Editor

9513 Posts
Chelsea ta kori kocinta, Thomas Tuchel

Chelsea ta kori kocinta, Thomas Tuchel

Daga WAKILINMU Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta kori kocinta Thomas Tuchel sakamakon rashin nasarar da ta yi a daren Talatar da ta gabata a gasar Zakarun Turai. Tuchel mai shekara 49 kuma tsohon kocin Borussia Dortmund da Paris St-Germain, ya bar Stamford Bridge bayan watanni 20. Mamallakin ƙungiyar, Todd Boehly ya sanya Tuchel a kan riƙon wucin gadi har zuwa lokacin da za a samu wanda zai maye gurbinsa. Cikin sanarwar da ta fitar ranar Talata, Chelsea ta ce ta yi ammanar yanzu ne lokacin da ya dace ƙungiyar ta samu sabon kocin da ci gaba da jan ragamarta.…
Read More
DSS ta kama Tukur Mamu a filin jirgin saman Kano

DSS ta kama Tukur Mamu a filin jirgin saman Kano

Daga BASHIR ISAH Jami'an Hukumar Tsaro ta DSS sun kama Malam Tukur Mamu a Bababban Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano da ke Jihar Kano. Tun farko Mnahaja ta rawaito yadda jami'an tsaro suka tsare Mamu a birnin Alƙahira, babban birnin ƙasar Masar, inda daga nan aka dawo da shi Nijeriya. Mamu ya ce shi da iyalansa suna kan hanyarsu ta zuwa Ƙasar Saudiyya ne inda aka tsare su na tsawon awa 24 a Alƙahira. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, jirgin da ya dawo da su Tukur Mamu ya sauka filin jirgin saman Kano ne da misalin ƙarfe…
Read More
Xi Jinping ya aike da saƙon taya murna ga zaɓaɓɓen shugaban Kenya

Xi Jinping ya aike da saƙon taya murna ga zaɓaɓɓen shugaban Kenya

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya aike da saƙon taya murna ga zababben shugaban ƙasar Kenya William Ruto a yau Laraba. Cikin saƙon, shugaba Xi ya ce, Sin da Keyan na da daddadiyyar alaƙar abota da haɗin gwiwa a ɓangarori da dama, waɗanda suka haifar da kyawawan sakamako a shekarun baya-bayan nan. Ya ce yana ba ci gaban hulɗarsu muhimmanci, kuma a shirye yake ya haɗa hannu da shugaba Ruto, wajen ɗaukaka huldar zuwa wani muhimmin matsayi domin moriyar ƙasashen biyu da al’ummominsu. Mai fassara: Fa’iza Mustapha
Read More
Al’ummar ƙasashen Turai na ɗanɗana kuɗar rikicin Rasha da Ukraine

Al’ummar ƙasashen Turai na ɗanɗana kuɗar rikicin Rasha da Ukraine

Daga LUBABATU LEI Yau kusan watanni shida ke nan, tun bayan ɓarkewar rikici a tsakanin Rasha da Ukraine. Sakamakon rikicin, kamfanonin samar da makamai da na hatsi na Amurka sun ci ƙazamar riba, a yayin da kamfanonin samar da makamashi ma ba su so a bar su a baya. Bayanai na nuna cewa, sakamakon yadda ƙasashen Turai suka biyewa ƙasar Amurka wajen ƙaƙaba takunkumai kan Rasha, yanzu haka, ƙasashen Turai da dama na fuskantar matsalar karancin makamashi mai muni, hakan ya tilasta musu sayen iskar gas daga wajen Amurka a kan farashi mai tsada, matakin da ya sa kamfanonin samar…
Read More
An shirya tattaunawar Tiangong tsakanin ‘yan sama jannatin Sin da matasan Afirka cikin nasara

An shirya tattaunawar Tiangong tsakanin ‘yan sama jannatin Sin da matasan Afirka cikin nasara

Daga CMG HAUSA An yi nasarar shirya tattaunawar Tiangong wato cibiyar nazarin sararin samaniya ta ƙasar Sin, tsakanin ‘yan sama jannatin dake kumbon Shenzhou-14 da wakilan matasa da yaran ƙasashen Afirka cikin nasara jiya Talata. Ban da babban wurin da aka keɓe a hedkwatar ƙungiyar tarayyar Afirka wato AU dake birnin Addis Ababa, fadar mulkin ƙasar Habasha, an kuma keɓe wasu wuraren tattaunawa a ƙasashen Afirka guda 8 waɗanda suka hada da Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar. Jakadan ƙasar Sin dake Nijar Jiang Feng, ya gabatar da wani jawabi a wurin tattaunawar da aka keɓe a ƙasar, inda ya bayyana…
Read More
Matakan yayata ilimin kimiyya na Ƙasar Sin zai amfani duniya baki ɗaya

