami'o'i (ASUU) suka tsunduma. Ƙungiyar tana neman kuɗaɗen inganta jami'o'in ne daga wajen gwamnati na yarjejeniyar 2009 FGN/ASUU da alawus-alawus na malaman da ya maƙale da kuma tabbatar da adalci a…
Read More
Ma’aikata sun duƙufa domin ceto waɗanda girgizar ƙasa ta aukawa a lardin Sichuan

Ma’aikata sun duƙufa domin ceto waɗanda girgizar ƙasa ta aukawa a lardin Sichuan

Daga CMG HAUSA Mahukunta a lardin Sichuan na kudu maso yammacin ƙasar Sin, sun ce ya zuwa wajen ƙarfe 2 na yammacin 6 ga wata, girgizar ƙasa mai karfin maki 6.8 da ta auku a gundumar Luding ta hallaka mutane 66. Mataimakin darakta a ofishin lura da ayyukan gaggawa na lardin Wang Feng ya ce, girgizar ƙasar ta auku ne a jiya Litinin, kuma baya ga wadanda aka tabbatar da rasuwarsu, ibtila’in ya sabbaba jikkatar sama da mutane 253, yayin da wasu 15 suka ɓace. Mahukuntan lardin sun ce an shiga aiki gadan gadan, domin shawo kan ibtila’in, inda ya…
Read More
Managartan matakan kawar da talauci a Xinjiang sun amfanawa al’ummar yankin matuƙa

Managartan matakan kawar da talauci a Xinjiang sun amfanawa al’ummar yankin matuƙa

Daga MINA Abokai, a wannan mako “duniya a zanen MINA” yana bayani ne kan yadda wani manomi a yankin Xinjiang mai suna Halik Geym ya fita daga kangin talauci da samun ƙarin arziki. Wannan ɗaya ne daga cikin manyan na’urorinsa na aikin noma masu inganci da yake amfani da su wajen shuka amfanin gona iri daban-daban. A shekarar 2021, kuɗin shigarsa ya kai kuɗin Sin Yuan miliyan 1.8 (kwatankwacin dalar Amurka dubu 260). Amma yau wasu shekarun da suka gabata, ya sha fama da talauci, bai iya samun amfani gona da yawa ba, saboda garinsa na dab da hamada, ba…
Read More
Ƙasar Sin ta yi nasarar gwajin harba tauraron ɗan Adam na Weili mai lamba 1 S3/S4

Ƙasar Sin ta yi nasarar gwajin harba tauraron ɗan Adam na Weili mai lamba 1 S3/S4

Daga CMG HAUSA Yau ne da misalin ƙarfe 10 da mituna 24 na safe, ƙasar Sin ta yi amfani da rokar Kuaizhou-1A a cibiyar harba tauraron ɗan adam ta Jiuquan, inda ta yi nasarar gwajin harba tauraron ɗan-Adam samfurin Weili Space-1 S3/S4 cikin sararin samaniya kamar yadda aka tsara, kuma aikin harba tauraron d'ɗan-Adam din ya samu cikakkiyar nasara. Wannan shi ne karo na 17 da aka ci nasarar yin amfani da rokar Kuaizhou-1A, wajen aikin harba taurarin ɗan-Adam zuwa sararin samaniya. Mai fassara: Ibrahim Yaya
Read More
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ƙarin harajin kiran waya

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ƙarin harajin kiran waya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙarin harajin kiran wayar sadarwa da ofishin kasafin kuɗi na Nijeriya ke ƙoƙarin yi. Gwamnatin ta dakatar da qarin kaso biyar cikin dari ne da ake shirin yi a baya. Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki a Fasahar Zamani, Isa Ali Pantami ne ya sanar da dakatarwar a ranar Litinin yayin taron ƙaddamar da Kwamitin Shugaban Ƙasa na haraji kan hanyoyin sadarwa don bunqasa ɓangaren tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani a Abuja. Ministan ya ce tun tuni fannin sadarwa ya cika da harajai da yawa. Gwamnatin Tarayya ta…
Read More
Rashin kulawa da jama’a ba dimukuraɗiyya ba ce

