09
Sep
Daga UMAR GARBA a Katsina Wani magidanci Amiru Sani mai kimanin shekara 27 a duniya ya bayyana wa manema labarai a Katsina cewar ya saki uwargidansa saboda yanayin matsin rayuwa da ya shiga. Magidancin mai mata biyu ya bayyana cewar yana matuƙar son matar tasa amma saboda matsin tattalin arziki da ya shiga ba zai iya cigaba da ɗaukar nauyinta ba. "Ba don ba na sonta ba, ba don na gaji da zama da ita ba, na saketa ne kawai don samar wa kaina sauƙi daga halin tsadar rayuwar nan da muka samu kanmu a ciki," inji shi. Amiru Sani…