Matakan yayata ilimin kimiyya na Ƙasar Sin zai amfani duniya baki ɗaya

Daga IBRAHIM YAYA A kwanakin baya ne mahukuntan ƙasar Sin, suka fitar da wani kundin bayani, mai ƙunshe da matakan yayata ilimin kimiyya tsakanin al’ummar ƙasar, matakan da ake fatan za su taimaka wajen ingiza ƙwazon al’umma a fannin samar da ci gaba ta hanyar yin ƙirƙire-ƙirƙire. Ofisoshin sakatariyar kwamitin tsakiya na JKS, da majalisar gudanarwar ƙasar ne suka fitar da kundin cikin haɗin gwiwa. Kundin ya kuma ƙarfafa muhimmancin haɗe matakan yayata ilimin kimiyya, da fannin ƙirƙire-ƙirƙiren kimiyya da fasaha. Kana ya fayyace sassa daban-daban game da irin matakan da za a aiwatar domin cimma nasarar da aka sanya…
Read More
Ranar Hausa Ta Duniya: An bar jaki, ana dukan taiki

Ranar Hausa Ta Duniya: An bar jaki, ana dukan taiki

Daga RABI'U NA'AWWA Hausa harshe ne da Allah ya tarfa wa garinsa nono. Bisa wannan dalilin likkafarsa sai ta ci gaba ta yanda ya zamto mesa mai haɗiye dukkan wani ɗan ƙaramin yare da ya kusance shi ko maƙwabtaka da shi. Sai dai kash! Mafi yawan al’umar da Allah ya mallaka wa wannan harshe bisa ga dukkan alamu, suna yi masa riqon sakainar kashi. Ko kuma mu ce, sun bar jaki ne sun kama dukan taiki. Misali, mu ɗauki harshen Swahili, wanda yake harshe na farko a Afrika da aka ce ya kere harshen Hausa a yawan masu magana da…
Read More
An tsare Tukur Mamu da matansa a Masar

An tsare Tukur Mamu da matansa a Masar

Daga BASHIR ISAH An tsare mawallafin nan wanda ke shiga tsakani wajen kuɓutar da fasinjojin jirgin ƙasan hanyar Kaduna-Abuja da aka yi garkuwa da su, Tukur Mamu, a ƙasar Masar. An tsare Mamu ne a ranar Talata a Babban Filin Jirgin Saman Alƙahira a daidai lokacin da yake shirin tafiya Saudi Arebiya. Mamu, shi ne mawallafin jaridar nan ta Desert Herald, kuma mai magana da yawun fitaccen malamin Islaman nan na Kaduna, Ahmad Gumi, ya taka rawa wajen kuɓutar da wasu daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su a hanyar Kaduna a watan Maris da ya gabata. Sai…
Read More
Fahimtar yaren namiji a soyayya da zamantakewa

Fahimtar yaren namiji a soyayya da zamantakewa

Daga AMINA YUSUF ALI Sannunku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. Barkanmu da haɗuwa a wani makon. A kwanakin baya mun tattauna a kan yadda maza za su fuskanci yaren mata a soyayya. Ba wani yare ne can daban ba kamar Yarbanci ko Turanci ba fa. Amma yare ne na fahimtar ɓoyayye da bayyanannen saƙon da jinsin macen yake isarwa ga jinsin namiji ko kuma fahimtar halayyarta don samun sadarwa mara sarƙaƙiya. Kuma meye amfanin samun sadarwan mai sauƙi? Sai don a samu zaman lafiya da fahimtar juna a zaman aure. Ma'aurata duk yadda za su…
Read More
‘Yan wasan fim biyar da suka fi arziki a duniyar finafinai

‘Yan wasan fim biyar da suka fi arziki a duniyar finafinai

Daga AISHA ASAS Bincike ya tabbatar cewa, ba waɗanda suka fi samun roman aikinsu a duniyar nishaɗantarwa kamar masu harkar fim da kuma masu buga wasan ƙwallo, hakan ya biyo bayan irin so da ƙaunar da mutane ke yi wa wannan ɓangare guda biyu. Sanannen abu ne, mutane mafi rinjaye na duniya na sha'awar kallon finafinai, walau waɗanda ake yi a yarensu ko na wasu al'ummar. Wannan ne ya sa harkar fim ta zama cikin jerin farko da ke samar da kuɗin shiga da kuma samar da aikin yi ga mata da maza musamman ma matasa, musamman a vangaren jarumai,…
Read More