Editor

9513 Posts
Hajjin 2022: Gwamnatin Zamfara ta mayar wa alhazai 1,318 Naira 50,000 kowanne

Hajjin 2022: Gwamnatin Zamfara ta mayar wa alhazai 1,318 Naira 50,000 kowanne

Daga SANI AHMAD GIWA a AbujaGwamnatin Jihar Zamfara ta mayar wa da kowane mahajjaci daga cikin alhazai 1, 318 da suka yi aikin hajjin bana zuwa ƙasar Saudiyya Naira dubu 50. Gwamna Bello Matawallle wanda ya bada umarnin mayar da kuɗaɗen, ya umurci hukumar alhazai ta jihar da ta tabbatar da aiwatar da wannan umarni cikin gaggawa. Ya umurci hukumar da ta fara biyan kuɗin daga nan zuwa ranar Litinin, 12 ga Satumba, 2022 a kowace ƙaramar hukuma 14 na jihar. Don haka, an shawarci maniyyatan da abin ya shafa da su je ƙaramar hukumar inda suka biya kuɗinsu domin…
Read More
Gwamna Buni ya bai wa iyalan Marigayi Sheikh Aisami kyautar gidaje uku

Gwamna Buni ya bai wa iyalan Marigayi Sheikh Aisami kyautar gidaje uku

Daga MOHAMMED EL-AMEEN a Damaturu Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni, a ranar Laraba ya raba wa iyalin Marigayi Sheikh Goni Aisami kyautar gidaje. Mai ba wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin addini, Ustaz BG Kyari ne ya gabatar da kyautar a gaban Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Umar Sulyman. Manhaja ta jiyo cewa an bai wa matan marigayin kowacce gida, da su ka haɗa da Aisha Badamasi da kuma Hajara Muhammad Ibrahim. Sannan gwamnan ya bai wa 'ya'yan marigayin su uku, waɗanda mahaifiyarsu ba ta gidan gida guda ɗaya. Yayin miƙa takardun gidajen ga iyalan marigayin Dukkanin gidajen da…
Read More
Neman illata Ƙasar Sin ya haifar da matsalar tattalin arziki ga Amurka

Neman illata Ƙasar Sin ya haifar da matsalar tattalin arziki ga Amurka

Daga CMG HAUSA Tashar yanar gizo ta Eurasia Review ta ƙasar Amurka wato nazarin Asiya da Turai, ta ba da rahoton cewa, a ƙoƙarinta na neman iko, gwamnatin Joe Biden ta Amurka na neman lahanta ci gaban tattalin arzikin Sin da na yammacin duniya, da ƙasashen Asiya masu tasowa da ma makomar dukkan ƙasashe masu tasowa. Rahoton wanda aka wallafa a ranar 31 ga watan Augusta, ya ruwaito Jack Kemp, mai fashin baƙi kan harkokin tattalin arziki na kamfanin dillancin labarai na Reuters na cewa, tun farkon 2018, Amurka take aiwatar da matakai da gangan, da zummar illata tattalin arzikin…
Read More
Ƙasar Sin muhimmiyar abokiyar hulɗa ce da Afrika za ta iya haɗa hannu da ita wajen yaƙi da yunwa

Ƙasar Sin muhimmiyar abokiyar hulɗa ce da Afrika za ta iya haɗa hannu da ita wajen yaƙi da yunwa

Daga CMG HAUSA Wani masanin tattalin arziki na ƙasar Rwanda Egide Karuranga, ya bayyana ƙasar Sin a matsayin ɗaya daga cikin muhimman ƙasashen duniya da ƙasashen Afrika za ta iya hada hannu da su, wajen yaki da ƙarancin abinci a nahiyar, saboda gogewar da take da shi da tarin fasahohin aikin gona. Masanin na ƙasar Rwanda ya bayyana haka ne jiya, yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, a gefen taron raya muhalli na Africa Green Revolution da aka kammala a Kigali, babban birnin ƙasar. A cewarsa, Afrika na iya koyon dabarun ƙasar Sin bisa la’akari da…
Read More
CMG ra watsa shagalin murnar bikin tsakar yanayin kaka ta shekarar 2022

CMG ra watsa shagalin murnar bikin tsakar yanayin kaka ta shekarar 2022

Daga CMG HAUSA Bikin tsakar yanayin kaka yana ɗaya daga cikin manyan bakukuwan gargajiya na ƙasar Sin. A wannan rana, Sinawa su kan haɗu, tare da kallon duniyar wata, da cin wainar wata, da tunawa da sauran ‘yan uwa tare da yi wa juna fatan alheri. A daren ranar 10 ga watan Satumba, wato ranar bikin tsakar yanayin kaka bisa kalandar gargajiyar ƙasar Sin, babban gidan rediyo da telebijin na ƙasar Sin wato CMG ya watsa shagalin murnar bikin na shekarar 2022, inda aka nuna shirye-shirye masu nishaɗantarwa ga masu kallo na sassan duniya. Taken shagalin murnar bikin tsakar yanayin…
Read More
Lewandowsk na iya zama warakar Barcelona – Masu sharhi

