Editor

9513 Posts
2023: Atiku ne zai ci Kano ba Kwankwaso da Tinubu ba — Shekarau

2023: Atiku ne zai ci Kano ba Kwankwaso da Tinubu ba — Shekarau

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau ya sha alwashin cewa shi zai kawo wa ɗan takarar shugabancin qasa a Jam’iyar PDP, Atiku Abubakar ƙuri’u mafi rinjaye a Jihar Kano sama da na Rabi’u Kwankwaso na NNPP da Bola Tinubu na APC a zaven 2023. Shekarau ya bayyana hakan ne a wata hira da a ka yi da shi a gidan talabijin na AIT a ranar Talata. Tsohon gwamnan Kano ɗin ya ce yana da ɗumbin masoya 'yan dangwale, waɗanda su ne su ka zaɓe shi a zaɓen 2003, lokacin da ya kayar da…
Read More
Xi Jinping da shugaban AU sun taya juna murna

Xi Jinping da shugaban AU sun taya juna murna

Daga CMG HAUSA Yau Jumma’a ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, da shugaban karɓa-karɓa na ƙungiyar tarayyar Afirka AU, kana shugaban ƙasar Senegal Macky Sall, suka aika wa juna sakon murnar cika shekaru 20 da kafa AU da ƙulla alaƙar diflomasiyya tsakanin ƙasar Sin da AU. Shugaba Xi ya ce, alaƙar Sin da AU na dada haɓaka, wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen zurfafa dankon zumunta tsakanin Sin da Afirka, da ƙara faɗaɗa haɗin-gwiwarsu a sabon zamanin da muke ciki. Ya ce yana fatan haɗa kai tare da Macky Sall da sauran shugabannin ƙasashe membobin AU, don tabbatar da aiwatar…
Read More
Bikin baje koli na CIIE zai samu halartar kamfanoni sama da 280 dake kan gaba a duniya

Bikin baje koli na CIIE zai samu halartar kamfanoni sama da 280 dake kan gaba a duniya

Daga CMG HAUSA Jiya ne, aka gudanar da taron masu saye da sayarwa na reshen bikin baje kolin ƙasa da ƙasa na kayayyakin masarufi da cinikin ba da hidimma CIIE kana taron shigo da jarin waje na birnin Shanghai, inda aka bayyana cewa, yanzu an kammala aikin yin rajistar kamfanoni da za su halarci bikin, inda fiye da kamfanoni 280 daga cikin 500 dake kan gaba a duniya ne suka tabbatar da aniyarsu ta halartar taron, daga cikinsu kashi 90% sun halarci bikin na bara. Mataimakin darektan hukumar baje ƙolin kayayyakin da aka shigo da su ƙasar Sin Liu Fuxue…
Read More
Masana kimiyyar ƙasar Sin sun gano wani sabon ma’adini da aka ɗauko daga duniyar wata

Masana kimiyyar ƙasar Sin sun gano wani sabon ma’adini da aka ɗauko daga duniyar wata

Daga CMG HAUSA Masana kimiyya na ƙasar Sin, sun gano wani sabon ma’adini da aka sanyawa suna Chang'esite-(Y), wanda kumbon Chang'e-5 ya kwaso daga duniyar wata. Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa, da hukumar lura da ayyukan binciken samaniya ta ƙasar ko CNSA, da hukumar lura da makamashin Atomic ta ƙasar ko CAEA suka fitar a Juma’ar nan, an ce an tantance sabon ma’adinin ne bayan zurfafa binciken kimiyya. Da yake karin haske kan hakan, mataimakin daraktan hukumar ta CAEA Dong Baotong, ya ce wannan ne karon farko a tarihi da ƙasar Sin ta gano wani ma’adini a duniyar wata, kuma…
Read More
Muna ɗaukar mata aiki amma sai wacce ta dace – Kwamandan vijilante na Kano

Muna ɗaukar mata aiki amma sai wacce ta dace – Kwamandan vijilante na Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Kwamandan ƙungiyar tsaro ta vijilante a Jihar Kano, Shehu Rabi’u ya ce suna ɗaukar mata aiki, domin akwai rawar da suke takawa a wajen tsaron jihar. Da ya ke zantawa da manema labarai a ofishinsa a Kano ranar Talata, Rabi'u ya ce ba ko wacce irin mace su ke ɗauka aikin tsaro ba, sai wacce ta dace. Ya ce suna ɗaukar ma’aikata aiki waɗanda shekarunsu suka fara daga 18 zuwa 40, inda ya qara da cewa su na yin duba na tsanaki kafin ɗaukar ma’aikata domin guje wa ɗaukar bara-gurbi cikin al’umma. “Mukan ɗauki mata…
Read More
‘Yan fashi sun fasa bankuna da dama a Jihar Kogi