Rashin kulawa da jama’a ba dimukuraɗiyya ba ce

Daga BELLO WANG Mutanen duniya na kallon ƙasar Amurka a matsayin wata babbar ƙasa, wadda ke kan gaba a fannin tattalin arziki, da na ingancin aikin likitanci. Sai dai ƙasar ta fi shan kaye a fannin tinakar cutar COVID-19 a duniya, ganin yadda mutanen ƙasar miliyan 94.6 suka kamu da cutar, kana wasu miliyan 1.04 daga cikinsu suka mutu sakamakon cutar, inda suka kasance kimanin kashi 1 bisa kashi 6 na adadin duniya baki daya. Sai dai ƙasar ta sake gyaran manufarta a fannin tinkarar annobar COVID-19 a kwanan baya, inda ta fara dakatar da samar da na’urorin gwajin kwayoyin…
Read More
Shugaba Xi ya bada umarnin bada fifiko ga ceton rayuka a gundumar lardin da girgizar ƙasa ta aukawa

Shugaba Xi ya bada umarnin bada fifiko ga ceton rayuka a gundumar lardin da girgizar ƙasa ta aukawa

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya ba da muhimmin umarnin bayar da fifiko ga aikin ceton rayuka, ba tare da yin ƙasa a gwiwa ba, domin rage asarar rayuka, sanadiyyar girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.8 da ta auku a gundumar Luding na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin ƙasar, a yau Litinin. Hukumomi a yankin sun ce mutane 21 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar iftila’in. Lardin ta aike da sama da ma’aikatan ceto 600, kuma 300 sun riga sun isa wurin da iftila’in ya auku domin shiga aikin ceto da gyara tituna da tura jirage marasa…
Read More
Gwano ba ya jin warin jikinsa

Gwano ba ya jin warin jikinsa

Daga CMG HAUSA Waye mai satar shiga yanar gizo mafi muni a duniya? Yau Litinin hukumar daidaita mummunar manhajar da ta bata kamfuta ta ƙasar Sin da kuma kamfanin Qihoo 360 na ƙasar Sin, suka gabatar da rahotannin binciken batun kutsen yanar gizo da aka yi wa jami’ar koyon ilmin masana’antu ta yankin arewa maso yammacin ƙasar Sin wato NPU. Wani abun shaida ne na daban. Rahotannin sun nuna cewa, ofishin kula da aikin kai harin musamman wato TAO dake ƙarƙashin jagorancin hukumar kula da tsaron ƙasar Amurka wato NSA, ya yi amfani da hanyoyi 41 wajen yi wa yanar…
Read More
Ƙasashen dake da alaƙa da “ziri ɗaya da hanya ɗaya” suna fatan ƙarfafa haɗin gwiwa da Ƙasar Sin a fannin cinikayyar zamani

Ƙasashen dake da alaƙa da “ziri ɗaya da hanya ɗaya” suna fatan ƙarfafa haɗin gwiwa da Ƙasar Sin a fannin cinikayyar zamani

Daga CMG HAUSA Ana gudanar da bikin baje kolin cinikayyar hidima na ƙasa da ƙasa na ƙasar Sin (CIFTIS) na shekarar 2022 a nan birnin Beijing. Wasu daga cikin ƙasashe, da kamfanoni da ke halartar wannan baje kolin sun fito ne daga ƙasashen da ke da alaƙa da shawarar "Ziri daya da hanya ɗaya". Mahalarta taron daga waɗannan ƙasashe sun bayyana cewa, yin amfani da fasahar zamani, ya samar da damammaki wajen bunƙasa cinikin hidima a duniya, kuma suna fatan yin haɗin gwiwa da ƙasar Sin a fannoni da dama a nan gaba. A cikin yankin nuna hidimomin al'adu da…
Read More