11
Sep
Daga CMG HAUSA An kammala gasar bidiyo ta matasan Sin da Afrika ta “Great to Meet You” karo na farko jiya Asabar, gaba ɗaya bidiyo 102 ne suka shiga gasar, inda guda 3 suka samu kyautar matsayi na farko, guda 6 suka samu na biyu, saura goma suka samu na matsayi na uku. An shirya bikin miƙa lambobin ne a hedkwatar babban rukunin gidan rediyo da talibijin na ƙasar Sin wato CMG na nahiyar Afirka dake birnin Nairobin ƙasar Kenya, tare kuma da gabatar da shirye-shirye kai tsaye ta kafar bidiyo a faɗin duniya. Hedkwatar CMG dake Afirka ce ta…