Lewandowsk na iya zama warakar Barcelona – Masu sharhi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Masu sharhi a fagen wasan ƙwallon ƙafa sun bayyana cewa, bayan wani yanayi na firgici da Barcelona ta shiga a kakar da ta gabata, sakamakon fitar wasu daga cikin manyan ’yan wasanta, za a iya cewa yanzu Barcelona ta samo warakar matsalarta. Fitar babban ɗan wasanta Lionel Messi ya jefa ƙungiyar cikin laluɓen wanda zai maye wagegen giɓin da ya bari. Kodayake, a watan Fabirairu da ya gabata ta sayo ɗan wasan gaban Gabon Pierre-Emerick Aubameyang wanda kuma ya taka rawar ganinsa wajen ganin ya ceto ƙungiyar daga halin da ya same ta. Ta kuma ƙara…
Read More
Kamfanin Fulawa Mai Kwabo ya sake rabon motoci don ƙarfafa gwiwar abokan hulɗa

Kamfanin Fulawa Mai Kwabo ya sake rabon motoci don ƙarfafa gwiwar abokan hulɗa

Daga AMINA YUSUF ALI A wani yunƙuri na ƙara ƙarfafa kyakkyawar alaƙarsu da masu ruwa da tsaki a kasuwancinsu, kamfanin Fulawa Mai Kwabo (Flour Mills of Nigerai, FMN), Kamfanin da ya yi zarra a Nijeriya wajen samar da kaya masu inganci kuma mamallakin sanannen kamfanin kayan abincin nan na Golden Penny, ya ba da kyautar tireloli ga dilolinsu da suka cancanta a ƙarƙashin tsarin  B2B. Kamfanin ya yi rabon ne domin ƙara danƙon alaƙar dake tsakaninsa da dilolin da kuma ƙara sauƙasƙa musu harkokin tafiyar da kasuwancinsu.  Ranar da  aka gabatar da taron, kamfanin ya rarraba sabbin tireloli dal, guda…
Read More
2023: Ba za mu sake saka makusantan ‘yan takara a tawagar yaƙin neman zaɓen PDP ba – Gwamna Bala

2023: Ba za mu sake saka makusantan ‘yan takara a tawagar yaƙin neman zaɓen PDP ba – Gwamna Bala

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi ya bayyana cewar tawagar yaqin neman zaɓe na Jam’iyyar PDP ya zuwa zaɓen shekarar 2023 ba za ta ƙunshi jinsin ‘yan uwa ko dangin ɗan takara domin ƙarfafa su ta hanyar siyasa ba. Sanata Bala ya ce jam’iyyar ta PDP ba za ta ƙara amincewa ta faɗa cikin wancan kuskure da makamancinsa ya faru a shekara ta 2019 ba, lokacin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubar ya ɗora makusantansa akan tawagar yaƙin neman zaɓe, da hakan ya yi sanadiyyar faɗuwarsa a wancan zave ba. Idan za a…
Read More
2023: Al’ummar Tibi sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Sule a karo na biyu

2023: Al’ummar Tibi sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Sule a karo na biyu

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Al’ummar ƙabilar Tibi na ƙasa reshen Jihar Nasarawa sun bayyana tare da tabbatar wa gwamnan jihar, Injiniya Abdullahi Sule cikakken goyon bayansu. Shugabannin al’ummar Tibin sun bayyana haka ne a lokacin da suka jagoranci ɗimbin al’ummarsu inda suka ziyarci gwamnan a gidan gwamnati dake Lafiya babban birnin jihar. A jawabin shugaban ‘yan ƙabilar Tibin reshen jihar Nasarawa, Kwamared Peter Ahemba ya ce babban dalilin sake mara wa gwamnan baya don tabbatar da nasarar sa karo na 2 shine yadda gwamnatinsa ta shawo kan matsalar rashin tsaro da ya addabi jihar da daɗewa. A cewarsa…
Read More
Dalilanmu na bin Sha’aban Sharaɗa Jami’iyyar ADP a Kano – Rarara

Dalilanmu na bin Sha’aban Sharaɗa Jami’iyyar ADP a Kano – Rarara

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Jam’iyyar ADP a Kano ta bai wa ‘yan wasan Hausa da mawaƙa guraben takara da dama a cikinta. Idan za a iya tunawa a Asabar ɗin da ta gabata ne Sha’aban Ibrahim Sharaɗa ya ƙaddamar da takarar Gwamnan Kano a cikin jam’iyyar. Yanzu haka dai jam’iyyar ta bai wa mawaƙi Aminu Ala takarar Majalisar Wakilai ta Nassarawa. An kuma bai wa Daddy Hikima wanda aka fi sani da ‘Abale’ takarar majalisar a Ƙaramar Hukumar Kumbotso. Da yake qarin haske kan dalilinsu na bin Sha’aban Sharaɗa, mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ya ce sun bijire wa APC…
Read More