‘Yan fashi sun fasa bankuna da dama a Jihar Kogi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rahotanni daga Jihar Kogi na cewa 'yan fashi da makamai sun far wa rassan bankunan Zenith, da UBA da First Bank da ke ƙaramar hukumar Ankpa. BBC ta rawaito cewa lamarin ya faru da tsakar rana, inda ɓarayin suka yi awon-gaba da maƙudan kuɗaɗen da ba a san adadinsu ba. Ganau sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa, 'yan fashin sun zo bankunan cikin ƙananan motoci da babura da bas-bas, inda suka wawushe kuɗin da ke bankunan da wurin hada-hadar kasuwancin kuɗi na POS da ke kusa da bankunan. 'Yan bindigan sun yi ta…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ƙarin harajin kiran waya – Pantami

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ƙarin harajin kiran waya – Pantami

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙarin harajin kiran wayar sadarwa da ofishin kasafin kuɗi na Nijeriya ke ƙoƙarin yi. Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki a Fasahar Zamani, Isa Ali Pantami ne ya sanar da dakatarwar a ranar Litinin yayin taron ƙaddamar da Kwamitin Shugaban Ƙasa na haraji kan hanyoyin sadarwa don bunƙasa ɓangaren tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani a Abuja. Ministan ya ce tun tuni fannin sadarwa ya cika da harajai da yawa. Gwamnatin Tarayya ta hannun ofishin kasafin kuɗi na tarayya a baya ta bayyana cewa za ta fara aiwatar da…
Read More
Nijeriya za ta zama babbar mai kai wa Turai iskar gas — Minista

Nijeriya za ta zama babbar mai kai wa Turai iskar gas — Minista

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙaramin Ministan Albarkatun Man fetur, Timipre Sylva, ya ce Nijeriya na shirin zama babbar mai safarar iskar gas ga Nahiyar Turai, sakamakon matsalar makamashin da ake fama da ita a duniya, wanda yaƙin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine ya haifar. Sylva ya shaida hakan ne a ranar Talata yayin wani zagayen tattauna wa a yayin babban taron Gastech karo na 50 da ke gudana a birnin Milan, Italiya. Ministan ya ci gaba da cewa, a halin yanzu, tallafin da ake samu na bunƙasa iskar gas ya kasance nasara ga Turai da Afirka.…
Read More
Sarkin Hausawan Pantami ya zama Jakadan Zaman Lafiya

Sarkin Hausawan Pantami ya zama Jakadan Zaman Lafiya

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Wasu ƙungiyoyin al'umma uku a Gombe sun karrama Malam Abdussalam Muhammad Sarkin Hausawan Pantami da lambar yabo ta Jakadan Zaman Lafiya wato 'Peace Ambassador' a turance. Ƙungiyoyin su ne Arewarmu Duniyarmu da Arewa Youth and Women for Change da kuma Hausa Fulani Youth and Development Orientation Forum Association of Nigeria (HAFYDOF). Sun karramma Sarkin Hausawan ne a matsayinsa na dattijo mai kishin al'ummarsa da kuma taimaka wa matasa. Da yake jawabi a wajen bikin da suka shirya a Gombe, Shugaban Ƙungiyar Zauren Hausawa ta duniya, Ambasada Muhammad Kabiru Kuri, ya ce sun karrama sarkin…
Read More
‘Yan sanda sun ceto ɗan takarar majalisar dokoki daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

‘Yan sanda sun ceto ɗan takarar majalisar dokoki daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar 'yan sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar kuɓutar da ɗan takarar majalisar dokoki ta jihar Katsina a ƙarƙashin Jam'iyyar PDP a zaɓe mai zuwa na shekara ta 2023. 'Yan bindigar dai sun yi garkuwa da Hon. Ibrahim Tafashiya wanda ke neman zama ɗan majalisa mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Kankiya a zaɓe mai zuwa. Kakakin rundunar SP Gambo Isa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar. “Gaskiya ne tawagarmu ta kuɓutar da Tafashiya daga hannun ‘yan ta’adda kuma an sake haɗa shi da iyalansa,” inji shi. Kakakin rundunar ya ci…
Read More